SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA                     Www.bankinhausanovels.com.ng  Kafun mintuna kaɗan dandazon mutane sun cika kan babban titin da hatsarin yafaru, kowa salati kawai yakeyi domin kuwa duk wanda yaga yanda motar Zaid tayi ƙwatsa ƙwatsa  bazai taɓa tunanin mutumin dake ciki zai fito a raye ba,   gaba ɗaya mutane carko carko sukayi kowa tsoron zuwa wajen motar yake gudun kada wuta ta tashi dashi, domin kuwa har motar tafara tashin hayaƙi, wasu daga cikin mutanen da suka taru a wajenne suka taimaka suka ƙarasa wajen motar,  da ƙyar suka iya zaluƙo Zaid wanda gaba ɗaya fuskarsa ta ɓaci da jini duk jikinsa jini ne,   kallon gawa kawai mutanen da suka ciro sa suka shiga yi masa, domin kuwa a yanda suka gansa babu alamar rai ajikinsa, babu kuma alamar cewa zuwa nan gaba zai iya farfaɗowa, sai dai kuma ba’aja da ikon mai sama (ALLAH)  Dai dai lokacin motar ƴan sanda suka ƙaraso wajen, kai tsaye su suka ɗauki Zaid suka sanyasa acikin motarsu, direct aka wuce asibiti d…