TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 2
TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 2 A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta. “Cewa yayi yana sonki hala” shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce. “Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma” ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee. “Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne” Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya. Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba. Da hirar Dee Yusuf su ka isa ka…