YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 2 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 2 BY ANUP JANYAU (_SPY_?) Www.bankinhausanovels.com.ng “What!!!?”. Wani farin mutum wanda kallo d’aya zaka yimishi ka gano yana cikin lokaci, ya fad’a tare da saurin mik’ewa daga meeting d’in da suke yi. Da kallon mamaki mutanen dake zazzaune suka bishi. Shi kuwa bai tsaya kula kallon da suke yimasa ba ya bar wurin hankalinsa a d’an tashe, wurin da babu mutane ya isa, murya k’asa-k’asa yake fad’in, “Hello Kana jina?”. “Ina jinka Mai gida”. “Ina so ka sanya ido sosai a kansu, ka tura amintattun mutanenka a sirrin ce su dubo mai suke yi a can bayan garin, wallahi hankalina a tashe yake don kuwa jikina yana bani akwai wata a k’asa, anya bazan sa a kashe su kawai mu huta ba?”. “A’ah Mai gida, kashe su shine babban kuskuren da zamu aikata domin kuwa bamu san ko su d’in su waye ba, kuma bamu san da wane irin shiri suke ba, bari dai in tura a dubo su d’in kamar yanda ka buk’ata”. “Okay!, yanzu muna meeting ne zan tab’oka daga baya”. Yana gama fad’in haka ya k…