Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC.
Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako
ƘARFE A WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL
⚔️*🔥ƘARFE A WUTA🔥*⚔️ MALLAKAR AISHA ADAM (AYSHERCOOL) *Labarin ƙarfe a wuta, ƙirƙirarran labari ne, idan yayi
kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.* Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai
da izinina❗ Page 1 Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar
gudun AC. Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar
masu jiran wani sakamako. Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta,
fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali,
fuskarta tayi sharkaf da hawaye. "Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan
sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?" Cikin ƙulewa wata babbar mace ta ce "Dama wani sakamako
ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta taɓa mage ba, abun da
na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa,
yanzu ta nuna maka ita ƴar kunama ce" Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da
nadamar abubuwan da suke gudana…