ZUMA CHAPTER 8 BY SHATUUU ZUMA CHAPTER 8 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng Duk bansan abinda ke faruwa ba saboda na riga na kashe wayata baki daya tun friday da muka dawo daga asibiti da daddare, tsoro na daya shi ne kiran Aliyu ya shigo min wayata bansan me zance masa ba, bansan a wanne hali yake ciki ba bansan ba ko Daddy ya bashi wannan mummunan labarin. Haka na cigaba da zama da waya a kashe babu abinda nake se dai idan maganar ta dawo min na shiga toilet na saki ruwa nayi kuka na wanko fuskata na fito. Wajen yamma Aminatu ta gama shiri zata koma hadejia inda anan take nursing training dinta cikin sabuwar school of nursing da aka bude, dakina ta shigo hannunta rike da plate din abinci ta zauna gefe na tareda aje min tace+ “Yaya Nanah an samu matsala ne da Aliyu? Naga yau kika ce zasu zo amma shiru” Furta sunan Aliyu da tayi se naji idanuna sun ciko da kwalla, nayi saurin kawar da kaina ina bude baki na dan iska tasa hawayen ya koma, saboda bana son wani yaga ina kuka akan maganar har suga laifin Daddy k…