TATTALINTA CHAPTER 8

TATTALINTA CHAPTER 8
TATTALINTA CHAPTER 8 Yayi ball da ledar dake ajiye gabaki d’aya kayan ciki suka tarwatse Balqees da Nadiya suka zaro ido suna yi mai kallon mamaki da al’ajabi. Sake bin kayan yayi d’aya bayan d’aya ya dinga ball dasu kamar wani zararre, Balqees ta bi kayan da kallo domin kayan costmetiec ne, kuma daga gani zasu yi tsada masu kyau dasu harda spray suma kusan guda biyar haka ya bisu yana wulli dasu sai da yayi musu filla-filla ko wanne ya samu guri sannan ya juya ya kalleta idanuwan shi sunyi jawur yace, “A gidan uban wa kika yayubo mana wannan sakaran wawa me shegen surutun tsiya ah…?!” Ta yatsina fuska wannan karan ba kuka ta fara magana ciki-ciki tana cewa. “Gaskiya ni Yaya Sultan na gaji, ya za’ayi ka dinga korar min masoya? Nazo da Adam kace yayi kankanta na samu Salman a makaranta ban kawo shi nan ba ka dakatar dashi yanzu na samo wannan kazo kace wai ya fiye surutu ai surutu baya hana aure bare soyayya.” Ta fad’a tana fari da idanuwa tare da cono baki tana murgud’a shi yace, “…