MUSABBABI CHAPTER 13 BY HAJ HABIBA
A hankali garar da Malam Mahmud ya yima Afrah suka Kare, ya zamana abincin da Afrah za ta ci ya fara yi mata wahala, tunda Musaddik baida inda zai sami abinda zai ciyar da ita, idan ma ya samun, su kan Kare ne a wajen shaye-shayensa. Ta bangaren Hajiya Kilishi kuma ko faranti daya na abinci ba ta iya ba ta balle har ta sa ran za ta taimaketa da wanda za ta dafa. Ba ta iya taimaka mata da komai, sai wulakanci da cin zarafi, shi ya sa gaba daya ma ta daina shiga cikin gidan Hajiya Kilishi. Amma duk da haka, duk ‘yan aikin da Hajiya Kilishi take da su, haka nan za ta aiko Afrah ta je ta sa ta aiki kuma ko a gabanta aka gama abinci, ba ta yarda a zuba mata ta ci. Haka za ta gama aikin, ta koma bangarenta da yunwa. Wani lokacin ne ma idan ta je Islamiyya. Ya Sayyadi kan ba ta kudi, su ma da kyar take amsa, don kudin daya ba ta gudunmawa da ta yi niyyar ta. yi sana’a da su ne. Amma tuni suka kare, saboda zararsu da take tana yin hidimar gidan. Da kuma Musaddik ya fahimci akwai dan wani abu a han…