CANJIN RAYUWA CHAPTER 5 BY HALIMA A K/MASH
yaron nan, domin mahaifiyarki ma ta zo min da zancen. Sannan ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki, domin ta lura ba ki cika son ibada ba, kuma ni ma tunda ba ki son yin sallah ba zan amince ba, domin abin ya yi yawa kenan Mimi. Don gaskiya mahaifiyarki tana da hujiar cewa in bar ki, Mimi ta rude, Dad don Allah kar ka bar ni, ka san fa ba sa so na. Ya ce, suna sonki na sani Mimi, in kin dan zauna za ku shaku ni ma ba a son raina zan bar ki ba. Ta soma kuka wiwi tana fadin Dady kawai ka ce ka daina so na, Please Dady kar ka barni ba zan zauna ba. Ya dafa ta, shikenan na ji ki yi shiru zan tafi da ke, amma kin san dole sai ta bata rai ko? Ta ce, Dad in mun tafi za ta huce, ya ce, a’a dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta. Ta yi shiru tana tunani, ya katse ta da cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu, don ni ma ba zan so a ce ‘ya ta mai kyau kamarki, amma ba ta san komai a cikin addininta ba. Take wata dabara ta fado wa Mimi ta ce, Dady me zai sa ba za ka …