TATTALINTA CHAPTER 13 THEND KARSHE

TATTALINTA CHAPTER 13 THEND KARSHE
TATTALINTA  CHAPTER 13 THEND KARSHE     Bayan wasu watan ni lokacin cikin Nadiya yayi girma sosai girman da ciki be ta6a yi mata ba. ajiye aikin asibitin ta tayi ta dawo gida ta zauna, komai sai dai ayi mata dan babu abinda take iya yi. Zaune take tana karatun wani littafin addu’o’i, yayin da su humaira da Islam ke ta wasa sai ga Balqees ta dawo daga gidan hajiya, zama tayi a parlor’n tare da kallon Nadiya tace.  “Sannu ya jikin..!”  “Sai godiyar ubangiji kawai, ya kika baro hajiya kakan da kuma k’afar ta ta…?”  “Lafiya lau can na bar ta ina shiga gidan ta din ga min fad’a wai na taho na barki, shine nace mata zuwa nayi na ganta dan kar ta mutu ba’a sani ba, shine wai toh sai na riga ta mutuwa dan ita sai taga auran takwarar ta (Islam).”  Nadiya ta kyalkyale da dariya, tana cikin yin dariyar ne taji ana tsikarin ta a marar ta, nan da nan tayi saurin rik’e ciki tana furta kalmar “innalillahi wa’innailaihir rajiun.” Balqees najin haka ta yi saurin zuwa gurin ta tana tambayar ta menene Nadiya …