WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU                    Www.bankinhausanovels.com.ng  Sunkuye take tana hura wuta da bakinta, gaba ɗaya tokar karan ta yayyaɓe mata fuska. Nishi taketa yi ga kuma zufa. Kai ta ɗaga sama tana hangen hadarin daya gangamo. Gabanta ya faɗi ras! Wasu ƙwala suka kwaranyo mata wai yau ita ce take hura wuta da karare lallai duniya labari.    Ta tuna irin rayuwar data gabatar a baya, zuciyarta ta cika da ƙuncin halin da take ciki. Sai dai tasan ko giyar wake tasha Tukur ba zai saketa ba shiyasa ma ta haƙura ta miƙawa ubangiji lamuranta. Tana nan tsugune ta rasa madafa, har haɗarin ya gama kankama. A gefe kuwa facalolinta sai dariya suke tiƙa mata saboda murna. Cikin ikon Allah sai ga tasowar iska, wannan iskar ita ta taimaka mata ta hura wutar nan da nan ta tuƙa tuwo ta kwashe.   Sai bayan isha’i ta gama komai kamar an bada umarni kuwa sai ga kecewar ruwa kamar da bakin ƙwarya.   A gajiye liƙis ta samu guri ta zauna, idanunta har wani yaji-yaji suke yi mata sa…