WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU Www.bankinhausanovels.com.ng Ƙara ƙanƙame wayar ta yi a kunnanta, hawaye masu zafi na zubar mata. Maganganun Yaya Amina na shigarta, kowace gaɓa amsar saƙon take bawai dan ta gajiya da yawan amsar ba. Amma kullum ana kira mata lokaci-lokaci tana san sanin yaushe ne?+ “Zahidaht!” Ta faɗa da murya mai amo, “Nasan ke ake zallunta, amma hakan ba zai sa in ƙi baki haƙuri ba, wata rana sai labari. Duk wani yunƙuri da zaki yi yanzu ba shi da wani alfanu. Labiba ta riga da ta bugawa ahalinmu tambarin da ya zame mana baƙin fenti” Lumshe idanunta ta yi tana jin tsanar hallayar Labiba har cikin ranta. Ita kuwa ba dan an tabbatar mata da ta haɗa uba da ita ba a yau da ta yi shellar ta cire Labiba daga cikin ahalinta, ƙila koba komai ta samu sassaucin tata rayuwar auran, domin ta lura da ita Kabir ke amfani matsayin makamin kassara ƙumajinta. Ido ta sauke akansa lokacin da ya sawo kai ɗakin. Tabbas a buge yake kuma ba zata yi sakaci ya daketa a hof…