TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 6 TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 6 “Haba Alhaji ai sai ka kashe ta daukar doka a hannunka bai kamata ba sam, ka bari ma asan wa yai mata cikin sai ku dau mataki” cewar Doctor Mahmud. Ganin da gaske ya ke suka hadu suka bambareshi daga jikinta yana ihu kamar mahaukaci, gaba daya ya zauce saboda tashin hankali, “ku barni na kashe ta dan wallahi da naga wannan tashin hankalin gwara naga gawarta, kuma wallahi ba dai gidana ba ki sanja wani uban ba dai ni ba.” “Ai bata da wani uba da ya fika kuma wallahi a gidanka zata zauna daram.” Umma ce ta fada tana kuka “tun sanda kuka taho na biyo bayanku dan duk maganarsa a kunnena yai muku, kuma dama na zargi wani abu a raina tun da naji shiru basu dawo ba.” “Kika kara magana sai ranki ya baci dan ba wata yar iska da zata zauna min a gida, ta koma inda taje tayo iskancin nata har tayo cikin amma wallahi ba dai gidana ba, idan ko ba haka ba wallahi sai dai ki bita ku tafi gaba daya.” “Wallahi ba inda zan bita kuma a gidanka zata zauna ko kaffara bazan ba, waya jan…