ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI'A DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya dama tuni na yi tunanin samun wannan tarbar farin Cikin daga gare ki.” Www.bankinhausanovels.com.ng Nan suka juya hirar ta su zuwa wani zancen daban. Sun jima suna hira daga nan suka yi sallama. Ko ba komai Haana ta dan samu nutsuwar zuciyarta kadan da haka har ta samu barci ya yi awan gaba da ita Alhaji Jafar ne ya yi sallama ya shigo dakin Haj. ASIya wato Mommy inda ya tarar da ita tana shirin barci. Bayan ta amsa sallamar cikin murmushi ta ce, “Daddy ai na yi tunanin a can ma za ka kwana dubi agogo ka gani, gaskiya yau hira ta yi dadi wato hirar yaushe gamo aka yi kenan. Shi ma murmushin ya yi ya ce, Wane ni na kwana a can ina tare da Su amma zuciyata tana gurin ki. Ya fada yana kokarin zama a kan gadon. Kenan na canja tunanina. Da hakan kuwa ya fi yi miki sauki. Gaba dayansu suka saka tariya, tun lokacin da komai ya daidaitu Alh. Jafar bai da wani buri illa ya ga ya farantawa mai dakinsa domin idan ba ita ba babu…