MAI TAFIYA CHAPTER 2 MAI TAFIYA CHAPTER 2 Www.bankinhausanovels.com.ng Ina mafita? A lokacin da babu mafita!4 Kano, Nigeria Washegarin rasuwar Muhammadu Hindatu ta tattara na ta ya na ta ta koma gidansu, ‘Yanuwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ma ta gaisuwa. Ta kudurce a ranta cewar idan fa bata nemi mafita ba to da daya da daya sai ta nemi ‘ya’yanta ta hange su a hannun mutuwa.2 To zaman gidan ma jiya i yau. Makauniyar uwarta na nan yadda take da kannenta gudu uku mata, sai ita cikon ta hudu da ‘ya’yanta biyu cikon biyar da shida wanda suka samu mazauni a dan tsukakken dakin mutum biyu. Maza yanzu ba sa son zawarcin mace mai ‘ya’ya in dai ba dukiya aka bar musu ba, don haka daga mutum ya zo daya, biyu sai ta ji dif. Wani abu da ya fi daure ma ta kai da kuma ba ta haushi bai wuce gani ganin da kannen nata ke ma ta ba suna ma kallon wacce ta zo ta takura musu. Wani mugun raini ne ya shiga tsakaninsu kamar wacce kan ta aka fara zawarci. ‘Ya’yanta sai suka zama ganguna sai dai ka ji tim! An kai musu duka ba gaira…