MAI TAFIYA CHAPTER 6

MAI TAFIYA CHAPTER 6
MAI TAFIYA CHAPTER 6 Www.bankinhausanovels.com.ng  Ranar wanka ba a boye cibi Kano, Nigeria Hindatu ce ke zaune a gaban mudubi tana kwalliya, tayi da wani maneminta zasu hadu karfe hudu na yamma daidai. A wayarta ta saka wata wakar sa’adu bori da take so tana bi da baki6 Lale hadiza lale lale hadiza yar malummai ka ga hadiza ta birgeni Ina cikin yawona ka ga hadiza ta birgeni Yara suna kiranta amare manya suna kiranta amare Zama da kishiya tilas ne ba don uwargida na so ba! Kai! Duniya tana kaunar Saadou Bori Allah dai ya jikan sa. Anya idan ta tashi aure da Alhaji Awaisu ba za ta kira yaron saadou bori ya wake su ba? Irin arzikin Alhaji Awaisu ai sai da haka yanda za ta fantama a cikin kawayenta.7 Ita yanzu duk yanda za a yi bata iya auren wanda bai tara dukiya ba, wanda ba zai gina mata tamfatsetsen gida ba da motoci na alfarma suna harabar pakin. Ya bata ko da miliyan goma ne ta hado lefe na kece raini, Allah ta tuba ina tsiya tsiya ina miliyan goma a wajen Alhaji Awaisu! Ai wuce nan.8 A ciki…