MUSABBABI CHAPTER 4 BY HAJ HABIBA

Musaddik a matsayin mijin aurenta ba, shin me kaddara ta tanadar mata? Zama da mutum irin Musaddik wanda bai ma san inda rayuwarsa tasa gaba ba. Wanda bai san yadda zai tarbiyantar da ita, ko kadan ba irin Musaddik bane mijin da take kwadayin zama a Karkashinsa. Ya Sayyadi Habib shi ne wanda ta horar ma da zuciyarta kaunarsa, ta kuma kwadaita ma kanta auransa. Domin tana da tabbacin shine wanda zai yi mata jagora har gidan aljanna, sai dai kash! Ba ta so yadda labarin ya tsaya ba, ba ta so karshen labarin ya zama haka ba. Domin kuwa ko ta ki ko ta so soyayyarta da Ya Sayyadi ta zama tarihi daga lokacin da mahaifinta ya umarceta da auran Musaddik, tabbas! Za ta yi ma mahaifinta biyayya, koda hakan. zai zama sanadiyyar fadawarta mummunar rayuwa, domin duk duniya ba ta da kamar mahaifinta. Ba ta tunanin akwai abinda zai bukata ta yi masa, matukar tana da halin yi masa ta kasa yi, don haka za ta iya sadaukar da komai nata, domin samun farin-cikin mahaifinta, tunda Allah ya taimaketa ta samu ta …