YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 4 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng “Good morning everyone!. I’m L.G(Lieutenant General) Aliyu Iko”. *_Raf! Raf!! Raf!!!_* Suka shiga tab’a mishi cike da girmamawa, hakan ya bani tabbacin shi d’in babba ne sama da su. D’an murmushi yayi sannan ya cigaba da fad’in, “Ah! da farko dai ina yimuku barka da isowa wannan muhimmin meeting, ina fatan dukkanku kun iso lafiya?”. A tare suka girgiza mishi kai alamar eh. Fita yayi daga masaukinshi, ya nufi wurin wata k’atuwar Computer dake ajiye cikin hall d’in daf da inda suke tana fuskantar su, hakan yasa duk suka maida hankalinsu a kan Computer da zanen wani k’aton map ya bayyana a cikinta. “Kamar yanda kuka sani wannan TASWIRAR k’asar SARBIK ce. A k’alla munada jahohi 40 a cikin wannan k’asa mai tarin albarka. Kowa ya san shekarun da suka gabata k’asar SARBIK ta kasance k’asa mai dawwamammen zaman lafiya, cigaba tare da wadatar arziki da albarkatun k’asa. Kafin yanzu ta zama hedikwatar …