CANJIN RAYUWA CHAPTER 4 BY HALIMA A K/MASH

turare ya ce, ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko ya ya ne dai daga can zan wuce Malumfashi. In duba su Binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba. Sannan inda lokaci zan shiga Masari can ma na jima ban je ba. Kin ga sai na kwana kenan, gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo. Hajiya, Sauda ta ce, Allah ya tsare sai ka dawo din, amma batun tafiya da Mimi ne nake tunani a kai. Ya kalle ta, kamar ya ya? Ta ce, sai ka dawo dai Allah ya tsare, ya dan tabe baki amin. Suna fitowa Falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi, ya amsa da daidai, sannan ya kalli Usaina, Mimi fa? Ta ce, tana kwance Dady,: ya: ce, shikenan za mu yi waya. Hajiya ta raka shi har mota, wannan ba sabon abu bane, haka ta saba tun suna da kuruciya. Falon ya kacame, yaran suna ta karin kumallo, sai hayaniyarsu da Karar kofuna. Mimi ta fito sanye cikin riga da wando masu dan kauri na barci. Sauri take yi, tare da fatan Allah Ya sa…