TATTALINTA CHAPTER 9

TATTALINTA CHAPTER 9
TATTALINTA CHAPTER 9 *A* yadda yaji ta fara magana yasan labarin auran shi yaje kunnanta domin yana d’agawa yaji tace, “Sannu ango Sultan.” Yayi fuska kamar beji abinda tace ba sai ma cewa yayi. “Umma ina ta shirin bugo miki waya sai kuma gashi kin bugo min ya gida..?!” “Ban sani ba, nace ban sani ba. yanzu Ahmad ni zaka yaudara sabida cimma wani kudiri naka? Karfa ka manta ni mahaifiyar kace nafi k’arfin duk wani abu da zaka yi na kashin kanka amma har kaje kayi aure ba tare da sani ba ko shawara dani ko? Toh ka kyauta kuma ina son gobe-goben nan na ganka a gida Nigeria ina matarka Nadiya take…?!” Jikin shi ne yayi sanyi sosai ya kuma kasa bata amsar da ta tambaye shi domin shi kanshi ba zai ce ga inda Nadiya take ba dan yayiwa me gadinsu waya yace bata koma can ba. Muryar Umman yaji tana sake tambayar shi jiki a sanyaye yace mata, “Umma Nadiya bata nan ta wuce O’Marah.” Baki biyu kenan yayi be san abba ya gayawa Umma ba sai jiyayi tana cewa, “Karya kake yi domin ni ba haka abbank…