CANJIN RAYUWA CHAPTER 19 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 19 BY HALIMA A K/MASHI yi. A kan Zainabu kuma tace kar ya damu, kila ita din ba alheri ba ce a gare shi. Ta ce, in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma Islamiyyar. Ya ce, shi ma tunaninsa ke nan a yanzu. Sukayi bankwana, bayan ta ba shi wani turare mai kamshi. Ya fito Mahmud ya kai shi tasha. Bai samu motar Abuja kai tsaye ba, don haka sai ya hau ta Kaduna. Suka miki hanya, zuciyarsa da rauni, bai san lokacin da zai warke ba. Hajiyar Mardiyya, matar Alhaji Isa Mani, abokin Alhaji Bashir ita ce ke kwada: sallama a falon Hajiya Sauda. Hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce, “sannu da zuwa Maman su Nabila.” Ta ce, “yawwa Hasina. Hajiya fa?” Ta ce, “bari in duba ta.” Nan Hajiyar Mardiyya ta zauna kan kujera. Hasina ta fito ta ce, “tana wanka ne. ” Hajiya Mardiyya ta mike, “bari in shiga cikin dakin.” Kawaye ne sosai, har yanzu ba su yada juna ba, don sun fi mazan nasu zumunci, har da matar Alhaji Kabiru, Hajiya Ramatu, abo…