MUSABBABI CHAPTER 5 BY HAJ HABIBA

shi yake bukatar nasiha tare da dora shi a hanyar Allah. Kuma dole na so masa abinda na ke so ma kaina, domin imanin dayanmu baya cika, har sai mun soma Dan-uwanmu abinda muke so: ma kanmu. Saboda haka ki cire damuwa a zuciyarki, zan goya miki baya dari bisa dari har sai kin cimma burinki Murmushi ya subuce a fuskar Afrah, ta kura ma. Ya Sayyadi ido, hakika kallo daya za ka yi masa, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, âmma baya son bayyanawa. Hakika Ya Sayyadinta ya cika gwarzon maza, ya cika jarumi. “Hakika Ya Sayyadi ban taba ganin namiji me zuciyar imani da tausayi da kuma fahimta irinka ba, tabbas ina taya kaina jaje da bakin-cikin rashin masoyi irin ka, sai dai tarihin rayuwata na san ba zai taba kammala ba, ba tare da ka shigo ciki ba, ba zan taba mantawa da kai ba har na koma ga mahaliccina.” Ya injina kai yana Kokarin maida hawayen da ya taru masa a ido, ya ce “Babu komai Fateema, haka Allah ya tsara mana, ba kuma za mu taba yin fushi da yinsa ba, domin ya yi mana na’ imomi da …