RAMUWAR GAYYAH CHAPTER5
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 5 K’arfe biyar da rabi sawwam yafarka, ummulkhair ya kalla wacce ke kwance gefenshi ta cure jikinta wuri guda,+ Hannunshi yakai kan goshinta ya taba, duk zufa ta tsatssafo mata kamar wacce take zaune atsakiyar rana, Tashi yayi ya shiga toilet ya tsaftace jikinsa yafito, zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi kamar kankara sai zallar farin ciki dake wanzuwa acikinta marar yankewa, Idonshi akan khairi ya dauko kayanshi yasaka, gaban gadon yaje ya dagata ahankali ya gyara mata kwanciyarta, fuskarta yabi da kallo yana murmushi saboda baccinta take hani’an kamar ta shekara batayi ba, Sai da yabata wani zazzafan kiss a kumatunta sannan yaja bargo ya lullubeta yafita masallaci. Karfe shida da yan mintuna yadawo cikin dakin amma har lokacin ummulkhair bata tashiba asalima ko juyi bata yiba tana nan a yarda yatafi yabarta, Gefenta yaje ya kwanta ya dagota zuwa jikinshi ya rungumeta, “My lonely yau kin tabbatar da abinda nadade ina fada miki cewar zan baki dad…