RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 1
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 1 _Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai…._ ~~~”Wannan shine abinda nake son kiyi kamar yadda nafada miki abaya, hakika ummulkhair nadade ina burin Allah ya bani ya mace domin wannan burin nawa ya cika amma Allah bai baniba sai yanzu, ina fata zaki dage ki zama silar cikar Burina kamar yadda nadade ina fata,+ Idan kikayi haka kin gama yimin komai kuma zanyi alfahari dake sannan koda na mutu to zan mutune da farin cikin abinda kika yimin, ina fata zaki mayar da hankali kan abinda natura ki sannan banda kula kawayen banza da samari barkatai idan kikayi haka to lallai ranki zai baci, Allah yayi miki albarka ya baki nasara” Idonta fal da kwalla ta dago tana duban mahaifin nata wanda ke kishingide akan kujera fuskarsa cikeda walwala da annuri, “Abba nayi maka alkawari zan zama silar cikar burinka kamar yadda ka dade kana fata sannan zanyi abinda ka turani batare da an samu kuskure ba” Sai alokacin mahaifiyarta dake zaune agefe tayi magana itama idonta dauke da kwalla, “Yanz…