YAREEMAH KHALEED CHAPTER 6
YAREEMA KHALEED
CHAPTER 6
da zallar Ιacin ran kalamanta Abibi ya nufi inda take, yana zuwa ya tsinketa da marin da saida taga hasken wuta.
“Ζarya kikeyi munfuka, wallahi baki isa kin Ιata mana suna ba domin kuwa muΙin mutanen arziΖi ne kuma kowa ya shaida hakan, wace ke? nawa aka biyaki?, to bari kisan abinda baki sani ba daga ke har jahilan mutanen da suka aiko ki domin kici zarafinmu kunyi kaΙan” ,
“nida Sa’adatu ba irin shaiΙanun mutanen nan bane marasa imani masu butulcewa ni’imar ubangiji da zai Ιauki kyauta mai girma ya bamu mu wulaΖantata ba, Ζ³aΖ΄a da kike ikirarin mun haifa tabbas wannan haka yake komi kin faΙi dai-dai sai zance Ιaya da kikai kuskure akai, bamu saida Ζ΄armu ba, Allah’n daya bamu shiya amsa abarsa, bawai dan baya sonmu da ita ba sai dan yafimu sonta, da hannuna na Ιau gawar RAIHANA na kaita maΖabarta, amma ni ban saida Ζ΄ata ba saboda wani abin dubiya, kuΙin dana fi Ζarfinsu tin kamin zuwan RAHINAT da RAIHANA duniya”
ta Ιago idanunta suna masu zubda hawaye tace, “to Abbi ni kuma wace? mine matsayina a wurinku? miye asalina? dan Allah ka fitar dani daga ruΙani domin kuwa a yanzu inada buΖatar jin Ιumin iyayena, ina son na sami kusancinsu koda babu soyayyarsu kamin na koma ga Allah”
Abii yace, “mu bamu sanki ba, hasalima bamu da wata masaniya akanki, wala’Allah su macutan da suka sauya maki kamanni zuwa irin siffar Ζ΄armu suke son yin amfani dake ta wata hanyar, yanzu gashi suna neman saki a wuya, domin kuwa ni Abdullahi bazan Ζyaleki ba kuma bazan yafe maki ba har sai na Ιaukarma Ζ΄ata fansar wuyar da kika jefata aciki….”
ta katsesa da faΙin, “to Abii idan kuma nice Rahinatu fa?”
wani irin juyowa yayi da jin zancen nata, ya daΙe yana Ζare mata kamin ya koma kan Rahinat ma ya Ζare mata kallo,wani tsoro yaji ya ziyarce shi, karfa aljanu su buΙe masu ido.
ta kuma katse tinaninsa, “Abii baka tinanin nice salahar Rahinat Ιinka waccen kuma Ζ΄ar basaja….”
itama bata kai aya ba Khaleed ya nunata da yatsa yace,
“Ζarya take Abii, ba itace Rahinat ba, ga Rahinat kusa dani…kamar yanda na gaya maki ni ba mutum ne mai son a Ιatawa lokaci ba, dan haka karki kuskura gaskiya ta fito daga bakin waΙanda nike tsare dasu domin bazaki ji da daΙi ba…..”
shima maganarsa ce ta tsaya lokacin da Mami ta jefo masa tambaya.
” kai taya kake da tabbacin cewar wannan ce Rahinat Aayan?”
STORY CONTINUES BELOW
Ιan saukar numfashi yayi ya miΖa hannunsa zai kamo hannun Rahinat tai saurin janyewa tana jifansa da harara.
kuma miΖawa yay zai kamota ta sake janyewa, gira Ιaya ya Ιaga yana kallonta, Allah sarki magana ce fal a bakinta take son fitar da ita amma ta kasa, yanda yake kallonta Ιin yasanya ta tsuke fuska ta kauda kai gefe.
_My Angel, kina son kice min zamu buga dramer dake bayan war-warewar wannan al’amarin kenan._
yay zancen cikin zuciyarsa yana mai murmushin saman leΙe
kowa Khaleed yake jira ya nuna evidence nasa na cewan Rahinat itace real one, dan haka kowa ya kafa masa ido yana kallonsa.
Raihan ko cike da Ζosawa da rainin hankalin daya ke ganin Khaleed zaiyi yace,
“shima munafikin karku yarda dashi domin ko Ζarya…..”
sai kuma yay shiru tinawa da cewan fa da Rahinat ai bata magana, ita kuma wannan gata harda zayyano bayanai.
Ammi tace, “Allah ya taimaki sarki Ζarasa faΙin abinda zaka faΙa dan Allah, kai Ιaya nake da tabbacin kasan Ζ΄ata a wurin nan, ba don kaiba ma bazamu san inda take ba”
“ehhh Ammi hakane, Rahinat bata magana”
“a’a Ζ΄ata ni tana magana, bata taΙa kamuwa da ciwon rashin magana ba…. dan haka indai har wannan ta hannun mugun sirikin nawa itace bata magana to tabbas itace Ζ΄ar basaja, wannan kuma itace Rahinatu nah
ta Ζarasa maganar tana mai tafiya ta rungume Raihana tsam ajikinta.
Abii ma ya sauke ajiyar zuciyar kamin yace, “Ζwarai kuwa zancenki haka shike Sa’adatu, Ζ΄armu tana magana so ba wani rainin hanΖali da za’a kawo mana na cewar bata magana”
Ammi cikin kuka take cewar, “Allah ya isa tsakanina da duk wanda yay silar shigarki wannan halin Rahinat, tinda kika faΙa ΖADDARAR SO kika haΙu da jarabta”
+
ta saki Raihana ta nufi inda Rahinat ke tsaye ta Ιaga hannu ta zabga mata mari,
“muguwa macuciya ,Allah ya isa cutar mana da yarinya da kikai kuma bazamu yafe maki ba sai munyi shari’a dake”
ta Ζarasa faΙi tana mai tankaΙa Rahinat baya ta faΙi a Ζasa.
tana zubda hawaye tayi saurin miΖewa ta kama Ammi, tana kuka tana kwatanta yanda kurame ke magana take ma Ammi bayanin, “wallahi nice Rahinat Ammi, karki yarda da waccen muguwar ,rashin maganata ma itace sila amma wallahi Ammi nice Rahinat”
kuma tankaΙata Ammi tayi ta faΙi Ζasa, “keni karki yaudaren da wannan zancen naku mai ban tausayi”
ta kuma miΖewa ta nufa Abii ta kama rigarsa tana ta masa bayanin bebaye amma shima saiya Ζara hankaΙata gefe.
kuka sose ta sake fashewa dashi tana tsugune, jinta take tamkar ta haΙiyi zuciya ta mutu ta huta da wannan sauyin rayuwa daya sameta,tinda ta haΙu da Khaleed zuciyarta ke cikin wuya har kawo iyau.
“ban san ta yanda zan masu bayani ba su yarda dani Rahinat, baki da wani abu da zan nuna masu su shaida kece Ιin tasu?”
taji maganar Raihan akanta, bata Ιago ta basa amsa ba kawai ta girgiza masa kai.
baki Ιaya ko su Uncle Badamasi dasu Suwaiba sunyi can kan Raihana, daΙi duk ya cikasu Abii har ya kira asibiti yace abama Hajiya ga Jikalle.
albishir Ιin kaΙai da aka mata ya farfaΙo da ita daga kwanciyar jinyar da take.
Maganar Waziri ce ta miΖar da Rahinat a razane tai wurin Khaleed.
“ai shiru mai martaba zai yanke hukunci”
hannu ta haΙa tana roΖon Khaleed ya taimaka mata, kafaΙa ya Ιaga mata ya kauda kai, hannu tasa ta juyo da fuskarsa tana murza hannayenta, cikin yanga ya kuma kauda kansa gefe.
ganin alamun shi wasa ma ya Ιauka abin ta dunΖule hannu ta dakeshi a Ζirji, sose yaji zafin dukan dan har saida ya shafa wurin.
kwai-kwayar yanda ta haΙe gira tai sama shima shima yayi, ganin hakan yasa ta kuma kai masa bugu a Ζirji d duka hannunta biyu.
“ashhhh dafa zafi”
ya faΙi yana mai kallonta, cikin kuka tasa tafukan hannunta ta turasa ta juya zata tafi ya janyo hannunta.
ΖoΖarin fizgewa take amma ya hanata.
“kina son su Abii su gasgata ke Ιin tasu ce?”
da sauri ta juyo tana Ιaga masa kai alaman ehh.
sautin muryarsa a Ζasa yace, “to karki kuma janye hannunki idan nazo kamaki, kuma kin yarda daga baya saina rama wannan dukan da kikai mani?”
fizgewa tayi zata tafi taji yace, “wallahi tallahi summa tallahi Abii idan har kuka kama zancen wadda kuke tare da ita to kun kama gaibu, ga real Rahinat nan amma wannan fek ce, idan har kuka tafi kuka bar Rahinat to baku mata adalci ba”
“zancen banza, babu wata magana da zan kuma yarda da ita ,yanzu haka ina jiran kotunku ta yanke mata hukunci ne kamin nima na haΙata da nawa hukumar su hukuntata a bisa basaja da tayi a matsayin Ζ΄armu harta sanyata cikin wuya
“rantsuwar da kai rantsuwa ce babba kuma rantsuwa mai haΙari, kasan hukuncin wanda yay Ζarya a bisa wannna rantsuwa, miye hujjarka akan hakan Khaleed?”
mai martaba ya jefo masa wannan tambayar, wani daΙi Khaleed yaji cikin ransa da kiran sunan da Mai martaba yay masa, domin kuwa yau shekara 7 kenan rabon dayaji sunansa a bakinsa.
“su matso data wurinsu kusa tukunna domin shaidar da zan nuna tana jikinta”
harsu Abii zasu musa mai martaba yace zai hukuntasu akan hakan tinda acikin kotun fadarsa suke dole subi umarninsa.
Ammi da Abii suka kamo hannun Raihana suka kawota tsakiyar fada, shima Khaleed kamo hannun Mami yayi dana Rahinat suka hauro zuwa tsakiya.
umarni ya bada da abashi kujera, cikin hanzari kuwa aka kawo lafiyayyiyar kujerar girma aka aje.
zaunar da Rahinat yay akai, da sauri ta yunΖura zata tashi yasa Ζafarsa ya danne tata, hannu tasa ta janye Ζafar da iya Ζarfinta, zata kuma yunΖurawa yay mata wani kallo daya bata tsoro, dan tana son kawai ya fittadata ne ta koma ta zauna amma bawai dan tana tsoron nasa ba.
fadawa yasa dasu miΖo masa Raihana,Ammi zata hana waziri yace mata “kul”
magana Khaleed ya fara, “Abii kaman yanda bayananta da naka suka fita tabbas haka komi yake, itama Ζ΄arku ce amma ba ba asalin Ζ΄arku Rahinatu ba, bayanin ta yanda gawa ta dawo mutum zatai maku daga baya domin ni yanzu burina na ceci rayuwar matata” ,
+
Ζasa ya zauna bisa carpet Ιin da aka shimfiΙa masa, “Abbi na faΙa son Rahinat batare dana son kowace ita ba, sannan na zauna da ita har na wahalar da ita cikin rashin sani duk batare dana san itace wadda zuciyata ke muradi ba, Abii wannan itace asalin Ζ΄arku Rahinat zan kuma baku hujjar da zata gamsar daku hakan”
ya Ιaga ido ya dubi Rahinat data Ζura masa ido yace, “zo nan”
kaman bazata taso ba sai kuma ta taso ta taho, kusa dashi ya mata nuni data zauna, har zataΖi sai kuma tai saurin zama dan ita tana tsoron dogarai.
tana zama ya kama fuskarta tare da juyar da fuskar tata gefen hagu, wata tusar jaki ce a wurin mai Ιan girma yace dasu Abbi,
“Abbi ka duba ta wajenka ka gani, bayan baiwar tusar jakin da Allah yay masu ta gefen ido akwai wata a fuskarta?”
Abbi ya duba yace, “a’a bata da ita”
ya Ιago da fuskarta ya masu nuni da wata tusar jakin dake haΙarta domin maganar da yay harya gaji,
nan ma Abii ya duba yace, “a’a”
nan Khaleed ya Ιan kwanto da Raheenat jikinsa ko kunya ya kamo hannun damanta dake gefe.kai-kaicewa Rahinat keyi tana son janye jikinta amma sai wani Ζara kwantota jikinsa yake, yatsunta ya kamo yay ma Abii nuni dashi.
+
a cikin Ζasaitar maganarsa yake cewa, “ya matsayin wannan yatsan yake a wurin Angel?”
da rashin fahimta Abbii yace, “wace kuma Angel ko wane?”
yanda kasan ta Ιarar da Khaleed haka taji, Ζwacewa tai ajikinsa ta Ιago kunya duk ta gama cikata,Raihana kam ji take inama itace da ba abinda zai hanata sake lafewa jikinsa, gaskiya Rahinat tayi sa’ar miji, kuma matsawar ta rasa *SULTAN AYAN* wato mijin Ζ΄ar uwarta haΖiΖa zata iya rasa ranta.
Nimrah ce ta bama Abbi amsar , “Abbi yana nufin Rahinatu”
“auho” Abbii ya faΙi yana gallawa Khaleed harara, saboda duk gidansu Rahinat kowa haushinsa yake ji.
Abbii ya duba Raihana yace, “miΖon hannunki”
Ζin miΖa masa tayi har saida ya kama da kansa tukunna, ganin yatsan cindo a hannunta ya saketa ba shiri, hannun Rahinat ya koma kallo.
“inaa wannan aljana ce ba Ζ΄armu bace, domin kuwa cindon yatsan dake jikin Ζ΄armu tin tana shekara 7 aka mata aikinsa aka yankesa, dan haka Sa’adatu ta wurinsa itace Rahinat Ιinmu”
kamin Ιaya daga cikinsu ya kuma magana Raihana ta Ιauka.
“niba aljana bace Abbii mutum ce mara gata mara asali tinda ban san iyayena ba, haΖiΖa da ace nasan da wannan sheda da Sultan Khaleed zai nuna to itama dana bi hanyar da muka zama iri guda da Rahinat”
ta duba iyayen nata tace, “Ammi! Abbii! ku amsa laifinku ko karku amsa amma saida Ζ΄arku kukayi ba mutuwa tayi ba…”
idan da lafazin dake Ζona ran Abbii ya biyo bayan wannan, yatsa ya Ιaga yana nunata ta kama ta sauke , kamin yay magana ta Ιora,
“Ammi! Abbi! ku yarda ko karku yarda nima Ζ΄arku ce”
ta zira hannu cikin rigarta ta fito da hoto ta Ιaga ta nuna masu.
“wannan shine hoton da aka bani akace sune iyayena, kuna so shima kuce min yanda kuke da kokonto kanmu haka abin yake?”
hannun Abbii na rawa ya fizgi hoton yana kallo, mamakinsu duka ko a yanzu basu da ajiyar pix Ιin nan saboda tin na amarcinsu ne.
ta kuma Ιauko wani shima ta Ιaga, fizgarsa shima Abbii yayi yana kallo, hoton da sukayi a england ne suda yaran, lokacin tin Rahinat batai aure ba.
“dan Allah ki faΙa mana tsakani da Allah wace ke kuma aina kika sami waΙan nan hotuna?”
_”ni yarinya ce wadda ta taso agidan marayu batare da iyayen da suka haifeta ba, na taso cikin kulawa da Ιawainiyar wadda aka saidani a wurinta, ta bani ci ta bani sha ta kuma sanyani a makaranta harna girma na kai shekara 12 wanda alokacinne nasan ainihin wace ni” ,_
_”yanda naga wasu marayun suna samin ziyara daga Ζ΄an’uwansu shiyasa na tambayi Mama wato uwar marayu wadda ke Ιawainiya damu, ina kuka nake roΖonta data taimaka nima asamo mani Ιan uwana koda mutum Ιaya ne na gansa tinda Mamana da Babana sun rasu, tana lallashina take shaida mani na kwantar da hankalina soon zanga jinina, ina murna na share hawayena naita mata godiya” _
_”faruwar haka da sati guda saiga wata dattijuwar mata ta kawo mani ziyara da kayan hidimarta masu yawa,naji daΙi matuΖa saboda tinda nake ban taΙa samun kaya irin wannan ba kai kace ma ba gidan marayu nake ba, da zata tafi kuwa ina kuka nace mata dan Allah ita Ιin wace a wurina? ta gyara tsayuwarta kamin ta sami wuri ta zauna ta fara faΙa min tarihi na, ta dafa kafaΙa cike da tausayawa tace dani” ,_Raihana, ni ba kowanki bace,ni da kike ganina sunana Hajiya Safna kuma agarin niger nike da zama, watarana kwatsam na kai ziyara asibitin gamkalley sai naci karo da wasu bayin Allah mata da miji sun sami arziΖin haihuwar Ζ΄aΖ΄a biyu duk mata, muka gaisa dasu na tayasu murna na wuce inda zani, to bayan na shiga ciki na gama abinda zanyi na fito saiga wannan matar tazo min da son in taimaka mata, nace mata mai take so tace dan Allah suna so su sayar da Ζ΄arsu guda Ιaya ne, cikin Ιimbin mamaki nake kallonta da kuma haushi kamin na watsa mata tambayar dalili, nan mijinta yake cemin suna da kuΙi iya kuΙi sai dai bazasu iya rainon Ζ΄aΖ΄a biyu alokaci Ιaya ba dan haka suke son sayar da Ιaya cikinsu, ni kuma batare dana kuma bari maganar tasu taja ba na tambayesu babu matsala dama nima ina biΙar Ζ΄a saboda Allah bai nufeni da haihuwa ba amma nawa zan basu na amshi Ζ΄ar, matar tace dani ko nawa ne suna so indai zasu rabu da Ζ΄ar saboda ita raino yana mata wuya, na rubuta masu check na naira million goma na miΖa ma mijin, da mamakina sai naji yace sunyi yawa saboda Ζ΄arsu bata kai tsadar da zasu saidata haka ba, kai infact ma shi yafi Ζarfin wannan kuΙin dan haka kawai idan da kuΙi jikina na basu, na buΙe jaka na Ιauko dubu Ιari uku na basu, sai mahaifinki ya rage dubu Ιari yace sun barmi a dubu Ιari biyu, daga nan matar ta sakko mani dake daga bayanta ta miΖo mani mukai sallama dasu sunata farinciki. to dana koma gida ni kuma anan na tarar da Ζalubale daga wurin mijina na cewar bazan shayar dake ba saboda bai amince ba wanda ba Ιan cikinsa ba yasha nono na, naita bashi haΖuri amma fafur yaΖi haΖura, ni kuma alokacin tausayinki da Ζaunarki sun addabi zuciyata ina jin har saidai mu rabu dashi amma bazan iya barinki ahaka ba, ya kafa ya tsare bazan zauna masa agida ba na tashi na maidaki inda na amsoki, kinata tsala kuka abin tausayi na koma wannan asibiti, koda naje sai mukaci karo da iyayenki an basu sallama zasu wuce gida, nan nayi masu bayanin komai amma sukace su basu san wannan ba Ζarshema basu kuma saurarata ba suka shiga danΖareriyar motarsu suka tafi suka barni anan, to na rasa ya zanyi na rasa mafita kawai saina yanke shawaran kaiki wurin mahaifiyata dake a garin Jigawa, a daren wannan rana na kawowa mahaifiyata ke domin ta kula dake to amma itama sai muka sami matsala ta rashin ruwan nono da bata dashi, Ζarshe dai muka yanke magana akan kawai akaiki gidan marayu, washe gari da asuba na kaiki asibiti saboda kwana da kikai da zazzaΙi aka dubaki tare da baki magunguna sannan na kaiki gidan marayu na nan jigawa state, duk Ζarshen mako ina zuwa na ganki domin tabbatar da irin kulawar da ake baki har zuwa lokacin da kika fara girma ni kuma ayyauka suka mani yawa alokacin bani samun daman zuwa jigawa akai-akai shine na barwa Hajiya Saddiqa amanarki, to kinji labarinki Raihana”_
+
_”lokacin da Umma nah ta gama bani labarin kuka nake sose, tambayar da nayi mata shine waya raΙa min sunana? tace dani iyayena, su suka shaida mata an mani huΙuba da Raihana Ζanwata kuma Rahinatu, na kuma tambayarta dan Allah kota san sunan iyayena tace mani ehh Alhji Abdullahi Matawalle da Hajiya Sa’adatu, tambaya ta uku dana mata shine kozan iya samun hotonsu, take tasa hannu ga jakarta ta Ιebo mani hotuna biyun nan, anan na san inada wasu Ζ΄an’uwan bayan Rahinatu, tin daga wannan lokaci kuma a wannan rana naji na tsani iyayena da kuma Ζ΄ar’uwata da aka haifemu tare, naji na tsani garin da aka haifani na kuma ji na tsani garin jigawa wanda ban san dalili ba…bayan tafiyar Umma nah da wata Ιaya nai satar kuΙi a jakar Mama na bada aka sayo min rago nzan sauya suna to kuma saina fasa, Umma Nah naima waya nake faΙa mata ni zan bar Ζasar nan baki Ιaya zan koma wata Ζasar na fara
sabuwar rayuwa, nan ta bani haΖuri har saida tazo gidan marayu, to anan mun taho hanyarmu ta niger sai muka tarar da wasu mutane masu sayan bayi suna kaiwa Ζasashe da garuruwa, anan Mama ta saidani muhallina ya sauka anan Ζasar Libya cikin masarauta, daga wannan rana na zama baiwa nake aikace-aikace sai daimi, tinda nazo zuciyata ta kamu da son mutumin da bai son hayaniya baison mutane sam, kyakykyawan namiji jinin larabawa, son samun duk wace mace datai tozali dashi, mai tsananin tausayi da kyautatawa, domin duk aikin da mukesha idan yazo zaice a barmu mu huta, wasa-wasa sai ΖADDARAR SO ta afakamin domin banda tabbacin zan sameshi tinda ni Ιaya nake kiΙi da rawata, mai gaba Ιaya ma dai bazan sameshi ba saboda babu gami auran SULTAN da kuma BAIWA, kwana atashi ciwon ΖADDARAR SO na SULTAN AYAN ta nemi taimin illa, uwar Ιakina SULTANA YASMEEN ita ta lura da irin wahalar ciwon da nake fama dashi saboda na koma baci babu sha, tasa likitan masarauta ya dubani nan ya bata tabbacin na kamu da ciwon zuciya tare da hawan jini sose, ban damu ba kuma hankalina ko kaΙan bai tashi ba saboda nasan dalilin ciwona kuma koda cutar data fisa zan kamu da ita” ,_
_”agaba uwar Ιakina tasani da tambayar kan dole sai na gaya mata meke damunwa har ya haifar manida waΙannan ciwon, gaskiyar magana ban Ιoye mata son Sultan Aayan daya kamani ba har ya haddasa min ciwon zuciya sai dai kuma ban gaya mata ciwon da iyayena suka haddasa mani na hawan jini ba, da taimakonta da taimakon magungunan da nake sha na fara samin lafiya amma kullum zuciyata da ruhina basa barin tinanin Ιan gatan masarautar Libya da kuma abinda iyayena suka mani, kowanne dare mafarkina da tinanina yana Ζarewa ne akan hanyar da zanbi na sami Sultan Khaleed kota halin ΖaΖa sannn kuma na Ιauka fansar zaluncin da iyayena suka mani, kwatsam ina zaune watarana na mun gama hidimar cikin gida ina Ιan hutawa saiga jakadiya tazo kirana inji Sultana Yasmeen, naje na sameta take shaida min ga maganin damuwata, zasu haΙa sharri wanda suke son na bada gudunmawata akai to tana mai tabbatar min da zan sami auran Khaleed, ina zare ido nake tambayarta abinda zna aiwatar, abinda tace mani shine basu so Sultan ya sami sarautar da Mai martaba yake son bashi a gobe, MAKIRCI shine abinda kawai zai dakatar da Mai martaba ya fasa aiwatar da abinda yaso, zaiji ya tsani Khaleed amma ke kuma zaki sami Khaleed a wannan lokacin, ina farin ciki ina murna nake tambayarta me zan aiwatar na sami auran Sultan duk kuwa acikin zumuΙi nike tambayar tata, abinda ta shaida mani shine zasu sanya abu cikin drink nashi ni kuma alokacin zan aiwatar da nawa aikin” ,_
ta numfasa kamin nan ta Ιago ta kalla Maimartaba da yay kasaΖe yana sauraron zantukanta, taci gaba da faΙin,
_”kaman yanda na shaida maku a baya abinda ya faru tsakanina da Sultan Sharri ne, ehh tabbas haka yake sharri ne domin kuwa babu wani abu daya faru, kawai dai sun sanya masa abinda zai kawar da tinaninsa ne tare da tada sha’awa, sam abinda kukaga yana aikatawa bai cikin hayyacinsa kaman yanda duk nayi maku bayani a baya, wallahi tallahi dana san abinda zan aikata bazai sa na sami Sultan Khaleed ba to da ban aikata ba, da banyi abinda zaisa a nisanta idanuwana daga ganinsa ba saboda ina tsananin sonsa, hankalina bai kuma tashi ba sai bayan tsawon shekaru da aka Ιauka baya tare damu najin labarin auransa, ko alokacin ciwon zuciyata sai daya tashi,Sultana Yasmeen ita tayi Ιawainiyar maganina saboda a lokacin lallamani take gudun karna tona mata asiri, na kasa jurewa har saida na samo hoton bikin Sultan da matar daya aura, daga lokacin dana ga fuskar mai kama dani a wannan lokacin na Ιaura Ιamarar Ιaukar fansa mai tsauri, bayan tsanar da naima 2wins Ιina gashi yanzu tazo ta aure farinciki na wannan ya nuna min tabbacin ita da iyayena MaΖiyana ne basa sona ko kaΙan, take anan na fara tinanin abinda zanyi kala-kala wanda zansa rayuwar Rahinatu acikin Ζunci da wuya, wanda zaisa taji inama batazo duniya ba, take nan na yanke shawarar tonama take nan na yanke shawarar tonama kaina asirin Ζazafin dana ma Sultan domin Rahinat ta maye gurbin azabar hukuncin da za’a mani saboda inada tabbacin Mai Martaba bazai yi hukunci mai daΙi ba”_
+
sai kuma ta fashe da kuka sose mai cin kamin ta kada baki tace, _”Allah sarki Khulaid shine abokina a wannan masarauta, tinda mukazo muke tare har muka fara soyayya dashi, yana matuΖar sona sai daini kuma soyayyar da nake nuna masa yaudara ce, shine wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin na Ιauki fansar abinda iyayena suka mani da kuma aure mani miji da Rahinatu tayi, Ζarshe azzaluman cikin masarautar nan saida suka kasheshi kisa na walaΖanci kuma duk saina tona maku asiri, Allah ya jiΖanΖa Khulaid…..”
bakinta ne ya rufe sakamon jin muryar Khulaid yace, “ban mutu ba in araye Raihana”
ta Ιago da sauri ta kallesa, ya Ιaga mata kai da kuma cewan, “Ζwarai kuwa ina raye ban mutu ba, gawar wancan bani bane potocopy nane”
kukanta ne ya maye gurbin dariya, “ni kaina nayi mamaki da akace waΙan nna Ζananun Ζwarin sun kasheka, nai mamaki sose dan nasan wane kai Ιin”
police prisoner Ιin dake tare dashi ne ya Ζarasa cire masa Ιaurin fuskar da aka masa, nan ya fuskanci Ζhaleed dake masa wani irin kallo, ya Ιora da maganar Raihana daga inda ta tsaya.
_”ka kamani ne Sultan Aayan dan kawai jin yanda akai mukaje gidanka har muka sauya maka mata, tabbas munyi hatsabibanci sose a rayuwa nida Raihana, saboda yanayinmu yazo Ιaya, ni banaji itama bataji, kuma sai abin yazo da Ζaunarta da nakeyi wanda komine zan iya aikatawa domin samar mata da farinciki da jin daΙi, tin lokacin data yankewa kanta shawara da dabarar zata tonama kanta asiri a wannan lokaci ta shiga damuwa saboda bata san ta yanda za’ai ta Ιauko Rahinatu ta maye gurbinta ba, ni kuma ganinta acikin wannan damuwa na fito mana da wannna hanya, nasa ta Ιauko kuΙaΙe da gwala-gwalan da Sultana Yasmeen ta bata muka saida muka haΙa kuΙin mukai jirgin zuwa nigeria, kwananmu uku a nigeria muka fara neman inda kuke, ta hanyar address naka dake goggle muka sami bayanin komi, watarana mun dawo daga hotel muna Ζofar gidan mahaifiyarka sai gaka ka fito akan bike naka, Raihana ta fita da sauri taje wurinka saika sanya Ζafa kai fatali da ita a Ζasa ka Ζara gaba kana zuΖar siggaret, kamin na fito nazo na Ιauketa akan hanyar daka wullar da ita saiga Nimrah Ζanwarka ta fito zata fita anguwa sai ta ganta da sauri ta fito a mota ta nufeta tana kiran Ukhty, cikin rashin sani na cewar ba Rahinat bace ta kamata suka shiga gida, a zaman da sukai Nimrah na lallashinta da bata haΖuri anan Raihana ta fahimci cewar ba auran soyayya kukai da Ζ΄ar’uwarta ba kuma inda wadda ka tsana shine Rahinatu, ta nan muka Ζara samun more idea na gabatar da aikinmu, Mahaifiyarka da kanta ta kai Raihana har gidanka ni kuma ina biye da ita a baya, Allah ya taimaka bata shigar da ita har cikin gidan ba ta ijjeta kawai a bakin gate ita kuma ta koma gida, tana juyawa Raihana ta dawo ta shigo motata daga nan muka fara tinanin abu na farko da zamuyi, anan ne muka saye mai gadinka da maΖudan kuΙin da muka sata acikin wannan masarauta, bayan kwan abiyo mahaifiyarka ta wuce saudiya zuwa gidansu a wannan rana muka sami damar shiga gidanka”_mun saye mai gadin gidanka da million biyu, hakan ya bamu damar kutsa kai ciki a dai-dai lokacin daka damΖo matarka kan cewar lalle saita faΙi maka yanda akai Ζazafin data maka ya faru”._
+
Raihana ta amsa, _”lokacin daka fito waje da ita domin sata cikin Ιakin karnuka dan horata, ka juya ka shiga gida ni kuma a lokacin nasa Ιankwalin dake hannuna na rufe mata baki, wata allurar da muka yo odarta mai karayar da lafiyar jiki ita muka mata a maΖogaro sannan mua tusa mata wani ball acikin baki har sai daya kai maΖoshinta, wanda wannan likita ya tabbatar mana da zai hanata magana har sia lokacin da akai aikin ciresa shima sai an taki sa’a mutum zai dawo da maganarsa, kamin fitowarka na maye gurbinta shi kuma Khulaid ya kinkimeta ya fita da ita, nasan saboda baka Ζaunarta yasa baka gane ban-bancin dake tsakaninmu, domin da zaka gane da kayan dake jikinmu, a son samu na na kashe Rahinat har lahira to kuma saina tina da Ζuncin rayuwar dana kasance aciki tin ina jaririyata, hakan yasa nace da Khulaid ya maida ita Libya ta maye gurbina domin itama ta Ιan-Ιani wahalar rayuwa…hakan ko akai ita tana can wanda ban san a halin da take ciki ba kasancewar babu waya hannuna, ni kuma inan Ιakin karnuka kana ta azabtar dani iriri har na fara kasa jurewa raΙaΙin azabar da kake mani, bayanan dana rattabo maka a wannan lokaci duk nice ba Rahinatu ba saboda ita bata san komi game da hakan ba, nayi hakanne domin ka Ζara jin tsanarta aranka ,saboda ina so yanda na rasaka itama ta rasaka,shiyasa nayi amfani da damar cewar ka sake ni wanda naso alokacin ka furta min kalmar saki ko kuma ka rubuta takarda”._ ,
_”ranar dana ji bazan iya bane duba daka na neman halaka ni na faΙi maganar da zata Ιaga hankalinka saboda nasan duk duniya babu abinda kake so sama da mahaifinka, daga nan na sami damar dana gudu daga gidanka, ina cikin wannan gudu kuma mota ta kaΙeni, wasu bayin Allah suka Ιauke ni dasu da wanda ya kaΙeni, na kasance cikin kulawarsu tsawon watanni shida duk da cewar Ζalau nake bawai cuta nake ba amma saboda wata manufa tawa yasa nayi lamfo har tsawon wannan watanni, ban farka ba sai ranar dana ji ana Ζishi-Ζishin fitar dani Ζasar waje domin binciken lafiyata”_. ,
ta Ιago ta kalla Raihan da yayi lakato yana kallonta yana sauraron irin rashin imani nata, Ζ΄ar dariya tayi sannan tace ,
_”Sultan Raihan kayi haΖuri domin kaima na nuna maka nawa hatsabibancin, wayarka da kake tinanin ta faΙi alokacin daka na Ιawainiya dani a asibiti ba faΙuwa tayi ba ni na saceta saboda ina da buΖatar yin waya da Khulaid naji halin da ake ciki, ya shaida mani Rahinatu na cikin mawuyacin hali dan yanzu haka ma farfaΙowarta ake jira daga dogon suman da ake tinanin tayi wanda a zahirin gaskiya ba suma tayi ba, ni da kaina na zuΖe jinin jikinta gami da mata allurar bacci ta tsawon wata guda, ya shaida mani Abu Ayan wato shugaban Ζasarmu ya sanar ma da mai martaba abinda ke faruwa, shi kuma yasa an kafa an tsare Rahinatu zuwa lokacin data tashi ta zayyano masa magautan cikin wannan masarauta, ranar da muka dawo Ζasar Libya bayan Khulaid ya Ιauko ni koda na shiga harabar Sultana Yasmeen abinda na jiyo shi ya Ιaga min hankali, tin ranar da Umma ta faΙa min tarihi na naji zuciyata ta ΖeΖashe da tausayi ko so na iyayena da kuma Ζ΄ar uwata da muka fito duniya a tare, amma ranar sai naji tausayin Rahinatu ya kamani har bazan iya barin su Sultana Yasmeen su aiwatar da abinda suke sonyi ba na Ζudirin kasheta”._ ,
ta maida kallonta ga Abie dake zaune kan kujera kusa da mahaifinsa wato Mai martaba.
“Abie gidanka shine gidan shugaban Ζasar nan wanda ke kewaye da dakarun tsaro na tashin hankali, wanda tinda nake ban taΙa ji ko labarin inda ake bawa tsaro ba irin wannan gida, amma sai gashi a hatsabibanci na dana Khulaid sai da mukayi mafakar da zamu dinΖa shiga cikin gidan, ta bayan gidanka muka haΖa ramin da zai dinΖa sada mu da shiga ciki a duk lokacin da muka so, duk wasu jami’an tsaro dake mutuwa ba kowa ke kashesu ba saimu, hatta ranar da muka saki
harbi aka tada tiergas mune ba kowa ba shine a wannan lokacin na koma asalin wurina da Raihinatu ta maye gurbinsa, su Sultana Yasmeen sunzo gidanka a wannan lokaci, inda suka rigamu sa’ar Ιauke Rahinat suka gudu, gudun kar a sami Ιacin rana na maye gurbinta, tare da taimakon likitanmu ya min allurar bacci ta wata guda, Khulaid kuma ya bini da duk wani bandage”._
+
Khulaid ya amsheta, “bayan fitowata a wannan lokaci shine nabi diddigin inda su Sultan Dameer suka nufa ta wurin jakadansa wanda duk abinda ke faruwa yasan komi bayan na sayesa da gwala-gwalai, a lokacin da suka kai Rahinat asibiti sonsu a kasheta sai Allah ya kaini kamin lokacin, a zahirin gaskiya bani bane, Jakadan Sultan Dameer na sanya akama plastic surgery zuwa irin kamannina, shiyasa koda suka kasheshi suka Ιauka nine, ban san taya har suka Ιauke Rahinat ba ta dawo hannun masarauta saboda ni tin a wannan lokacin da naje asibitin naga ba ita kawai sai nayi tafiyata sbaoda nima na fara tsoron tonuwar asirinmu domin bazanji da daΙi ba a hannun wannan masarauta, sai a shekaranjiya da na gaji da jin labarin irin halin da Rahinat ke ciki na fito domin faΙar gaskiya, koda naje station sai na tadda Inspecter suna bincike akan hakan wanda Sultan Ayyan ya umarce su da suyi, ta haka aka kamoni aka kawo ni hannunsa”._
“Ya Mai Martaba duk fitinar data faru acikin wannan masarauta ta faru ne silar Ζ΄aΖ΄anka, basu kowa bane magautan wannan masarauta face Ζ΄aΖ΄anka, ba kowa ke son ganin bayanka, bayan Ιanka Morad, bayan jikanka Aayan face Ζ΄aΖ΄anka guda 6 wato Sultan Dameer,Sultan Baheer,Sultan Salman, Sultan Abid da Sultana Yasmeen”._
Raihana ta faΙa.
Khaleed take kallo wanda yake mata kallon jin haushi da tinanin irin fansar da zai Ιauka kanta na cutar masa da Angel.
“Sultan Khaleed nayi matuΖar mamaki da ka gane cewar wace ni, taya akai kai mani basaja, kuma ya akai kasan ni Ιin ba matarka bace?”.
bai bata amsa ba sai neman hukunci daya buΖaci Mai Martaba yayi, ba akan Ζazafin da aka masa ba, akan cutar da akaima Angel Ιinsa.
nan take Mai Martaba ya bada izinin a shigo masa dasu Sultan Salman kaf Ιinsu, aka kawo kowa amma babu Sultan Dameer, hankalin Raihan a tashe yake Ζololuwa, ya rasa wanna irin hali mahaifinsa yake dashi na hassada da Ζyashi, yanzu gashi ya gudu, ko inya gudu ina zashi.
yana wannan tinani yaji Khaleed na bada umarnin a kuncewa waΙanda yasa aka zo dasu fuska, da mamakin kowa fuskar Sulatan Dameer ta bayyana da kuma Mai gadin gidan Khaleed.
doguwar ajiyar zuciya Raihan ya sauke, gefe guda ya juyar da fuskarsa yana runtse ido.
jin saukar hawaye jikin Khaleed ya waigo daga kallon Dameer da yake, Rahinat yaga tana kuka sose, ido ya runtse yana mai jin zafin zubar hawayenta, Ζaramar rigar dake saman jallabiyar daya sanya ya cire, fuskarta ya tallafo ya shiga goge mata fuskarta da wannan rigar.
hannu yasa ya kwantota jikinsa yana mai shafa kanta alamu na lallashi, Ζwacewa tayi tana galla masa harara, tashi tayi a wurin nasa ta nufa inda Raihana ke zaune tsakiyarsu Abbi.
kamo hannunta tayi ta wani Ζwace a fusace.
cike da tsantsar tsana take kallon Rahinat tace, “du faΙin duniya babu wanda na tsana sama dake Rahinatu, karki Ζara kusantoni, ki barni nima yau naji Ιumin azzaluman iyayena da suka gujeni duk da cewar ba sonsu nake ba”.duka da mamaki su Ammi suke kallonta da jin Ιacin kalamanta, Abbi banda sarawa da kansa yake babu abinda yake ji, wacce macece wannan tayi munaΖisar raba shi da Ζ΄arsa harta Ιata masu suna a wajenta, mai suka mata ita kuwa a rayuwa. +
Ammi tana hawaye ta jefowa Raihana tambayar, “Raihanatu idan har kin gasgasata cewar Allah Ιaya ne kuma haΖiΖa babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi, to ki yarda wallahi summa tallahi bamu sai daki ba, duk abinda aka faΙa maki sharri ne, amma munji mun yarda a yanzu mun amsa laifinmu mu kamin gaskiya tayi halinta”.
Ammi ta sakko Ζasa ta haΙa hannayenta biyu tace da ita, “na roΖeΖi da Allah ki faΙa min matar data gindaya maki wannan Ζaryar, ki faΙa min azzalumar matar data rabamu dake”.
cikin tsawa Raihana ta dakatar da Ammi da cewan, “Ammi karki sake kuma karki kuskura ki Ζara gangancin kiran Umma na da azzaluma, duk wata azzaluma a duniya to ta biyo bayanki amma badai Umma nah ba”.
bata ankare ba taji saukar wani lafiyayyaen mari saman kuncinta.
a Ιimauce ta Ιago ta kalla Abduljjabar wanda ke tsaye kanta yana faman huci, wani marin ya Ζara mata wanda yay silar sata suman zaune.
“dan kutumar ubar uwar data raineki duk irin haukan da kike ji dashi na taka ki na dameki, banza jahila kawai”.
juyawa yayi ya amsa wata lafceciyar dorina a hannun dogari, take ya shiga lafta mata tana ihu, duk yanda aka so a hana shi kuma a Ζwaceta amma abin ya gagara.
sai da Ammi cikin kuka tace dashi, “Abdul ko k aΖyaleta kona maka baki”.
ta faΙi masa domin tsoratarwa saboda taga yana neman yin kisan kai, sai wani tattake ta yake yana laftarta da iyaka Ζarfinsa.
daktawa yayi yana huci, da yatsa ya nunata yace, “karki kuskura kice min baki dashi, in kuwa ba haka billahillazi wannna haΖora talatin da biyun dake bakinki saina zubar maki dasu yanzu anan”.
ya miΖa mata hannu yace, “ki bani hoton shegiyar uwar taki da kike wa uwar data haifeki gargaΙi akanta”.
ai duk ta gama tsorata da yanayin Abdul, dan haka kuwa ba shiri ta zira hannu cikin rigarta ta Ιauko hoton ta miΖa mas ahannu na rawa.
fizga yayi ya warware shi yana dubawa, hoto ne daka rubuta my swt mother ajiki, duban fuskar hoton da zaiyi yasanya sa sakin dukkan abinda ke hannunsa ya kuma ware ido yana kallo.
ganin haka duk su Abbi suka yo kansa suna tambayarsa wace, Uncle Badamasi ya kalla wanda daka kalla fuskarsa kaga wanda Ιacin rai ya gama cikata da kuma tausayi.
a hankali cikin tashin hankali ya furta, “Anty Asma’u”.
suma su Abbi da Uncle Badamasi suka haΙa baki, ” Asma’u kuma, kana nufin Antynku?”.
ya Ιaga masu kai alaman ehh, amsar hoton daga hannunsa Ammi tayi ta kalla, itama da Ιimbin mamaki da al’ajabi ta furta, “Na shiga uku Asma’u”.
sai kuma ta fashe da kuka, “Asma’u dama Ζiyayyar da kike min har ta kai haka, Asma’u me nayi maki a rayuwa ni kuwa”.
ta zube gwiwoyinta a Ζasa tana mai zubar hawaye.
Uncle Badamasi ya kalla Raihana yace, “kin tabbata itace matar data sayeki a hannunmu?”.
ta Ιaga masa kai tace, “ehh, kuma bani da kamarta a duniyar nan”.
ai take jiki na rawa Uncle Badamasi ya Ιauko waya a aljihunsa ya dannawa Nawwara kira.

Post a Comment for "YAREEMAH KHALEED CHAPTER 6"