TATTALINTA CHAPTER 10

TATTALINTA CHAPTER 10
TATTALINTA CHAPTER 10 Sultan yana kwance a gida yana had’a lecture notes cikin laptop d’in shi a dole shi baza shi gurin taron ba a haka Nadiya ta shiga d’akin ta ganshi a kwance a gado. Tsayawa tayi a bakin k’ofa tana binshi da kallo zuciyarta na bugawa wani irin mad’acin kishi ya taso mata, tana k’ok’arin shiga wayar shi ta fara ringing ya sanya hannu ya d’auka tare da karawa a kunnenshi, ji tayi yana cewa. “Ke billy kun rainani ko?bana ce muku bazan zoba ko so kuke a zage ni?…au kuka babyn take yi bayan tuntuni na gaya mata babu wani event da zanzo me yasa take son sanya kanta cikin damuwa ne?…toh wai ma tana ina ma bani ita nan.” Da sauri Nadiya ta shiga ciki, a bayan shi ta kwanta ta shiga shafo kirjinsa, cikin kunnansa tayi mai magana. “Kace mata zakaje wannan itace alfarma ta biyu da zaka yi min dan Allah.” Dai-dai sannan billy ta mik’awa Balqees waya, shasshek’ar kukanta ya jiyo si jikinsa yayi sanyi ya lumshe ido tare da zura hannu bayan shi yana shafo gashin Nadiya cikin sanyi…