TATTALINTA CHAPTER 12

TATTALINTA CHAPTER 12
TATTALINTA CHAPTER 12    Sosai suka yi yawo duk inda suka je sai abokan sa sunyi mai tsiya sai dai kawai ya share su, basu koma gida ba sai bayan sallar isha’i duk sun gaji dan haka kowa d’akin sa ya shiga dan kimtsawa.  ….  Sai da cikin Nadiya ya kai watanni  biyar sannan suka gane cikin da take da dashi, murna a wajan sultan ba’a magana har fad’a yayi mata sabida 6oye mishi cikin da takeyi dan haka tayi mai ana humaira ma.  Shirye-shiryan bikin Nabeelah su Nadiya suke yi duk da cewar cikin ta ya tsufa amma babu inda bata zuwa, shima Yusif an sanya ranar auran su inda ya yadda zai auri bilkisu ‘yar gidan Adda Aisha, sai k’anwarsa Aisha da itama ta hakura da Sultan ganin ba samun sa zata yi ba tsakanin su da Nabeela sati d’aya.  Nadiya na kwance a  d’aki tana bacci kasan cewar ta d’auki hutun haihuwa a asibiti yayin da Balqees dasu Jamila su Fiddausi dasu Aisha ke zaune a parlor sun saki teburin hira kowa na fad’ar matsalarsa Balqees ta yatsinna fuska tare da cewa.  “Ni babu abinda yake damu…