YAREEMAH KHALEED CHAPTER 6 YAREEMA KHALEED CHAPTER 6 da zallar ɓacin ran kalamanta Abibi ya nufi inda take, yana zuwa ya tsinketa da marin da saida taga hasken wuta. “ƙarya kikeyi munfuka, wallahi baki isa kin ɓata mana suna ba domin kuwa muɗin mutanen arziƙi ne kuma kowa ya shaida hakan, wace ke? nawa aka biyaki?, to bari kisan abinda baki sani ba daga ke har jahilan mutanen da suka aiko ki domin kici zarafinmu kunyi kaɗan” , “nida Sa’adatu ba irin shaiɗanun mutanen nan bane marasa imani masu butulcewa ni’imar ubangiji da zai ɗauki kyauta mai girma ya bamu mu wulaƙantata ba, Ƴaƴa da kike ikirarin mun haifa tabbas wannan haka yake komi kin faɗi dai-dai sai zance ɗaya da kikai kuskure akai, bamu saida ƴarmu ba, Allah’n daya bamu shiya amsa abarsa, bawai dan baya sonmu da ita ba sai dan yafimu sonta, da hannuna na ɗau gawar RAIHANA na kaita maƙabarta, amma ni ban saida ƴata ba saboda wani abin dubiya, kuɗin dana fi ƙarfinsu tin kamin zuwan RAHINAT da RAIHANA duniya” ta ɗago idanunta suna masu zubda hawaye tace, “to A…