WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sunkuye take tana hura wuta da bakinta, gaba Ιaya tokar karan ta yayyaΙe mata fuska. Nishi taketa yi ga kuma zufa. Kai ta Ιaga sama tana hangen hadarin daya gangamo. Gabanta ya faΙi ras! Wasu Ζwala suka kwaranyo mata wai yau ita ce take hura wuta da karare lallai duniya labari.
Ta tuna irin rayuwar data gabatar a baya, zuciyarta ta cika da Ζuncin halin da take ciki. Sai dai tasan ko giyar wake tasha Tukur ba zai saketa ba shiyasa ma ta haΖura ta miΖawa ubangiji lamuranta. Tana nan tsugune ta rasa madafa, har haΙarin ya gama kankama. A gefe kuwa facalolinta sai dariya suke tiΖa mata saboda murna. Cikin ikon Allah sai ga tasowar iska, wannan iskar ita ta taimaka mata ta hura wutar nan da nan ta tuΖa tuwo ta kwashe.
Sai bayan isha’i ta gama komai kamar an bada umarni kuwa sai ga kecewar ruwa kamar da bakin Ζwarya.
A gajiye liΖis ta samu guri ta zauna, idanunta har wani yaji-yaji suke yi mata saboda tun asuba bata runtsa ba. Tana jin shigowar Tukur Ιakin ya jiΖe sharkaf nan tsakiyar Ιakin ya cire kayansa dagashi sai gajeran wando ya buΙe kwaba ya Ιauki wasu ya saka ya haye gado ya Ζudundune. Takaicin bar mata kaya da ya yi anan ya sake kasheta. Kamar ba zata tankaba ta daure ta haΙiye abinda ya tsaya mata a maΖoshi ta furta,
“yanzu saboda Allah ka cire kaya ka bar su a nan kuma jiΖaΖΖu?”
“Ke Labiba kin fa cika Ζorafi wallahi, ke komai wai abin magana ne a wajenki. Idan ma barin kayan na yi mene ne amfaninki, aurenki fa nake yi dole ki yi min bauta kamar yadda KOWACE MACE take bautar aure a gidan mijinta. Mtssss! Ni an haΙani da aiki wallahi, mace sai mitar jarraba ke bakisan mace me mita aurenta saurin mutuwa yake yi ba?”
Wani Ζududdune ya tahomata tun daga tsakiyar ka be sauka ko ina ba sai tsakiyar cikinta, tana jin lokacin da Ιan cikinta ya yi wata irin motsawa. Ta cije baki tana tuna daidai da rana guda bata taΙa zuwa awo ba bare ta san ya lafiyar abinda yake cikinta.
Ζiri-Ζiri mahaifiyar Tukur ta haramta hakan. Ta tuna cikin Ummi yadda Yusuf yake jelangiyar aro machine yana kaita awo ya Ιaukota. Hawaye ta share, zuciyarta na faΙa mata ba zata bari Tukur y shata bulus ba.
“Tunda kasan da hakan me ya hana ka yadda Ζwalon mangwaro ka huta da Ζuda?”
“An zo wajen! Ahaf to anΖi a sake kin” Ya furta yana zabura kamar wanda aka yi wa allaura “kin nufin in sakeki Labiba? Haaaaaa” ya yi dariya me sauti duk da ruwan da yake zuba,
“ko karan hauka ya cijeni wallahi ban shika miki ko igiya guda. Waga batun ki sakayashi cikin zuciyarki zama dani haihata Labi baby”
Yadda ya furta baby Ιin ya fi komai yi mata ciwo dan haka ta ja bakinta ta yi shiru kawai.
Suna nan zaune Ιakinta ya soma zuba yoyon ruwa ta tsakiya. Ido ta Ιaga kawai sai ta soma hawaye. Zuciyarta ta yi wata irin matsewa Ζwarai ta sani girbin aikinta da ta shuka take yi amma batu na gaskiy ta gaji da yanayin tana buΖatar sassauci.
Wata zuciyar ta tanasar da ita cewar addu’ar bayi na saurin amsuwa yayinda ruwan sama yake zuba. Kamar wadda aka yi wa allura haka ta ji wani kuzari ya shigeta ta Ιaga dukkan hannayenta sama. Kuka take me sauti, me fita da yanayin da ya ke nuna neman agaji. LaΙΙanta suka motsa da wani irin karsashi data manta rabon da ta ji makamancinsa.
“Allah na tuba, na kaskantar da kaina a gareka ya ubangiji ka dubeni badan ni ba badan halina ba. Allah ni baiwarka ce me saΙo a gareka, ina ta wasulu da sunayenka tsarkaka ina tawasuli da alΖur’aninka me girma Allah kadda ka dubi tarin zunubaina, Allah ka dubeni da rahamarka ka kawomun sassauci cikin rayuwar danake fuskanta”
Sautin kalamanta har kunnuwan Tukur da yake kwance, wani irin sanyi jikinsa ya yi ga wani tausayinta daya mammayeshi. Tsam ya tashi ya kwashe kayan da ya zubar mata a tsakar Ιaki tare da Ιauko roba ya tara a wajen da yake zubar ruwan. Ζarasawa ya yi kusa da ita, kallonta yake ya kasa ce mata komai, ita ma kallonsa take tana jin wani wannan nauyin na Ζirjinta na raguwa a hankali.
***
Washegari kamar almara ta tashi da baΖuncin Amne, karon farko tun watanni goma na aurenta. Lallai yau tana cike da murna, da fara’a da komai ta tareta abin mamaki hadda Umminta. Duk yanayin nauyin jiki da take ji be hanata zaryar sama musu abinda zasu sa a bakinsu ba. Fita ta yi ta samo musu a wara a bakin hanya, ta dawo ta ajiye musu tare da ruwa.
Sai zuruftu take yi, Amne kuwa sai binta take da idanu cike da tausayi.Lokaci-lokaci takan faki idonta ta share hawaye Ζwarai tana tausayin rayuwar da Ιiyartata ta riski kanta amma tasan ita ce sillar rushewar farin cikinta.
Anata Ιangaren Labiba so take ta nemi yafiyar Ummi amma nauyi ya sa ta kasa koda tambayarta ina Ιan uwanta tun bayan gaisawa da suka yi babu abinda ya Ζara haΙasu.
Yanayin yadda take bin yarainyar da ido ya karyarwa da Amne guiwa. Tabbas sai yanzu take Ζara hango kuskuren da suka tafka na wargaza rayuwar uwa da Ζ΄aΖ΄anta.
Haka Labiba ta daure ta dinga jan Ummi da hira tana tambayarta makaranta da Ζananta. Uwa uwa ce koda kuwa ta buzuzu ce sai gashi Ummi ta ware harta sake da ita ta shiga bata labarin yadda Shukura take kyautata musu. Ba Ζaramin daΙi ta ji ba, duk da ana bata labarin hallacin matar amma jin daga bakin Ummi ya bata tabbaci domin tasan zaman uwar wani da wani sai Allah.
Da zasu tafi Ζuli-Ζuli me yawa ta siya wajen surukarta ta ba Ummi da daddawa ta ce ta kaiwa Auntynsu. Amne ma ta bat hada kukar kaΙi. Haka suka rabu cikin kewar juna sossai ta yi mata nasiha tare da alΖawarin aiko mata da jari ta kafa sana a domin tsayuwa da Ζafafunta. Aikuwa kwananta uku da tafiya ta yo mata aike. Cikin ikon Allah ta soma sarin buhun gyaΙa Ιararriya a Ιaya daga cikin shagunan da Yusuf ya buΙe, wani abin armashi shi yasa yaransa suka kawo mata a mota bayan ya Ζara Ζarfin jarin nata da cewar ga nasa taimakon nan. Domin duk halin da take ciki tsegumi na zuwa kunnansa dan dai ba me tankawar bane. Ranar yini ta yi tana jinjina karamcin Yusuf da kuma kyakyawar zuciyarsa.
Cikin ikon Allah ta soma sana’arta cikin nasara, hata Baba Harira bata yi mata buΖulu ba a wajenta take siyen gyaΙa da ma sauran matan Ζauyen masu sana’ar Ζuli. Sai ga shi har wani kumari ta yi saboda yadda kuΙi suke shigo mata. Shi kansa Tukur ya rage kaso goma na hallayarsa domin dai yanzu sana’ar wankin hula da wanki da guga yake a shagon daya buΙe a Ζofar gidansu. Kasancewar ya yi zaman maraya abin na shi a Ζawace yake yinsa sossai yake samun ciniki.
***
SanΙa take da dukkan wani taku data san ta mallaka domin gujewa farkawarsa. Tun lokacin da ya shigo da baΖar ledar ta Ζyala ido ta ganta hankalinta ya karkata kan yadda zata Ιauket.
Ganin ya samu bacci yasa ta shiga Ιakin da sanΙa, da dukkan zuciyarta take jin yau lokacin mutuwar aurenta ya yi matuΖar ta sami nasarar Ιaukar kuΙin.
Kabir da baccin takaicin Ramla ya kwashe shi be san wainar da ake toyawa ba. Tun lokacin da ya shigo yunwa na ΖwaΖularsa ya tambayeta abinci ta murguΙa baki tare da cewar bata yi ba ya shige Ιakinsa ya barta a nan. Kwanciya ya yi yan tunanin Zahidaht idanunsa har haska masa imagine Ιin rayuwarsu ta baya yake yi. A haka bacci ya kwasheshi cike da mafarkanta marasa kangado wanda akasari duk acikin korayen ciyayi yake ganinta.
Juyi ya yi sai ya buΙe ido kaΙan, hango Ramlatu ya yi tana laΙe-laΙe ta nufi ledar da mahaifinsa ya aikeshi ya kai masa saΖo banki. Shi kwata-kwatama ya manta da batun. Be motsa ba, so yake ya gasgata zatonsa. Ya sha ajiye kuΙi da shadodin da be Ιinka ba ya wayi gari babu, idan ya yi magana ta hayayyaΖo masa da masifa kan cewar ajiya ya bata. Dan haka sai ya Ζara lamΙo yana jin zuciyarsa na dokawa.
Tabbas kuwa sunkuyawa ta yi ta kwance ta Ιauki bandir na Ζ΄an dubu-dubu guda biyar. Ta maida ledar kamar bata taΙa ba. Mamaki ya kashe shi yana daga kwance.
Kamar ya barta ta tafi haka ya ji a ransa, amma sanin wace ce ita ya sa ya yunΖura da wani irin karsashi ya sha gabanta. Ta razana matuΖa, baikinta ya soma karkarwa ya nunata da yatsa yana hucci.
“Dama ke ce ki ke min sata Ramlatu?”
“Babe ka tsaya ka saurareni…”
Wanke mata fuska ya yi da mari, karon farko da ya ji baya shakkar dukkan mace tun bayan dukan Zahidaht, yau kam ya karya alΖawarin da y Ιaukarwa ransa. Sai dai ko kaffarar ce ya yi ta dag baya. Sossai ya zage Ζwanji ya zanneta. Da bakinta ta dinga faΙa masa irin abubuwan data Ιaukar masa da kuma dalilinta na auransa harma da cikkunansa data zubar. Ζwalla kawai ya ke sharewa yana kukan zuci.
“Na tuba Allah Zahi ki yafemun wallahi na horu”
Shi ne abinda bakinsa yake furtawa yana kallo ta kwashi kayant ta fice. Ramlatu ta tafi tana kuka zuciyarta cike da nadamar sakin da ya yi mata. Rayuwar da zata yi a gidansu kaΙai take hangowa. Na Ιaya su goma ne biyu ne kaΙi Ζ΄an mata dukkansu zawarawa ne. Kowa ce gashin kanta take ci. Mahaifinsu ba wani damuwa ya yi da lamarinsu ba saboda matarsa ta Ιauke hankalinsa. Lallai sai yanzu take hango babban kuskuren data tafka na suΙucewa auren Kabir.
Kabir ya jima anan zaune, gaba Ιaya jikinsa ya gama yin sanyi. Ya sani ya zallunci Zahidaht amma yana jin ankai gejin da bashi da Ζwanjin Ιaukar waΙanan zunuban. Shi kam ya haΖura da kowa ce mace a yanzu zai maida sauran rayuwarsa gaba Ιaya wajen bautar ubangiji ko ya samu sassauci. Koda batun sakin ya shiga gida ba Ζarmin faΙa ya sha ba bai Ιoye musu komai ba ya bayyana musu dalilonsa na sakinta. Mahaifiyarsa ta tausaya masa tare da yi masa kyakyawan fata.
***
Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji Labiba ta sauka lafiya. Ta haifi yaranta guda biyu mace da namiji. Tukur baki har kunne hakama mahiafiyarsa. Ranar suna Tukur ya yi mata bazata. Sunan Yusuf ya saka mata. Ita kuma ya sakawa macen sunan mahaifiyarsa amma Labiba ta sakaya mata da faΙin Ahyana.
Ba Ζaramin martaba ya Ζara a idanunta ba, Ζaunar yaron take da dukkan zuciyarta. Sunan mahiafinta. Sunan mijinta abin sonta data rasa sanadin son ranta. Kuma sunan Ιanta na biyu. Tabbas Tukur ya kafa babban tarihi a rayuwarta. Dan haka ta Ζara kwantar da hankalinta biyayya take masa kamar KOWA CE MACE.
Bayan suna da kwana sittin ta shirya ya rakata suka je ganin gida da zaga dangi. Ta yi kyau abunta kamar ba ita ba saboda ta sakama ranta nutsuwa. Su kansu ahalinta sunyi mamakinta. Har gida ta je ta sake neman gafarar Yusuf tare da yi wa Shukura godiyar kulawa da yaranta. Anan ta ga Ιiyar Shukuran da suka yi wa Zahidaht takwara. Yarinyar sak mahaifinta. Ga ta kyakkyawa ga shiga rai. Da zasu tafi Yusuf ya tambayi Tukur sana’arsa ganin ya kama kame-kame ya sa Shukura ta Ιauko masa dubu Ιari biyu da hamsin ya ba shi ya ce ya ja jari. Sai ga Labiba na kuka tana godiya. Amne ma har gida ta zo ta yi masa godiya tare da neman yafiyarsa.
Yusuf ya zamo tauraron zuri’arsu domin dai gaba da baya shi ya gaji mahaifin Labiba. Duk wata hidima da yake yi ya Ιora a kanta kuma da jiki da zuciyarsa yake yi. Ya yi duk iya ΖoΖarinsa ya fahimtar da ahalinsa illar auren haΙin da suke yi ba tare da yarjewar yaransu ba. Tabbas sun gamsu tare da kashe wannan Ζuduri a ahalinsu amma ba gaba Ιaya ba idan kuna son juna sukan haΙaku aure haka kuma idan ka kawo ta waje suna maraba da ita domin Shukura ta zamo musu aya.
Komawarsu Labiba ba Ζaramin martaba ta Ζara samu wajen surukarta ba. Hatta facalolinta shakkarta suka soma yi. Kowa na nan nan da ita. A hankali ta soma jan Ζ΄an matan Ζauyen tana wayar musu da hankali kan tsafta da kuma addinni. Nan da nan sunanta ya yi fice kowa ita. Tukur na Ιagawa da alfaharin aurenta.
Jarin da Yusuf ya bashi ya zamo masa tsani, noman albasa ya ke yi kuma Allah ya saka masa albarka sossai a harkar. Ya haΙa da noman rani sai ga Tukur na fita da kayan miya mota-mota zuwa jihar legas. Labiba ta yi amfani da damarta wajen Ζara wayar masa da kai. Da kyautatama Ζ΄an uwansa.
Allah me yadda ya so sai ga soyayya ta Ζulu tsakanin Maito autarsu Tukur da Yaya Khamis. Amne ta fi kowa murna domin yarinyar ta nutsu ta koma ta hanun daman Labiba. Matarsa kuwa kamar zata yi hauka sai dai kashedin mahafinsu ya ratsa kunanta na cewar matuΖar ta kashe auranta badai gidansa ba. Sai yanzu ta shiga nadamar abinda take yi wa Amne na rashin kyautawa. Hajiya Mawwaddah kanta ta shiga taitayinta.
A hankali farin ciki ya zagaye Ιaukacin ΖAN SAΖALO FAMILY. Suna kishi da alfahari da junansu. Suna kyautattawa junansu ga kuma taimakon na Ζasa dasu. Kawunansu a haΙe yake sossai abin sha’awa.
TAMMAT BI HAMDULLAH.
Post a Comment for "WATA MACE CHAPTER 7 KARSHE BY SANA S MATAZU"