ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Damuwa ce ta Cika masa zuciyarsa fal. Tabbas ya na Cikin tsaka mai wuya, ta ya zai iya janye wannan al amarin, ya ma zal 1ya cire Haana daga ransa, ga tausayin Rauda ma da yake kwana ya Tashi da shi. Dama ya zo ne ya fadawa iyayensa cewa duk su biyun zai hada ya aura. Ya fara kawo maganar Haana ne don ya ji yadda za su karbi abin, sai kuma ga shi natan ma ba su karba ba, balle kuma a je ga batun na Rauda. Ya ma rasa yadda zai yi da damuwarsa. Sai kawai ya dauki wayarsa ya kira Rauda, Wajen sau uku ya na kiran wayar amma ba’a daga ba, sai a na hudun daf da za ta tsinke ta daga. Ya Abba ne zaune gaban Granny don amsa kiran da ta yi masa, su biyu ne kawai a dakin daga shi sai ita. Granny ta dube shi ta ce. Mustapha karami dama na kira ka ne don mu YI wata magana, to amma ina son na ji ra ayinka akan haka. To Granny ai ke nake saurare. Ya fada ya na mai kara sanya nutsuwa hade da murmushi a fuskarsa. Mustapha shin ka na da wata …