CANJIN RAYUWA CHAPTER 16 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 16 BY HALIMA A K/MASHI irin shi ne masu yin magani ba.” Ta ce, bari ka ji abin da ya ce min. Nan ta fada masa yadda suka yi. Ya ce, “ok, ki kira shi yanzu. Sai dai ina son ki sani ba mu da isasshen lokaci, saboda kullum kwanakin aurenki Kara kusantowa suke yi.” Ta ce, “to bari in kira shi. Zan fada maka duk yadda muka yi.’ Ba tare da wani dogon nazari ba, Mimi ta soma kiran layin Isma’il. Ya gama shafa’i da wuturi ke nan, yana kwance kan dardumar duk hankalinsa ya koma. Katsina, gani yake yi kamar akwai abin da Mahmood yake boye masa. Yana ganin cikin satin nan zai koma gida. Karshen wata ya yi masa nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare. Ringin din wayar shi ne ya katse masa tunani. Cikin sauri ya duba, bai san lambar ba, amma yadda ya ga lambobin ya san cewà na musamman ne. Ya daga tare da sallama, ‘yar siririyar murya ce ta amsa da “Hello!” Ya sake yin sallama, ta ce, “nice Mimi.” Ya ce, “ba ki amsa sallamata ba, wanda ya kasance amsa sallama wajibi ne a ciki…