ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE
ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE                 Www.bankinhausanovels.com.ng  Tafiyar motar a wane irin yanayi ne da Jidda ba zata iya fassara shi ba, ta kasa gane gudu suke ko kuma akasin sa, tunda ga abubuwa nan suna wucewa cikin matsanancin gudu amma kuma a cikin motar kamar a hankali suke tafiya saboda yadda komai yake dum-dum.+ Kuma har a lokacin tana takure a kan kujerar ta kasa ko motsi sannan in banda sanyin A.c da k’amshin turaren nan nasa ba abinda ke shiga kwakwalwarta. Ga duhun magriba ya fara lullub’e gari a lokacin, ga k’afarta da ba takalmi duk ta tako shinkafar da aka zubar a k’asa sanda ya jawo hannunta zuwa waje, don haka tana son ta mik’a hannu ta karkad’e su amma tsabar tsoron yadda ingarman jikinsa ke zaune a gefenta yasa ko kwakwaran motsi ta kasa. Fuskarta na juye kawai tana kallon window, kuma da alama shima bai ko kalli inda take ba tuk’insa kawai yake. Bata san inda suke bi ba amma hankalinta ya nuna mata cewa hanyar barin gari ne tunda ta fara ganin k’aran…