ZANEN DUTSE CHAPTER 5 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 5 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 5 BY AISHA-SHAFIEE                   Www.bankinhausanovels.com.ng  ASALIN LABARIN.+ Kowanne labarin duniya yana da tushe. Kowanne yana da mafari. Me kenan? Wani abu da ya faru har ya zama sanadin wanzuwar jirkitattun al’amura. Zahra Tabi’u. (Farin Wata)2 YOLA, Jimeta. Shekarar 1987. Motar ƙirar Peugeot ce 305, mai kalar ruwan ƙasa sabuwa dal sai ƙyalli take cikin hasken safiyar da rana bata gama buɗewa sosai ba, fitilar danjojinta a kunne suke yayin da ƙarar horn ke fita daga cikinta alamun matukin na jiran a bude masa tangamemen gate din ginin dake gabansa wanda a samansa aka zana harafan sunan ‘Sectariate’ (Sakateriyar ƙaramar hukumar ta Jimeta) Minti daya, biyu, sai gate din ya bude cikin sauri motar ta kutsa ta karasa ciki. “Allah ya huci ranka yallabai, Allah ya ƙara girma, ayi mana afuwa wallahi muna can ciki ne ana tattauna wani al’amarin da ya faru.” Dattijon da ya bude kofar ta fada cikin durkusawa yayin da hannunsa ke dunkule a iska yana kallon matuƙin cikin motar …