ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI'A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE
ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE  Www.bankinhausanovels.com.ng  da kuma jimamin rashin da muka yi na  Www.bankinhausanovels.com.ng Alh. Kabiru, babu wanda bai tausaya min ba, amma ni samun Maryam shi ne ya Kara dauke min damuwar, tun daga lokacin na fara fitar da rai na akan aure. Mustapha na da shekara hudu Maryam na – da shekara daya a duniya Innawuro ta samu ciki wanda tun daga samun sa take cikin matsala, ga kuma laulayi na Kin Karawa, domin kullum tana cikin larura, dole yasa aka cire Maryam daga shan Mama ganin itama ta fara yin rashin lafiya. ‘Kullum muka zauna ni da ita ta dinga yi min magana akan cikin nan, da kuma cewa. “Rehana anya kuwa wannan cikin zai barni na rayu da ku? Domin tunda nake ban taba daukar ciki mai wuya haka ba. Idan har na mutu ki daure ki kular min da Maryam da Mustapha, ki riKe su tamkar yadda za ki riKe yaran da kika haifa a cikin ki, bana so ki bar su hannun su Saude, domin ba za su riKe su tsakani da Allah ba. Domin na fuskanci tsanar…