YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 3 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 3 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng UK ?? Flight d’insu na sauka airport ta tari cab tare da fad’a mishi sunan Hotel d’in da zai kaita, don UK ba bak’uwarta ba ce. Suna isowa Hotel d’in ta sallameshi sannan ta wuce reception ta karb’i key ta nufi room d’in da zata sauka. Wanka tayi domin jin dad’in jikinta, sannan ta gabatar da sallar azahar. daga nan bacci ya kwasheta, bata falka ba sai wuraren 3:30pm. Sai a lokacin tayi order abinci ta samu ta ci. Ga baki d’ayan yinin ranar babu aikin da tayi sai hutu kawai don tana tattare da gajiya. *Washe gari* Around 12:35pm ta gama shirinta, pink t-shirt ce jikinta da black jeans sai wani black veil data d’aura a kanta amma hakan bai hana saukowar bak’ar sumarta akan shoulder d’inta ba, sosai tayi kyau kamar wata baturiya. Cikin sauri ta d’auki wayarta ta fice daga room d’in. Cab ta tara tare da sanar da shi inda zai sauketa wato address d’in Abreen. daga d’an nesa tace ya sauketa, ka…