ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  maka duk tayoyin ka na yi maka asarar fitar na bi ta wancan get din tunda estate din ba get daya ne da shi ba. Wani irin kallo ta yi masa ta datse lebenta tsabar takaicin abin da ya fada mata tsayawa ta yi tunanin mai za ta fada masa ta yi, domin ya gama kai ta bango take ta tuno abin da zai kona masa rai lokaci daya, domin haka Haana take da wuya kayi nasara a kanta in dai magana ce.  Www.bankinhausanovels.com.ng Ta ce, “Ayya malam maza wuce abin ka nima ga can Ya Abba ya dawo zan je gurinsa ya gaya min kalaman soyayyarsa masu dadi, don ka je kai ma an fada maka ai ba haushi ko ganin laifi zan yi ba maza tafi kada kuda ya riga ka. Tana gama fadin haka ta juya abin ta kafin ta shiga motar, sai da ta juyo ta ga yadda yanayin fuskarsa ya canza nan dadi ya kama ta, domin kasa cewa da ita komai ya yi ta shiga godewa Allah a zuciyarta ta ce. Yawwa na gode Allah tunda na gano abin da zan dinga yi na konawa Man din nan ra…