TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 4 TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 4 Innalillahi wainna’ilaihir raji’un, Hajiya! Hajiya ta! girgiza ta yake iya karfin sa, ya sungume ta yai waje da gudu. Haruna! Haruna! juya mota maza maza mu wuce. Duka masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ganin Daddy yana wannan ihun abunda basu taba jiba. Hankalinsu be gama tashi ba sai da suka ga Mommy a hannunsa, ga dukkan alamu babu rai a tare da ita. Gaba dayansu suka yo kansu suna salati, wata tsawa ya watsa musu “ku matsa ku bani waje.” A sukwane ya shiga bayan motar dan tuni Haruna ya juya motar, ya fada ciki yaja suka bar gidan, suka nufi wani private hospital mafi kusa dasu. Ko parking be gama bari yayi ba ya fito, kamar jaririya haka ya dauketa ko nauyin ta baya ji yai cikin asibitin da ita. “Doctor dan Allah katemake ni, karta rasa rayuwarta dan Allah ka temaka mun” haka kawai yake furtawa. Nan da nan Nurses suka amshe ta sukai emergency da ita, Doctor din na ciki nan da nan yai kanta ya fara bata temakon gaggawa, dan doguwar suma tayi ga dare ya faray…