MUSABBABI CHAPTER 6 BY HAJ HABIBA
Haqiqa akwai abinda Kawunka ya hanga yake son ya hada ka da Afrah aure, domin tabbas! Aure a yanzu bai dace da kai ba, illa iyaka wata manufa da yake da ita, idan yana tunanin dan abinda ya rage maka na daga gadonka ne yake son ya had auranka da ‘Yarsa, don su kwashi rabonsu. Ai ya kamata ka yi masa bayanin cewa ba ka da sauran komai, domin abinda ya ragen ka dade da dagawa ka sayar, ka yi shaye-shaye da kudin, babu abinda yarsa za ta aura, sai Musaddik da wahalarsa. Hankalin Musaddik ya tashi ko kadan baya jin dadin maganar da Hajiya Kilishi take yi ta cin fuska da wulakanci, ya yi Kasa da kansa, ransa na Kuna, a yayin da ta ci-gaba da magana. “Ni wannan yarinyar ko kadan ba ta burgeni ba, ba ta ba ni sha’awa, don haka ba na murna ko maraba da auranka da ita Ya dago ya kalleta sosal sannan ya ce.Hajiya ke ce mutum na farko a duk duniya da na taba jin kin ce Afrah ba ta burge ki, domin Afrah tana burge kowa, ko ba don kyawun fuskarta ba, don kyawun halayenta da natsuwarta, dole ta burge k…