CANJIN RAYUWA CHAPTER 22 BY HALIMA A K/MASHI
da fada maka, laifinka ne kai da Nafisa ba. Kun gina ta a kan yi mata duk abin da take so. Ya kamo hannuwarta, na yarda laifina ne. Nafisa ta biye min ne don ganin hakan nake so. Abba ya ce, to Dady ka ce ta dawo mana. In yaso ka ba ta shi wanda take so din, tunda Na’ima za ta auri wanda ba ta so din. Ya kalli Abba, ba canji ke nan. Zan ci gaba dayi mata abin da take so ke nan? Ai yadda ba ta yi min abin da nake so ba, haka nan ba zan tabayi mata wanda take so ba. Ai ta yar da wannan gatan da kanta. Ita ma zan mata abin da ba za ta manta ba, kamar yadda ni ma ba zan manta da abin da tayi min ba. Hajiya Sauda ta ce, yanzu a ina take? Oho! in ji Alhaji. Jiya dai an ce suna Kaduna. Hajiya Sauda ta ce, Allah ya kauta. Daidai lokacin wayarsa ta yi ringing, sannan Momy Nafisa ta shigo tana cewa, Alhaji kana da baki.Duk tare suka fito. Hajiya Sauda dasu Hasana saman Mimi suka nufa saboda gidan da mutane. Har an soma cin abinci. Dangin Momy Nafisa sun fi yawa. Usaina ta kalli Hajiya Sauda bayan su…