Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU


                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ƙara Ζ™anΖ™ame wayar ta yi a kunnanta, hawaye masu zafi na zubar mata. Maganganun Yaya Amina na shigarta, kowace gaΙ“a amsar saΖ™on take bawai dan ta gajiya da yawan amsar ba. Amma kullum ana kira mata lokaci-lokaci tana san sanin yaushe ne?+

“Zahidaht!”

Ta faΙ—a da murya mai amo,

“Nasan ke ake zallunta, amma hakan ba zai sa in Ζ™i baki haΖ™uri ba, wata rana sai labari. Duk wani yunΖ™uri da zaki yi yanzu ba shi da wani alfanu. Labiba ta riga da ta bugawa ahalinmu tambarin da ya zame mana baΖ™in fenti”

Lumshe idanunta ta yi tana jin tsanar hallayar Labiba har cikin ranta. Ita kuwa ba dan an tabbatar mata da ta haΙ—a uba da ita ba a yau da ta yi shellar ta cire Labiba daga cikin ahalinta, Ζ™ila koba komai ta samu sassaucin tata rayuwar auran, domin ta lura da ita Kabir ke amfani matsayin makamin kassara Ζ™umajinta. Ido ta sauke akansa lokacin da ya sawo kai Ι—akin. Tabbas a buge yake kuma ba zata yi sakaci ya daketa a hofi ba.

***

Kai kawo yake yi tsakanin Ζ™ofar shiga gidan da sitroom, gaba Ι—aya rigarsa ta jiΖ™e da gumi. Ba komai ke Ι—aga masa hankali ba face kukan karnukan da ke tashi. Kwanansa a waje ba matsala bane, sai dai be san illar da zasu yi masa ba. Ya sake duban agogonsa, a yanzu ya share awa uku kenan yana kiran wayarta tare da buga Ζ™ofar gidan. Babu Ι—aya da ta yi cikin abu biyu zuwa ukun da yake buΖ™ata. BuΙ—e Ζ™ofar ko kuma amsa wayarsa ya san halin da Ι—iyarsa ta ke ciki kawai ya wadace shi basai ya kwana gidan ba. Haka saΖ™wanin magiyar da ya ke jera mata babu wanda ta amsa masa. Kansa ya ci gaba da sarawa idanunsa suka kaΙ—a.

Zuciyarsa ce ta doka da wani irin karsashi lokacin da ya ajiye kallonsa a bangon gidan. Wata inuwa ya hanga doguwa tana nufoshi, idan ba gizo idanunsa suke yi masa ba hadda leda a hannun inuwar. Duk wata addu’a da ya taΙ“a sani a rayuwarsa ya shiga karantowa.

Jikinsa ban da karkarwa babu abinda ya ke yi, kamar almara ya ji sautuka biyu a daidai lokacin da ya fitar da tsamanin ya yi gamo,

“Baban Khalifa me kake yi anan, ga dare ga kuma karnunkan nan marasa kirki?”

Garam! Sautin zare sakatar gidan ya sauka a kunnansa. Ajiyar zuciya ya saki, yana ajiye kallonsa a saitin maΖ™ocinsa Malam Ali,

“Wallahi Ummi na siyowa magani, ina ga bacci ya Ι—auke Mamanta, amma ga shi nan ta buΙ—emin Ζ™ofar!”

“Asha”

Ya furta da fuskar alhini, domin su Ι—in sababbu ne wajen jin yana buga Ζ™ofa duk lokacin da zai dawo. Tun suna yi wa matarsa uzuri shi da maiΙ—akinsa har suka dangana abin da rashin tarbiya. Ba yau ne farau ba da zai share awoyi yana haΖ™Ζ™ilon buga Ζ™ofa, sai dai duk lokacin da tsautsayi zai haΙ—aku ka tambayeshi zai yi Ζ™oΖ™ari wajen kare iyalinsa ta hanyar uzururruka da yawa,

“ni ma dubiya ce na je, kuma na rasa abin hawa da wuri, ayi mata ya jiki don Allah. Sai da safe”

“Na gode Allah Ya kaimu”

Tana tsaye Ζ™yam tana sauke masa kwandon harara, ba tare da ya kalleta ba ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan. Ummi na kam kujera duk ta sauya yanayi. Ban da rawar sanyi babu abin da take yi. Da hanzari ya Ι—agota sai amai, tun tana yi da Ζ™arfinta har ta kwanta jikinsa. Tana tsaye tana kallonsu sai huci ta ke, bai bi ta kanta ba ya gyara yarinyar ya bata fresh milk da magungunanta. Ya kaita Ι—aki cikin Ζ™annanta tare da tofesu da addu’a ya fito. Bai nufi wajen abinci ba, yana da yaΖ™inin bazai samu ba, leda guda ya ajiye gabanta ya wuce Ι—akinsa da guda. Babu kunya ta Ι—auΖ™a ta wuce tana Ζ™unΖ™uni.

Sai da ya tabbatar da cikinsa ya Ι—auka sossai, sannan ya miΖ™e ya Ι—auro alwala ya hau abin sallah. Ya jima yana kaiwa ubangiji kukansa daga bisani ya yi shirin kwanciya. Juyi Ι—aya biyu ya kai hannu sashin da ya kamata ace anan take amma wayam! Babu alamunta, ya san za a rina abu ne da bai kamata ace ya yi mamaki ba, amma kuma ya zai iya da yanayinsa? Shi kam ko karan hauka ya ci je shi ba zai kai kansa Ι—akinta ba domin yasan Ζ™amshin mutuwa zai shaΖ™o. Runtse idanu ya yi yana jin wani irin abu a Ζ™asan zuciyarsa, a haka bacci ya yi awon gaba da shi…

***

“Yaya Amina ki zauna mana”

“In zauna Laby? Ai banga wajen zama anan ba, zuwa na yi in duba Ummi dan jiya tare aka kaisu kyamis da Nazir Ι—ina”

Ta faΙ—a tana ajiye mazaunanta kan kujerar da ta fi aminta da ita, sai dai zumbur ta miΖ™e sakammakon zama kan malellen fitsari har da Ι—igon kashi. Kallonta take da zallar mamakin hallayarta, ji take kamar ta shaΖ™eta ta mutu kowa ya huta da baΖ™in cikinta, dariya take tana Ζ™arawa cike da nishaΙ—i,

“Wallahi yaya Amina bata jin daΙ—i, amma da sauΖ™i”

“Ina Baban nata?”

Ta faΙ—a tana nufar hanyar Ι—akinsa, domin tasan anan ne zata sami sa ida. Sai dai bata Ζ™arasa ba saboda abin da kunnuwanta suka jiyo mata.

“Rabona da shi tun jiya dana horashi da tsayuwar awoyi a waje”

Mamaki ya daskarar da ita, bata bari ta cigaba ba ta tanka,

“Labiba wai yaushe zaki sauya ne?”

“Sai ranar da Ι—an uwanki ya sauya kashin awaki. Wato ni gandun laifi ko? Hmmm! Ai wallahi naso karnukan jiya sun manna masa hauka! Ban da wulaΖ™ancin ƊA NAMIJI awa nawa ina jiransa? Daga siyo maganin Ummi mutum ya shuri awa biyu da rabi”

“Amma dai Labiba baki da mutunci, kin tambayi dalilin jinkirinsa ne? Saboda kin samu mutum lako-lako sai ki dinga zuba wuΖ™alancinki son ranki. Kina sane fa da yadda Ζ΄an kwanakin nan ake fama da wannan zazzaΙ“in ma maja, to tabbas jiya agun magani ya ja lokaci saboda Baban Nazir ya je kai Nazir allura tare suka dawo shi ya sauke su a gida a mashin Ι—in sa”

Turo baki ta yi kamar shantu,

“ya dai sauke su ya tafi hidimarsa, ai wallahi tunda Baba Ɗangaladima ya bani goyon bayan rufe Ζ™ofa idan ya wuce Ζ™arfe tara, wallahi ya dinga kwasar takaici kenan! Ni da GIDANA ba zan Ι—auki tijarar ƊA NAMIJI ba. Naga alama idan na biyeku wahala zan sha,kawai ku komai sai ku ce mutum ya yi haΖ™uri wata rana kuwa sai dai a riski gawar mutum haΖ™urin ya kashe shi”

Galala take dubanta yaro da wayau, tabbas ta yi nisa bata jin kira sai dai addu’a. Duk yadda ake faΙ—ar hauka da gaΙ“oncin Labiba bata kawo ya kai haka ba, tabbas ta Ζ™ara sallama mata da hallayarta. Da gudu ta shigo Ι—akin tana shassheΖ™ar dariya, faΙ—awa ta yi kan kujerar da mahaifiyarta take kai,

“Ummi kin ga yaya Shukura zata dokeni ko!”

Ta furta tana Ι“uya a bayan mahaifiyar tasu. Gyara zaman gilashin idanunta ta yi tana murmushi,

“Wasila ba kwa jin magana ko? Wai Shukura bata girmeki ba, amma kin mayar da ita abokiyar wasanki. Haka zaku tafi Sakwaton ku je kunata saka Yaya magana ko?”

Da hanzari ta sauko Ζ™asa, ta tanΖ™washe Ζ™afafu tare da zuba dukΖ™an hannayenta a fuskarta. Ta marairaice fuska kamar wata me neman taimako, tare da kama kunnuwanta dukka biyun.

“Na tuba Ummi kimin rai, dan kina iya cewa ba za a je dani ba kadda a je a dinga sa miki wannan farin tsohon naki magana”

Duka ta kai mata, ta kauce tana dariya da buga Ζ™afa, daidai shigowar mahaifinsu ta tafi da gudu ta Ι—aneshi. Har lokacin dariyar take yi. Ummi kuwa ta shaΖ™a sai Ζ™wafa take yi,

“Ummin yara ke da mutuniyarki kuma yau?”

“Abbu wai dan na ce farin tsoro shi ne fa..”

“Wannan da ki ka maΖ™alΖ™ale ne farin tsoho rasai..”

Ummin ta tareta, ai kuwa daga Shukura har Abbun da Wasilar suka kwashe da dariya suna kyakkyatawa. Sai ta miΖ™e ta bar musu Ι—akin. Sai da suka tsagaita sannan mahaifin nasu ya dubi yaran. Ɗakin mahaifiyar tasu ya nuna musu da hannu, Shukura ra noΖ™e kai tana taΙ“e baki. Wasila kuwa sai ta mirgina kai kamar marayan Ι—ata tare da haΙ—e hannaye biyu. Sai dai yadda Abbun nasu ya yi yasa suka Ζ™ara kwashewa da dariya. Sai kace wani yaro. Daga Ζ™arshe dai suka Ι—unguma zuwa Ι—akin baki Ι—ayansu. A zaune suka sameta tana gyara takardu.

Sai suka tsaya turus kowa na shakkar matsawa kusa da ita, Wasila ce ta zaga ta baya ta Ι—ane wuyanta tare da sakalo hannayenta dukka biyun.  Ai kuwa da hanzari Shukura ta zauna a gabanta tare da rike hannayenta dukka biyun. Abbu kuwa sai ya tanΖ™washe Ζ™afa tare da kama kunnuwansa yana kashe mata ido. Gaba Ι—aya sun dabaibayeta ta kasa motsi. Kowane da irin motsin da yake wanda ya ke nuna mata nadamarsa. Dan haka sai ta sare,

“bazan haΖ™ura ba!”

Ta furta tana Ζ™unshe dariya. Wasila ta yi wani zilo,

“Ummi Abbu fa cewa ya yi in dai baki haΖ™ura ba…” saita Ι—ora hannunta kan bakinta tare da furta”au suΙ“ul da baka!”

Dungureta ta yi da hannu,

“Me ya ce?”

“Wai dama wannan Ζ™awar taki data liΖ™e masa ita ce..”

But! Ta bige bakinta, ai kuwa suka kwashe da dariya. Itama sai ta biyesu tana dariyar dan sai lokacin ta ankare da abin da ta yi, gaba Ι—aya suka haΙ—a baki suna faΙ—in,

“Ta haΖ™ura ta haΖ™ura”

Shukura ce ta kama hannun yar uwarta,

“Sililiya mu je mu Ζ™arasa haΙ—a kayan tafiyarmu!”

Fita suka yi suka bar iyayen nasu, ya muskuta tare da Ζ™ureta da kallo,

“Anya zani Sakwaton nan kuwa Hadiza? Kwanaki uku babu ke kusa da ni akwai gyara!”

Ya Ζ™arasa yana langaΙ“e kai kamar Ζ™aramin yaro. Hannu tasa ta kama kunnansa tare da murΙ—awa a wasan dare. Shi kuma hadda wata Ζ΄ar Ζ™ara irin da zafin nan,

“Love da zafi fa”

Zare idanu ta yi tana kallon Ζ™ofa wai kadda yara su ji. Dariya ya yi tare da shafa kuncinta,

“Oya kin iya cutata da kunya kin iya bigeman bakin Ι—iya dan tace zan auro wayis ko?”

Duk sai suka saki dariya su duka biyun. Haka suka kasance wajen cin abinci ma cike da farin ciki ba abinda suke sai hirar tafiyar su Shukura.

Alhaji Abdurrahman asalinsa mutumin Sakwato ne, matarsa Hajiya Hadiza ita ma Ζ΄ar asalin garin ce. Aikine ya kawoshi Kano yana koyarwa a B.U.K. Mutum ne mai rufin asiri, bayan aikin gwamnati yana haΙ—awa da kasuwanci lesuna da shadodi. Daidai gwargwado ya tsayawa yaransa kan tarbiya. Yaransu biyu, Shukura ita ce babba tana matakin level one tana karantar business admin. Sai Wasila mai bi mata tana matakin Ζ™arshe a makarantar secondary. Sun jima Allah bai basu haihuwa ba, dan haka suna Ζ™aunar yaransu sossai. Saidai Ζ™aunar da suke musu bai dakusar da hoΙ“basar Ι—orasu kan kyakkyawar tarbiya ba. Matarsa mace ce mai kirkir ga kawaici da kunya, komai Ι—ayansu zai yi ya kan yi shawara da Ι—aya. Zamansu gwanin sha’awa. Duk shekara sukan shirya tare da iyalansa a can garin Sakwato suke yin sallah su gaisa da Ζ΄an uwa. Wannan karonma suna shirya-shiryan tafiyane shi yasa su Shukura suketa zumuΙ—i.

Tun da ya rage saura kwana biyu tafiyar suketa shiri. Sun yi soye-soye da dama na dangin kayan fulawa da sunan tsaraba. Washegari da sassafe suka Ι—auki hanya cike da farin ciki. Suna tafe suna hira da mahaifinsu a hanya. Akwai fahimtar juna sossai tsakaninsu da iyayansu haka ko damuwarsu basa iya Ι“oye musu. Gefin la asar suka sauka. Nan da nan Ζ΄an uwa suka shiga hidima da su, musamman da suka kasance masu san jama’a kowa nasu ne. Shukura da Wasila gidan Baba Magajiya suka sauka saboda Ι—iyarta Asiya, sossai suke mutunci da ita kuma akwai shaΖ™uwa tsakaninsu.

Bayan gaishe gaishe da hirar yaushe gamo, kowanensu ya miΖ™e yana neman huce gajiya. Washegari da su Shukura aka Ι—auki azumi, ranar da zasu zo ne dai suka ajiye saboda halin tafiya. Tare da Asiya suka shirya kayan buΙ—a baki, komai ya yi musu yadda suke buΖ™ata, ana gab da shan ruwa Asiya ta soma neman yaron da zai kai wa Yusuf kayan buΙ—a baki amma ta rasa. Tilas tasa hijabinta da zumar kai masa da kanta. Shukura ce ta yi zuruf ta bita, tare suka jera tana yi mata Ζ™orafin data zauna ba nisa zata yi ba. Dariyar wasa ta saki tana faΙ—in,

“kodai ba kya son in je in miki kwacen saurayi. Ai na ji Gwaggo ta ce kullum ke ki ke aika masa da buΙ—a baki!”

Dukan wasa ta kai mata,

“zuciyata na riga na bada riΖ™onta ga Ahmadina shi kansa ya san da zamansa taimako kawai nake yi!”

Dariya suka sa gaba Ι—ayansu, Shukura tace,

“Yauwa sis ni kuwa ina zamu kai Ι—inkinmu? Mun zo da lace da atamfa da kuma shada wadda zamu yi anko mu uku hadda ke”

“Baki da matsala wajen tela zamu…”

Daidai lokacin suka Ζ™araso bakin Ζ™ofar shagon Yusuf, samu suka yi yana alwala. Sai da ya kammala suka gaisa Asiya ta miΖ™a masa kayan buΙ—a baki. KarΙ“a ya yi yana zuba mata godiya da sa albarka. Idanun Shukura kan Ι—inkunan shagon tana yaba fikirar mai shagon.

“BaΖ™uwa muka yi ne..”

“Eh daga Kano suka zo, zama mu kawo ma Ι—inkinsu anjima ayi haΖ™uri mun zo a Ζ™ure baΖ™i ne..””

Sai lokacin Shukura ta sauke idanunta akansa, Ι—as gabanta ya faΙ—i. Wani irin kwarjini Yusuf Ι—in ya yi mata. Mamaki take zuΖ™eΖ™en saurayi haka ya Ι“ige a Ι—inki, lallai bashi da girman kai. Da hanzari ya Ι—auke kansa jin yadda zuciyarsa ta buga lokacin da suka haΙ—a ido,

“Ke baΖ™uwa ba ki iya gaisuwa ba, a haka zan yi miki zuran layin Ι—inkin?”

Firgigit ta Ι—auke idanunta daga Ζ™aramin hoton Yusuf da yaransa data zubawa ido, shi ma ya lura da kallon da takewa hoton. A ranta kuwa tana Ζ™isima Ζ™ila Ζ™annansa ne ko Ι—iyan yayyunsa. Sai ta ji hausarsa ta bata dariya, ta kuma burgeta. Karon farko da ta ji daΙ—in hausar Sakwatawa domin ta maidasu ababben tsokanarta har faΙ—a suke yi da Asiya. Murmushi ta yi tana jin kunyar rashin gaisheshi da bata yi ba. A kunyace ta gaisheshi suka wuce. Rakasu ya yi da idanu wani irin yanayi na saukar masa. Suna tafe Shukura ta kasa haΖ™uri,

“wai Asiya wannan ne telan?”

“Shi ne me kika gani!”

“Ba komai”

Ta bata amsa a taΖ™aice. Haka suka Ζ™arasa gida, bakinta ya yi mata nauyi akwai abubuwan da takeson tambaya da yawa akansa amma kuma tana jin nauyin tambayar Asiyan domin dai ita dai mamaki take yi, matashi kamarsa yana Ι—inki kuma Asiya ta Ζ™ara tabbatar mata da family nasa babban family ne a garin Sakwato. Suna shiga gida suka yi alwala suka yi sallah. Daga nan suka baje anata hidimar buΙ—a baki tare da hirar yaushe gamo. A haka aka kira sallahr isha’i matan suka bi jam’i mazan kuwa suka wuce masallaci.

Ƙarfe tara daidai, suna zaune a tsakar gida saboda zafi da suke ji sakammakon Ι—an Ι—agawar hadari. Hira suke a hankali wani yaro ya yi sallama,

“Assalamu alaikum. Wai gashi in ji Yusuf”

Amsawa Asma’u ta ti haΙ—e da karΙ“ar kwanukan, fes dasu a wanke. Murmushi ta yi tana yaba tsaftar Yusuf ba su taΙ“a bashi abin Ι“uΙ—a baki ba, ba tare da ya wanke kwanon ba. Sai yaron ya miΖ™o mata leda baΖ™a. Ta karΙ“a tana mamaki, kafin ta yi magana ya furta,

“ya ce don Allah kadda a dawo dasu, hijabaine na Muhammad ne babu yawa sai kuma Gwaggo”

Kafin ta sami zarafin magana yaron ya fice, Gwaggo na Ζ™walla kira ko ya juyo saboda ya gargaΙ—eshi. Wasila ce ta yi zuruf ta buΙ—e ledar sai ga Ι—inki daidai da autan Gwaggo Muhammad Arif. Sai kuma hijabi dogo mai kyau da tsari. Sossai abinda ya yi ya faranta ransu. Ko ba komai ka gaishe da me gaisheka koda ba zai amsa ba. Haka suka cigaba da hira, wanda rabinta Gwaggo ta Ι“ige da bata labarin halin kirkin Yusuf da yi masa addu’ar samun mace tagari. Domin tasan komai da yake faruwa da shi kasancewar tana da Ζ΄ar alaΖ™a da Amne ta siye da siyarwa.

Sossai Shukura ta tsume tana mamaki da al’ajabin irin rayuwar da yake yi da iyalansa. Iya tausayi ta tausayi ta tausaya masa. Ji ta yi gaba Ι—aya hirar ta gundureta ta rasa abin da yake mata daΙ—i. Jan Asiya ta yi suka koma Ι—akinta. Wasila kuwa ta baje tana kakabin halin Labiba. A wajen kwanciya dai Shukura kasa jurewa ta yi ta muskuta tana duban Asiya,

“Wallahi Asiya sai na ji ina Ζ™aunar in ga matar mutumin nan haka kawai”

Kallon mara wayau ta yi mata, sai kuma ta gimtse fuska,

“uwar karambani ki yi mata me?”

“Ko Ι—aya bani da abin da zan yi mata, kawai so nake na ganta”

Murmushi ta saki,

“kinyi sa a gobe Gwaggo zata aikeni unguwarsu wajen surukarsa sai mu san dabarar da zamu yi mu shiga gidan”

Lumshe idanu ta yi tana Ζ™iyasta Labiba a zuci da idanunta. Washegari da safe suka kammala duk wani aiki daya danganci gyaran gidan. Shukura tsaf ta zage aka yi komai da ita. Duk yadda Asiya ta so ta huta Ζ™i ta yi. Wasila kuwa gado ta Ι—are tana sharΙ“ar baccinta. Misalin Ζ™arfe sha Ι—aya suka karΙ“i aiken Gwaggo suka Ι—auki hanyi. Tafe suke suna hira Asiya na Ζ™ara nuna mata wasu wuraren tare da bayaninsu. Sha Ι—aya da arba’in a fallon Amne ta yi musu. Basu wuce mintuna goma ba suka yi abinda ya kaisu suka fito. Tunda suka fito Shukura take bin Asiya da ido. Ta matsu ta ganta a gidan Labiba. Suna gab da shiga kwanarsu suka yi kiciΙ“is da shi ya fito hannunsa riΖ™e da Khalifa. Da murmushi kan fuskarsa yake Ζ™arasowa wajansu. Asiya ta saki ajiyar zuciya. Domin gaba Ι—aya kanta ya Ι—aure tana tunanin yadda zasu shiga gidan su awa? A mutunce suka gaisa, Shukura da take Ζ™oΖ™arin sunkuyar da kai Ζ™asa yake zolaya,

“Bakuwa me rowar gaisuwa!”

Duk suka yi dariya, ta miΖ™a hannu tana faΙ—in,

“Fine boy ina mamanka?”

Babu jinkirtawa ya miΖ™a mata Khalifan, daketa zuba Ζ™amshi. Can Ζ™asan ansa yana gode wa Allah da ya yi masa wanka duk da kukan da yake yi. Domin ko sisi bame siyansa haka suka wayi safiyar. Idanunsa akan Shukuran daya nace da kallonta,

“Allah Asiya yau dai sai kin shiga gidan iyalina!”

Dariya ta Ι—anyi, kasancewar ya sha yi mata tayin hakan tana dojewa. Ba musu ya yi musu jagora suka rankaya suna taΙ“a hira shi da Asiyan. Da sallama suka shiga, daidai lokacin ta fito banΙ—aki daga ita sai zani Ι—aurin Ζ™irji. Kanta babu Ι—ankwali sai kitson da ya kasance rabi a kitse rabi a kwance. Ummi da ta ke zaune kan abin sallah ta nufo mahaifinta. Ita ma tanata zuba Ζ™amshi. Hannunta ya riΖ™e, ya sauke idanunsa kan Labiba da take dubansu a yatsune. Lokaci daya takaici da kunya suka yi masa rufdugu. Ya dubeta murya a tausashe,

“Maman Ummi baΖ™i ne damu”

Sai da ta mula tukuna ta tanka,

“Nagansu!”

Daga haka ta sa kai Ι—akinta. Asiya ta yi wa Labiba kallon kin gani ko? A sace ya kallesu sai dai ganin babu sauyi kan fuskokinsu yasa ya Ι—an ji dama-dama. Jagora ya yi musu zuwa Ι—akin nata duk da bashi da kyan gani. Haka suka zauna a tsume babu wata mutuntawa. Ganin babu sarki sai Allah suka yi masu sallama suka wuce. Shukura dai ta Ζ™ara tabbatar da maganar Asiya saidai zuciyarta bata bar mamakin wautar Labiba ba.+

STORY CONTINUES BELOW

***

Cikin Ζ™anΖ™anin lokaci Yusuf da Shukura suka yi wata irin shaΖ™uwa. Har ta kai yana bayyana mata matsalar da yake fuskanta da Labiba. Kodayaushe takan nusar dashi yi mata uzuri tare da Ζ™arfafa masa guiwa wajen Ι“oye sirrin gidansa. Ta Ι“angaranta kuwa tun dawowarsu Sakwato ta kasa gane yanayin da zuciyarta take ciki tsakanin Ζ™aunar Yusuf da kuma tausayinsa. Sukan Ι—auki lokaci suna waya da shi, ko shi bai kirata ba ita zata kirashi. Haka Ummi yakan haΙ—asu awaya suna gaisawa. Duk lokacin da zasu yi aike Sakwato kuwa zata tsarma wani abu ta ce da Asiya a aikawa Yusuf ya ba wa Ummi tun tana yi mata tsiya har ta sa mata ido.

Shi ma a nasa Ι“angaren gaba Ι—aya Ζ™aunar Shukura da Ι—abi’unta ya zagaye zuciyarsa ya hanashi sakat. Sai dai yana tunanin yadda zai wanye da Labiba. Ba ya waya da ita sai yana waje, haka yakan gargaΙ—i Ummi kan faΙ—awa Mamanta tana waya da Aunty Shuu! Kamar yadda take kiranta. Sossai ya maida hankali kan sana’arsa Allah alhakeem kuma ya sa masa albarka, yana samu sossai domin har mashin irin na matasa ya saya. Ummi ya sauya mata makaranta zuwa ta kuΙ—i, haka kuma ya buΙ—e center yana yi wa yara training kan Ι—inki, tare da siyar da form kan farashi mai rahusa. Nan da nan wajen ya karΙ“u sossai.

***

“Kai ma Jawwad kasan halina wallahi, ai tunda ta nuna min ita muguwa ce ni nafita iya mugunta. Wallahi bazan bari ta samu abinda take Ζ™ulafuci ba. Ba dai haihuwa take buΖ™ata ba, to kuwa matuΖ™ar ba zan ci dukiyarta ba ba zan daina zama sanadin zubewar abin da take muradi ba. Na lura akwai shigar ciki a tare da ita kuma shi ma sai ya bi rariya”

“Amma Kabir zuwa yanzu fa ya kamata ace mun saduda, Mun soma girma ni wallahi tsoronma na yi aure na haihu nake yi kadda a rama kan yarana. Gashi gaba Ι—aya dangi sun Ι—oramin karan tsana, in samu ko Ζ΄ar bazawara ma abani an Ζ™i. To dangi ma sun Ζ™i ni ina ga waje. Kai gara kai babu wanda ya fuskanci haΖ™iΖ™aninka sai matarka”

“Ka cika yawa Jawwad kana nufin wai yanzu kai tuba zaka yi? Mtsss! Ni ka zo ka rakani in karΙ“o maganin kawai…”

Da sauri Zahidaht ta yi baya Ζ™irjinta na dokawa, ko ba a faΙ—a mata ba yau ta gama fahimtar Kabir ne sanadin Ι“arinta. Hannunta tasa ta toshe bakinta, a Ζ™oΖ™arinta na maida kukan daya taso mata. Kaicon rayuwar son rai irin ta Kabir ashe duk wahalar da take sha shi ne sanadi. Kuma tsabar rashin imani bai taΙ“a tausaya mata ba. Sake runtse idanunta ta yi ta juya zuwa Ι—akinta tana daddafa bango. Yau tana hango KUSKURANTA matuΖ™a wajan sakayawa ahalinta aihinin waye mijinta. Tana jin tashin motarsa wani zazzaΙ“i ya sake rufeta. Sai dai yau ta Ζ™uduri ko zai yankanta sai ta ga bayan Ζ™udurinsa. Kai tsaye Ι—akinsa ta nufa ta hau bincikar lokokin da ya ke ajiye magunguna. Ta himmatu wajen binciken Allah ya bata sa ar abinda take san gani ta gsnoshi. Ɗauka ta yi tana murmushi tana share hawaye,

“Kabir na sami makamin yaΖ™arka da izinin Allah”!

Ta yi furucin kamar tana gabansa. Juyowar da zata yi idanunta ya sauka akan nasa idanun. Take ta firgita sai kuma ta gimtse. Hannu ya miΖ™a mata fuska babu annuri. Ta ja baya tana furta,

“wallahi bazan bayar ba domin shi ne hujjata ga Baba Ɗangaladima..”

Bata karasa ba yasa hannu ya hankaΙ—ata, ta yi hantsile gefan gadonsa ya daki cikinta. Ta Ζ™wala Ζ™ara ta zube Ζ™asa. Kanta ya yi a kiΙ—ime amma bata ko motsi. Hankalinsa ba Ζ™aramin tashi ya yi ba.

***

Kwanaki biyu kenan suna tafka tsiya da Labiba saboda fuskantar yana waya da mace. Rashin mutunci take zubawa son ranta. Sai dai ko Ι—aga kai baya yi ballantana ya dubeta. Hasalima shi a waje yake wayarsa gudun fitina amma haka zata leΖ™o ta baranda tana jifansa da duwatsu kamar wata yarinya. Wani lokacin kuma ta kule gidan sai dai ya kwana a waje.

Kamar kodayaushe yau ma yana dakalin Ζ™ofar gidan yana waya. Shukura ce take bashi labarin sakammakon jarabbawarta suna ta nishaΙ—i abinsu. Zuwa lokacin daga shi har ita sun fahimci suna san juna amma sun gaza bayyana hakan. Kamar amafarki ya hango tahowar Labiba tana sanΙ—a zata rufe masa Ζ™ofa. Saurin miΖ™ewa ya yi ya shammaceta ya tura Ζ™yauran. Aikuwa ta yi taga-taga zata faΙ—i ya tarota jikinsa. Hannu tasa ta turashi ya bige da bango kansa ya fashe daga gefan goshi.

“Ash!”

Ya furta yana sauke wayar, daga can Shukura na tambayarsa lafiya, kafin ta sake magana ta tsinkayo muryar Labiba tana aunamasa zagi,

“Wallahi Yusuf baka isa ba ka na yi min waya da karuwanka A GIDANA!”

Hannu yasa ya tankaΙ—ata saboda yadda kansa yake zubar jini. Gefe ta yi tana hucci su Ummi sun yi cirko-cirko suna kallonsu. Kai tsaye waya ta Ι—auka ta dannawa Amne kira ta fashe da kuka. Ƙarya da gaskiya ta zauna ta shirya mata. Ga Yusuf nan ya yi mata mugun duka saboda ta kamashi yana waya da budurwa. Aikuwa kamar jira take, tana katse kiran ta kira Khamis tana rattaba masa buΖ™atarta. Babu jinkiri ya kwashi yayyanta maza na Ζ™asa dashi su biyar suka nufi gidan. Lokacin da suka je Yusuf yana tsaka da waya da Shukura tana bashi haΖ™uri kan abinda ya faru Labiba kuma tana Ι—aki da yaranta. Basu yi wata-wata ba suka rufeshi da dukan kawo wuΖ™a. Mamaki ya kasheshi kan dalilinsu na dukansa. Tun yana Ι—aukar abin a wasa har ya soma Ζ™oΖ™arin kare kansa.

“Me na yi muku?”

Shi ne abin da yake faΙ—a, sai dai sunΖ™i bashi damar da zai fuskanci laifinsa. Cikin mintuna goma suka sassaΙ“a masa kamani yadda baya zato. Tun yana motsi har ya zama sai dai ido. Acan Ι—aki gaba Ι—aya Labiba ta tsorata, domin tana kallon komai ta taga. Ummi kuwa banda kuka da kiran Abba babu abin da take yi.

“Labiba kwaso kayanki mu tafi!”

Ras! Gabanta ya faΙ—i, ita fa ba cewa ta yi azo arabata da mijinta ba. Kawai dai taso a Ι—an tsoratashi ne ya daina waya da mata. Sai yanzu ma ta gano wautarta na kiran Amne tunda tasan Ζ™udurinta kan auransu. Dakewa ta yi ta fito tana Ζ™unΖ™uni tare da tallewa Ummi Ζ™eya. Sai dai tana fitowa ta tsandara ihu,

“Na shiga uku Yaya Khamisu kun kashe shi wallahi sharri na yi masa!”_Kowane sauyi ya kan amsa sunansa sauyi amma ya kan zo da sauΖ™aΖ™Ζ™awar cikar mutuntaka matuΖ™ar baya tafe da sauyin nagarta._+

Tsabar takaici kasa cewa komai Khamis ya yi. Kafin ya farga ta Ι—auki waya ta kira Yaya Adam tana kuka. Bata Ι“oye masa komai ba, hankali tashe ya bata tabbacin yana hanya. Sai dai duk yadda taso zama agidan har zuwan nasu bata samu ba. Ζ³an uwanta suka tasa Ζ™eyarta tana kuka tana komai. Aka bar Ummi zaune gaban mahaifinta dake halin MUTUWA DA RAYUWA.

A kiΙ—ime yaya Adam ya Ι—aukeshi suka wuce asibiti mafi kusa. Ummi kuwa yaya Asabe ce ta tafi da ita. Ana shiga da Yusuf asibiti Kabir na shigowa da Zahidaht. Ka tsaye wajen taimakon gaggawa aka wuce dasu. Dukkansu basu san inda kansu yake ba. Baba ƊanΖ™wairo da Baba Ɗangaladima nan da nan suka nufo asibitin. GabaΙ—aya hankalin zuri’ar a tashe yake domin babu tabbacin halin da suke ciki. Jimawa kaΙ—an likita ya nemi ganin wani babba cikin dangin Zahidaht, Baba Ɗangaladima ne ya wuce gaba. Sai dai bayanin da likita ya yi masa ya kiΙ—imashi. Zuciyarta ce ta kumbura. FaΙ—a sossai likitan yake yi bisa sakacin da aka yi a take ya bayyana masa ana buΖ™atar ayi mata aiki da gaggawa domin cikin jikinta ya jirkita tana zubar da jini idan san samu ne suna buΖ™atar fitar da shi. Hankali tashe ya nemo Kabir domin ya saka hannu. Jikinsa a sanyaye ya sa hannu aka wuce da ita Kabir banda kuka babu abin da yake yi.

Wani irin yanayi yake ji akan Zahidahr. Gab da za a shiga da ita ta farka, babu wanda ta nema sai Kabir. Lokacin da ya zo kasa haΙ—a idanu da ita ya yi. Gashi ta kasa magana, so take ya kalleta koda sau Ι—aya ne ko zai fahimci saΖ™on da ya ke cikin idanunta amma ya gaza. Lumshe idanu ta yi, wasu hawaye na kwaranya a kwarmin idanunta da suka sake cikowa maimakon zurmawar da kowa ya santa da ita. Wani abu ta ke ji da ba zata iya kwatanta yanayinsa ba, tunda take a rayuwarta bata taΙ“a jin yanayin ba. Haka aka turata aka wuce da ita. Yana jin yadda idanuwanta suke yawo akansa, sai dai nauyi da yake ji bazai bari ya aikata umarnin zuciyarsa akan nata ba. Sossai yake muradin su haΙ—a idanu sai dai lokacin da ya nufaci hakan ya makara…

Bangaren Yusuf suka sake komawa, shi da sauΖ™i ya farfaΙ—o amma ya sami karaya a hannunsa na dama. Sai kuma karaya a cinyarsa ta hagu. Ana tunanin dole sai dai a turashi asibitin Ζ™ashi na Kano. Cikin Ζ™anΖ™anin lokaci asibitin ya Ι—inke da Ζ΄an uwa da abokan arziΖ™i. Sai dai kowa ka dubi fuskarsa jingum yake. ShuΙ—ewar awa biyu da mintuna likitocin da suka shiga da Zahidaht suka fito suna sharce gomi. A karo na biyu suka nemi ganin makusancinta. Wannan karon bayan Baba ƊanΖ™wairo hadda Kabir aka shiga. Sai da bayanin da likita ya yi musu ya girgizasu. Zahidaht dai ta amsa kiran mahallicinta. Sossai iyayen suka kiΙ—ime da tashin hankali. Kabir kuwa a guje ya fito, Jawwad da ya shigo asibitin kenan ya riΖ™eshi yana tambayarsa ba’asi. Sai ya saka kuka tare da dunΖ™ule hannunsa yana bugawa a bango.

“Jawwad ta mutu! Ta tafi ta barmin komai ta barni in ci tsiyata”

Kuka ya sarΖ™eshi ya durΖ™ushe awajen. Sossai yake kuka tare da tonawa kansa asiri bisa abubuwan da yake yi mata. Babu abinda ya Ι“oye. Jawwad ne ya janyeshi yana toshe masa baki. Iyayen kuwa ko takansa ba wanda ya bi aka Ι—auki gawarta zuwa gida. Banda shassheΖ™ar kuka babu abin da yake tashi cikin estate Ι—in. Tabbas mutuwar ta girgizasu. Musamman Yaya Asabe gani take kamar Zahidahn ta mutu da Ζ™ulinta aranta na hanata bayyanawa zuri’arsu halin da take ciki. Sai dai kukan da Kabir yake yi yana maimaita shi ne sillar mutuwarta ya Ι—auki hankalin ahalinsu. Da yawa masu zuciya kusa nan suka shiga aibatashi, wasu kuwa shiriya suke nema masa. Duk sai Jawwad ya ji ya muzanta domin dai abokin Ι“arawo Ι“arawone musamman da shi Akuyarsa ta fi ta kowa kuka. Da yawa ma suna Ι—ora laifin kan cewar shi ya kangarar da Kabir Ι—in.

Jikin Labiba ya yi bala’in yin sanyi, gani take kamar Yusuf ma mutuwa zai yi. Nan da nan ta shige can cikin Ι—akin Amne ta Ζ™unshe kanta. Banda kuka babu abin da take yi tare da danasani. Burinta kawai san sanin halin da Yusuf Ι—in yake ciki. Sai dai bata sami fuska wajen kowa ba. Tun dare aka haΙ—a gawar Zahidaht wshegari da safe aka Ι—auketa zuwa gidanta na gaskiya. Iyaye da Ζ΄an uwa na kokawa tare da kyautatta mata zato bisa haΖ™uri da juriyar ibadarta ta gidan aure. Koda aka je maΖ™abarta da Ζ™yar Baba Muttaka ya bari Kabir ya kamata aka sakata cikin gidanta na gaskiya, sai dai yana sakata ya yanke jiki ya faΙ—i dole aka wuce asibiti da shi domi karΙ“ar taimakon gaggawa. Da yawa daga cikin mazatan gidan asibitin suka wuce dan ganin halin da Yusuf yake ciki. Ba laifi jikin da sauΖ™i, kuma likitocin sun sami tattaunawar data kamata ana tunanin basai an kaishi Kano ba.

BAYAN KWANA UKU!

Kwanaki ukun makokin sun zo wa zuri’ar a hagunce, da yawa daga cikinsu babu walwala a tare da su. Shukura da mahaifanta takanas suka zo gaisuwa tare da duba jikin Yusuf. Sossai ya ji daΙ—in karamciΙ“ mahaifinta da karar da suka nuna masa. Hakan ya Ζ™ara mata Ζ™ima da kwarjini a idanunsa. Kabir dai an sallamoshi amma jininsa ya yi mugun hawa saboda tunani. Kwata-kwata ya tsangwani kansa baya zama wajen da mutane suke zaune. Idan ya zauna kuma ya dinga surutai kenan. Bacci kuwa sai da mutane a kusa da shi suna rirriΖ™eshi saboda firgita ya ke yana kiran,

“Gata nan! Gata nan!!”

Duk wannan taΖ™adamar da ake yi Labiba na gida tana fama da Ι—acin rai, ko bakin Ζ™ofa Amne ta kasa ta tsare ta hanata fitowa balantana ta sami damar dubo Yusuf. GabaΙ—aya mazan gidan sun saka mata idanu suna sanin ganin iya gudun ruwanta. Matan kuwa sun sami aikin yi. Tabarmar zaman makoki ta koma dandalin gulma.

Tun daga ranar da Yusuf ya farfaΙ—o yake tunanin hukuncin da ya kamaci Labiba a zuciyarsa. Idan ya zauna tunani sai yake hango shin wace rayuwa yaransa zasu yi BABU MAHAIFIYA. Sai dai idan ya tuna WA YAKE AURE ya kan ji ya tsani kansa. Kamar kodayaushe jingine yake da gadon da aka kwantar da shi, yaya Adam da shigowarsa Ι—akin kenan ya dubeshi da kulawa,

“Yusuf kana buΖ™atar wani abu ne?”

Shiru bai amsa masa ba, sake maimaitawa ya yi amma kuma bai motsa ba. Da sassarfa ya Ζ™arasa tare da girgizashi. Ya saki ajiyar zuciya mai Ζ™arfi,

“Yaya yaushe ka shigo?”

HaΙ—e fuska ya yi yana dubansa,

“Lokacin da ka tafi duniyar tunani. Look Yusuf nasan ba tunanin kowa ka ke yi ba sai na Labiba. Ba zan hanaka tuna matarka ba amma wallahi tun wuri ka sauyawa kanka taku. Yau kwananka nawa a cikin asibitin nan cikin mawuyacin halin da ita ce silla? Amma babu Ζ™afarta babu ta mahaifiyarta ballantana wani makusancinta. Wannan bai isheka ishara ka fahimci wa ka ke aure ba?”

Ƙansa a Ζ™asa idanunsa taf da hawaye, muryarsa ta yi rauni sossai ya furta,

“Ku yi haΖ™uri komai lokacine!”

Mamaki ya kashe Adam Ι—in, domin a tunaninsa sakin Labiba zai yi amma sai ya ga saΙ“anin hakan,

“Yusuf wace irin zuciya ce da kai?”

“Yaya ba a gyara Ι“arna da Ι“arna. Kamar yadda ba a nunawa sakarai illar sakarci ta hanyar sakarci. Yadda ake tafiyar da wanda ya jahilci hanya bisa tafarkin da ya kamata hakane ya kamaci Labiba. Mu kasance masu uzuri agareta koda zai kai karo saba’in ba aibu bane!”

Baba ƊanΖ™wairo da ya shigo Ι—akin jinyar ya furta,

“Allah Ya albarkaci tunaninka Yusufa!”

Tsabar takaici kasa cewa komai yaya Adam Ι—in ya yi yasa kai ya yi ficewarsa. Shi kuwa lumshe idanu ya yi yana ayyana gejin da ya kamata ya Ι—auki mataki a kanta ba wai yanzu ba.

Post a Comment for "WATA MACE CHAPTER 4 BY SANA S MATAZU"