Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kafun mintuna kaΙ—an dandazon mutane sun cika kan babban titin da hatsarin yafaru, kowa salati kawai yakeyi domin kuwa duk wanda yaga yanda motar Zaid tayi Ζ™watsa Ζ™watsa  bazai taΙ“a tunanin mutumin dake ciki zai fito a raye ba,   gaba Ι—aya mutane carko carko sukayi kowa tsoron zuwa wajen motar yake gudun kada wuta ta tashi dashi, domin kuwa har motar tafara tashin hayaΖ™i, wasu daga cikin mutanen da suka taru a wajenne suka taimaka suka Ζ™arasa wajen motar,  da Ζ™yar suka iya zaluΖ™o Zaid wanda gaba Ι—aya fuskarsa ta Ι“aci da jini duk jikinsa jini ne,   kallon gawa kawai mutanen da suka ciro sa suka shiga yi masa, domin kuwa a yanda suka gansa babu alamar rai ajikinsa, babu kuma alamar cewa zuwa nan gaba zai iya

farfaΙ—owa, sai dai kuma ba’aja da ikon mai sama (ALLAH)  Dai dai lokacin motar Ζ΄an sanda suka Ζ™araso wajen, kai tsaye su suka Ι—auki Zaid suka sanyasa acikin motarsu, direct aka wuce asibiti dashi, duk da suma dai basu da tabbacin cewa yana da rai ko bai da shi….+

Emergency aka karΙ“i Zaid yayinda likitoti suka shiga basa taimakon gagawa domin kuwa sun gano cewa akwai rai ajikinsa, kawai de yayi mummunar buguwa ne…..  Saida suka share masa jinin dake kan fuskarsa kafun Dr.Bilal ya iya shaida fuskar Zaid Ι—in, take hankalinsa yaΖ™ara tashi, tsananin tausayin Zaid Ι—in ya kamasa, shin wani irin hali Alhaji Ma’aruf zai tsinci kansa idan yaji wannan mummunar labarin?,,,, haka dai sukayi iyaka Ζ™oΖ™arinsu wajen shawo kan al’amarin sai de kuma duk yanda suka so yadawo hayyacinsa abun yaci tura, abu Ι—aya suka dogara dashi, idan har baidawo hayyacinsa nan da 3 days ba, to fa lallai akwai matsala…. Kallon sauran abokan aikinsa Dr.Bilal  yayi haΙ—e da soma cire safar hanunsa, ganin haka yasanya suma suka cire nasu safan, daga nan suka fice daga cikin Ι—akin…

Kallon sauran Doctor’s Ι—in Dr.Bilal yayi haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya.    “Mubashi nanda 24 hour maybe zai yi farfaΙ—owa, sai de kuma Allah yasa buguwan da yayi bai taΙ“a masa lafiyan kansa ba”

“Insha Allah kansa bazai samu wata matsala ba, sai de kuma yakamata a nemi ahalinsa a sanar musu”  Wani Dr. yafaΙ—i haka..

“Insha Allah” Dr.Bilal yafaΙ—i haka ga abokan aikin sa, bayan ya soma laluΙ“an Numbern Dad Ι—in Zaid….

Alhaji Ma’aruf ne zaune a cikin katafaren falonsa wanda yagaji da haΙ—uwa, gefe dashi Hajiya Sajida ce tazuba tagumi daganinta kasan cewa tana cikin damuwa…  “Menene abun Ι—aga hankali har haka Hajiya?  kinfasan Zaid ba yaro bane shi, kuma faΙ—uwar gaban nan da kikeji nima inajinsa, sai de kuma…..” Maganar Alhaji Ma’aruf ne  ya katse sakamakon wayarsa da ta soma ruri alaman shigowan Ζ™ira,,,  mamakine ya bayyana akan fuskar Alhaji Ma’aruf  ganin cewa Dr.Bilal ne ke Ζ™iransa,,   bayan sun gaisane Dr.Bilal yayi gyaran murya haΙ—e da cewa Alhaji Ma’aruf  Ι—in yana buΖ™atar ganinsa,,, murmushi Alhaji Ma’aruf yayi  haΙ—e da cewa “Kakuwa ci sa’a ina gida, sai de ka hanzarta zuwa saboda zuwa Ι—an anjima zan fita”
Ajiyar zuciya Dr.Bilal ya sauΖ™e  haΙ—e  da cewa “Kayi haΖ™uri Alhaji amma maganar bata gida bace, Magana ce me matuΖ™ar mahimmanci kuma yana da kyau kazo Ι—in”
Cikin Ι—aurewar kai Dad yace da Dr.Bilal gashinan zuwa..

Kallon Alhaji Ma’aruf Mom tayi haΙ—e da cewa “Wayene, kuma me yake faruwa?” atake Mom taje romawa Dad waΖ΄an nan  tambayoyin..

STORY CONTINUES BELOW
“Bansan meye bane, amma idan naje zanji koma menene, Allah yasa dai ba matsalan Zaid bane” Alhaji Ma’aruf yafaΙ—i haka yana me nufar hanyar fita daga cikin falon nasa..

Da “Ameen” kawai Mom ta amsa masa domin kuwa tun Ι—azu takejin faΙ—uwar gaba, kuma duk taji jikinta yayi sanyi..

Cikin mintuna Ζ™alilan Dad ya iso asibitin,    kallo Ι—aya yayimawa fuskar Dr.Bilal ya fuskanci cewa akwae damuwa…

Bayan sun zaunane Dad yakai dubansa ga Dr.Bilal wanda yarasa ta’inama zaifara sanar da Dad Ι—in abundake faruwa…

“Inajinka Bilal kaΖ™irani  Ζ™ira na gaggawa sai gashi nazo kuma kayi shiru”

Ajiyar zuciya Dr.Bilal yayi haΙ—e da gyara zamansa   “Bansan ya zaka Ι—auki zancen bane Alhaji, amma kuma kasan me rai baya rabuwa da Ζ™addarorin rayuwa….”

“Bangane inda maganan ka ta dosa bafa Bilal, inaga zai fi kyau kamin yanda zanfahimta” Dad yafaΙ—i haka ta hanyar katse  Dr.Bilal  daga maganan da ya keyi..

Ɗan numfasawa Dr.Bilal yayi haΙ—e da soma cewa.
“Wato Alhj kamar dai  yanda na faΙ—a ma, ko wani bawa da irin tasa Ζ™addaran, dakuma irin yanda take zuwar masa, bazan Ι“oye maka ba Alhaji Ma’aruf, Ι—azu aka kawo mana Zaid yasamu haΙ—ari, yanzu haka yana accident & emergency munyi iyaka Ζ™oΖ™arinmu sai dai haryanzu bai farfaΙ—o ba, amma  insha Allah muna sa ran farfaΙ—owarsa nan bada jimawa ba”

Tuni Alhj Ma’aruf yacire hula’r dake kansa, salati kawai yakeyi, iya Ζ™ololuwan tashin hankali ya shigesa…..  “Ɗana Zaid fa kace Bilal, Ι—azu Ι—azu fa muka rabu dashi, amma kaduba fuskar da kyau kuwa?” Dad yatambayi Dr.Bilal cike da tashin hankali.

“Ƙwarai Alhj, amma ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai dai dai ta, muje ka gansa domin kuwa zuwa anjima babu wani wanda zamu bari yagansa, saboda yana da buΖ™atar hutu sosai”
Babu musu haka Dad yabi bayan Dr.Bilal har zuwa Ι—akin da Zaid ke kwance tamkar gawa, yayinda aka Ι—aure gaba Ι—aya kansa da bandage, sannan kuma an saΖ™alla masa wasu irin na’urori ajikinsa..

Hawayene suka cika idanun Alhj Ma’aruf alokacin da idanunsa sukai masa tozali da Zaid kwance kamar gawa,,   “wannan wace irin jarabawa ce  Zaid ya haΙ—u dashi, daga wannan sai wannan?” Alhj Ma’aruf yayi mawa kansa tambayar da baida wani me amsa masa ita…. Ganin da Dr.Bilal yayi cewa hankalin Alhj Ma’aruf yatashi sosai, yasanya ya jasa cikin office Ι—insa yashiga Ζ™arfafa masa guiwa akan cewa insha Allah nanda gobe Zaid Ι—in zai iya farfaΙ—owa, suna kuma sa ran cewa idan ya farfaΙ—o bazai tashi da wani matsala ba sai de Ι—an abun da baza’a rasa ba…   Shi dai Alhj Ma’aruf  jin Dr.Bilal kawai yakeyi, amma badon yana fahimtar abun da yake faΙ—a ba, a yanda yaga Zaid kamar gawa shiyafi komai Ι—aga masa hankali, yanzu tayaya ma zaije ya fuskanci Hajiya Sajida da wannan magana ?……

Lokacin da labarin hatsarin da Zaid yayi ya’isa cikin kunnen Hajiya Sajida da labisat baΖ™aramin tashin hankali suka shiga ba, haka su kazo asibitin damuwa bayyane akan fuskarsu, da Ζ™yar Dad ya iya rarrashin su, amma duk da haka basu daina kuka ba….

****
Duka hannayenta ta Ι—aura akan Ζ™uncinta,  kallo Ι—aya zakai mata kafuskanci cewa tana cikin damuwa, saboda  lokaci Ι—aya rama ta bayyana kanta ajikinta,    ita kanta batasan meke damunta ba, sai dai tasan cewa zuciyarta tana Ι—auke da damuwa me tarin yawa,  takan tsinci kanta cikin wani irin hali idan tatuno da cewa aurenta da Dr.Sadeeq saura Ζ΄an kwanaki ne suka rage, haka kuma takanjin matsanancin faΙ—uwar gaba aduk sanda Zaid yafaΙ—o cikin Ζ™wanyanta…

Wayarta ce tasoma Ζ™ara alamar shigowar Ζ™ira yayinda sunan Dr.Sadeeq yasoma yawo akan screen Ι—in wayar.   Cikin sanyin jiki ta Ι—aga wayan haΙ—e da karawa akan kunnenta, cikin muryarta me sanyi tayi masa sallama.

STORY CONTINUES BELOW
Fuskarsa Ι—auke da murmushi ya amsa mata, tamkar yana a gabanta,    “Kitaimaka ki fito ina Ζ™ofar gida” Abun Dr.Sadeeq yafaΙ—a kenan..

Ajiyar zuciya ta sauΖ™e haΙ—e da cewa “gani nan fitowa…”

Tana aje wayar ta fidda wani irin numfashi haΙ—e da cije laΙ“Ι“anta, sai da tayi kusan mintuna 5 a zaune kafun ta miΖ™e tsaye haΙ—i da Ι—auko wani mayafi ta sanya ajikinta…..  Kaitsaye hanyar fita daga cikin gidannasu ta nufa…
Kanta duΖ™e  a Ζ™asa haka take tafiya, harta Ζ™araso wajen da motarsa ke fake….. Hanu tasanya ta Ζ™wanΖ™wasa glass Ι—in window’n  motar kasancewar yana cikin motar baifito ba. Ahankali ya sauΖ™e glass Ι—in windo’n Ζ™asa, haΙ—e da sakar mata murmushi,, itama murmushin tayi masa haΙ—i da buΙ—e murfin motar tashiga bakinta Ι—auke da sallama..

Fuskarsa Ι—auke da murmushi ya amsa  sallama’n nata, haΙ—e da kafeta da idanunsa, tun fitowarta agida yake kallonta, sosai kuma ya hango damuwa atattare da’ita.

“Nayi zaton bazaki fito ba kinyi fushi dani” yafaΙ—i haka still manyan eyes Ι—insa na kanta…

Murmushinta me kyau tayi masa haΙ—i da Ι—an satan kallonsa, sosai yau Ι—in yayi mata kyau, gashi fuskarsa taΖ™ara haske sannan sajensa ya sha gyara,
” shima dai gaskiya kyakkyawa ne” tafaΙ—i haka acikin zuciyarta….

“Mezai sa nayi fushi dakai? nasan cewa hidima ne yayi maka yawa, kuma ae bani kaΙ—ai bace, itama kuma waccar Ι—in tana buΖ™atar kulawa daga gareka, kaga kenan bakayi laifin da zai sanya nayi fushi dakai ba” tafaΙ—i haka da iyaka gaskiyarta…

Murmushi Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da sake maida hankali da kuma idanunsa a kanta,,  tabbas wannan abun da Zahrah keyi kishine,  “to idan dai hartana kishinsa kenan tana son sa kamar yanda yake sonta?” tambayar da baiyi da amsarta,  bazai yaudari kansa ba, yasani Ζ™warai Zahrah batayi masa so me tsanani kamar yanda shi yake mata, amma kuma hakan bazai zamo wani babban abun damuwa a garesa ba, saboda yasani da yardan Allah watarana zata sosa zakumayi tayi masa SON SO…

“Ya aiki?” Zahrah ta faΙ—i haka ta hanyar katse masa tunanin dayakeyi gashi kuma yasanyata agaba sai kallonta yake kamar yasamu hoto..
Ajiyar zuciya ya sauΖ™e….. “Aiki babu sauΖ™i Princess yanzuma cancel Ι—in wani aiki nayi nazo, saboda inaga yakamata ace nasan duk wani tsare tsaren da zakiyi,  kingafa lokaci yana Ζ™ara matsowa, banaso ayi komai a Ζ™urarren lokaci”

Murmushi kawai tayi haΙ—e da sunkuyar da kanta Ζ™asa, cikin murya me sanyi tace “aini ba wani tsare tsaren da zanyi”

“Meyasa?” yatambayeta ataΖ™aice.

“Kawai”
itama tabashi amsa ataΖ™aice, domin ita har ga Allah bata da niyar yin ko wani  irin program’s ne, ko walima batasa aranta cewa zatayi ba.

“Shikenan to, amma dai nikam zan shirya mana diner, saboda haka ki shirya, zankuma samu  Husnah muyi magana da’ita akan yanda tsare tsaren bikin zai kasance sbd na lura kamar ke bason auren nan kike ba”

Saurin Ι—ago da kanta tayi ta kalleshi,   giransa Ι—aya yaΙ—aga mata yana murmushi..

Turo Ι—an Ζ™aramin bakinta gaba tayi haΙ—e da cewa “Nifa bance banason auren nan ba, kawai de banshiryawa program’s Ι—in  bane!” taΖ™are maganar cike da shagwaΙ“a …

Kallonta yashigayi na tsawon wasu mintuna kafun yayi murmushi….

“Meke damunki ne kwana biyu, ko baki da lafiya ne?”    ya jefo mata tambayar da bata tsammata ba.

Kallon kanta tashigayi domin tambayartasa ta bata mamaki sosai,  “me ka gani?”  ta tambaya cike da tsarguwa.

“Naga kin rame ne, ko ba kya cin abinci ne? Ya kuma tambaya cike da kulawa.

Ɗan murmushi tayi haΙ—e da cewa “inaci”
“To  ko dai aure kikeso ne?” yakuma tambayarta.
Saurin Ι—ago da kanta tayi takallesa saikuma tayi saurin maida kanta tsakan kanun cinyoyinta, wannan magana tasa da matuΖ™ar sanya mutum jin kunya take..

STORY CONTINUES BELOW
Murmushi yayi har saida haΖ™waransa suka bayyana,  dama yafaΙ—i hakane don yaga kunyarta to gashinan yagani cikin sauΖ™i…

“Kunyan me kikeji, dan natambaya ko aure kike so? ae dai naga kamar kin matsu da a Ι—aura aurenne”  wannan karon cike da zolaya  yaΖ™are maganar..

Murmushi Zahrah tayi haΙ—e da sake cusa kanta a tsakankanun cinyoyinta, shi dai halinsa ne sanya mutum yaji kunya…

“Ya zamuyi da maganar Ι—inkin kine?” yafaΙ—i haka don son kawar da wancan zancen..

Sai alokacin  Zahrah ta’iya  Ι—ago kanta,  sai dai kuma  bata iya  kallonsa ba.
Wani Ι—an abu dake manne acikin motar kamar  drower yajawo haΙ—e da ciro wani babban envelop dake aje ciki…
“Kiyi manage da wannan kafun nasake dawowa” yafaΙ—i haka yana me Ι—aura mata envelop Ι—in akan cinyarta… Kallon mamaki tashiga yi masa saboda bata fahimci menene acikin envelop Ι—in ba.  Kansa ya jinjina haΙ—e da sakar mata murmushi,,   ta buΙ—e baki zatayi magana kenan yayi saurin sanya hanunsa akan laΙ“Ι“ansa haΙ—e da cewa “Shiiiii banson kice komai, kije gida zamuyi waya, kinji my beutiful Wife!” yaΖ™are maganar yana me kashe mata idanunsa Ι—aya.
Murmushi kawai tayi masa haΙ—e  da buΙ—e murfin motar tafice bayan ta riΖ™e envelop Ι—in a hanunta,, yana ganin shigewarta gida shima yaja motarsa yabar Ζ™ofar gidan nasu..

Ajiyar zuciya Zahrah tasauΖ™e sakamakon ganin irin maΖ™udan kuΙ—aΙ—en da Dr.Sadeeq ya bata,,    wayarta tajawo haΙ—e da dannawa number’n Husnah Ζ™ira, bugu Ι—aya Husnah taΙ—auki wayar haΙ—e da cewa “Bride”

Murmushi Zahrah tayi haΙ—e da cewa “ina buΖ™atar ganinki Husnah”  
“Okay wannan ae ba’abun damuwa bane,  bani nan da 30 minute inazuwa”
Cike da jin daΙ—i Zahrah ta kashe wayan,   taji daΙ—i da Husnah tace gatanan zuwa, domin tabbas tana buΖ™atar taimakon Husnah.

Kamar yanda Husnah ta faΙ—a kuwa bawani  Ι“ata lokaci ta iso gidan su Zahrah,  KuΙ—in da Dr.Sadeeq yabata ta miΖ™o mawa Husnah,,   murmushi Husnah tayi  bayan ta gama Ζ™irga duka kuΙ—aΙ—en, domin dai ita dama Ζ™irga kuΙ—i baya wani bata wahala,   “200,000” Husnah tafaΙ—a tana kallon Zahrah.

Murmushi Zahrah tayi haΙ—e da cewa ” Gaskiya Ζ™awata kin iya Ζ™irga kuΙ—i sharp-sharp saikace wata ma’aikaciyar banki!” cike da zolaya ta Ζ™are maganar,,, dariya suka sanya su duka biyu…

“Yanzu dai kamata yayi  mufara Ζ΄an shirye shiryen da zamuyi, kuma kinga yakamata ace tun yanzu kinfara gyaran jiki” Husnah tafaΙ—i haka.

“Gyaran jiki kuma Husnah ? to ae ni banga wani aebu ba ajikina da zan gyara” Zahrah tafaΙ—i haka tana me Ζ™arewa fatar jikinta kallo..

“Ae basai kinga wani aibu ajikinkiba zaki gyara  Zahrah, ke dai yanzu tashi zakiyi muje gidan Auntie Amina takaimu wajen wannan me gyaran amaryan, kinsan tace mana 100,000  ne kuΙ—in aikinta, so kuma gashi yanzu munsamu kinga babu amfanin yin jinkiri, tashi maza muje” Husnah tafaΙ—i haka tana me miΖ™ewa tsaye.
Zahrah ma miΖ™ewa tayi haΙ—e da janyo mayafinta ta yafa….  Sai da suka fita har bakin titi kafun suka samu taxi suka shiga direct gidan Aunti Amina (Ζ™anwar Maman Husnah) suka nufa,  suna zuwa kuwa Auntie Amina tasa babbar Ζ΄arta Suhaima  wanda suke sa’anni da Husnah tayi musu rakiya zuwa gidan Hajiya Shuwa  wanda itace me gyaran amarya, Hajiya Shuwa dai Ζ™wararriyar megyaran jiki ne,  sosai take gayara mace  daga uwar gida har amarya, sosai ta shahara a wannan Ι“angaren ta iya gyaran jiki,  sannan kuma  ingantattun magunguna take haΙ—awa wanda idan kikasha saikin bada labari,    Husnah ce taja Hajiya Shuwa gefe tace tayi mawa Zahrah gyara me kyau sbd Ζ™addara yasa tarasa budurcinta, aikuwa babu cutarwa Hajiya Shuwa tace zata gyarata sosai da sosai, duk da abune wanda bazai taΙ“a yiwuwaba  ace tadawo virgin, amma zatayi iyaka Ζ™oΖ™arinta taga ta haΙ—eta ciki da waje…. Hajiya Shuwa ta yankawa Zahrah rana cewa sati uku zasuyi suna gyarata, daga randa aka fara gyarata kuwa to fa fita ya Ζ™are mata sai dai idan da dare, domin ba’aso rana yataΙ“a ta… Haka suka baro gidan Hajiya Shuwa, daga nan Shoprite Husnah taja Zahrah suka nufa, 100k Ι—in da yayi saura Husnah ta Ι—auki 50k aciki ta jidawa Zahrah english wears masu kyau da nuna tsiraici,  hatta kayan bacci sai da Husnah ta zaΙ“awa Zahrah, nagani na faΙ—a irin wanda ake Ζ™ira dashi gwamma babu,, ita dai Zahrah kallon Husnah kawai take, amma takasa cewa komai, haka suka gama Ζ΄an sayayyansu suka koma gida, sai da akayi sallan Magrib kafun Husnah tayiwa Zahrah sallama tatafi gida…….

STORY CONTINUES BELOW
*****

Ƙarfe 3 na yammacin yau kenan amma har yanzu Zaid bai farfaΙ—o ba, tun da safe ake sa ran farfaΙ—owarsa amma shiru har zuwa yanzu, gaba Ι—aya hankalin Mom atashe yake, gani takeyi tamkar Zaid Ι—in ya mutu ne, domin kuwa tun safe take tacewa abarsu su gansa, amma sam likitotin nan sun hanata ganinsa, saboda ba a buΖ™atar kowa yaje kusa dashi, sai dai idan harshi yafarfaΙ—o yabuΖ™aci hakan….
*****

Abu kamar wasa yau kwanan Zaid biyu acikin asibitin amma koda Ι—an yatsarsa ne bai motsaba,  wannan ne yaΖ™ara jefa Ζ΄an uwansa cikin tashin hankali, bama kamar Alhaji Ma’aruf domin kuwa Dr.Bilal yasanar masa cewa Zaid yakamu da wata irin ciwon zuciya me tsanani, wanda idan har ba’akiyaye ba to tabbas rayuwarsa tana cikin hatsari…
Sama sama yake fitar da numfashi ta bakinsa, yayinda ya soma  buΙ—e manya manyan idanunsa a hankali. gaba Ι—aya abun da yafaru dashi yadawo masa cikin kansa,  saurin Ι—ago hanunsa yayi yashafi kansa wanda gaba Ι—aya aka Ι—aure masa shi da bandage,, dai dai lokacin Dr.Bilal yashigo cikin Ι—akin,,,  fari’a ne ya faΙ—aΙ—a akan fuskar Dr.Bilal sakamakon ganin da yayi Zaid  yafarfaΙ—o…..”Alhmdlh sannu yajikin naka?” Dr.Bilal yatambayi Zaid daya kafesa da’idanu.

Bai iya amsa masa ba, sai kansa kawai daya Ζ™aΙ—a, lokaci guda kuma yasoma yunΖ™urin tashi zaune,   “Auuushhhhh!” Zaid yafaΙ—i haka da Ζ™arfi yana mesanya hanunsa akan  Ζ™afarsa na dama da take masa wani irin raΙ—aΙ—i..

“Sannu, kwanta ae basai ka tashiba akwai rauni sosai ajikin ka, musamman ma aΖ™afarka, saboda haka ka kwanta kawai” Dr.Bilal yafaΙ—i haka bayan ya Ι—aga Ζ™afar Zaid Ι—in na dama ya maida ita gefe saboda akwai ciwuka sosai ajikinta, ko kyakkyawan motsi ba’aso tayi, saboda ciwukan zasuji kamar ana Ζ™aiΖ™ayasune…

Dr.Bilal yana fita bai jima ba saigasu Alhaji Ma’aruf da Mom sun faΙ—o cikin Ι—akin,,, Mom na ganin Zaid ta fashe da kuka haΙ—e da Ζ™arasawa garesa ta kamo duka hannayensa,,,  sannu kawai taketa aikin jero masa saikace wanda  ya tafito a labour room.Lol…… Da kai kawai yake iya amsa musu sannun da suke yi masa,,,   Dr.Bilal ne yakuma shigowa cikin Ι—akin.  hanunsa Ι—auke da wasu magunguna haΙ—e da allurai…  Kallon Mom yayi haΙ—i da cewa “Hajiya inaga yakamata ace anhaΙ—a masa ko tea ne saboda akwai allurai da magungunan daya kamata ace yasha, zakuma su iyayi masa illa idan har baici abinci ba,,,  jikin Mom harrawa yake tace “Akwai ma abinci likita ae sainabashi yaci ko”

“A’a Hajiya tea yakamata ace yasha idan yaso daga baya saiyaci abincin”  kafun ma Dr.Bilal yaΖ™are maganar Mom  tanufi wani  Ι—aki da aka basu, wanda anan ma suka kwana, kuma dama akwai kayan haΙ—a tea wanda Labisat ta Ι—auko musu a gida sukayi breakfast,,, mintuna kaΙ—an Mom tahaΙ—owa Zaid tea me kauri,  da taimakon Dad Zaid yatashi ya zauna,, Mom dakanta take bashi tea Ι—in saboda tsabar soyayya, shikuwa sai wani jan aji yake, idan takawo  cup Ι—in bakinsa sai yaΙ—an Ι“ata lokaci kafun yake buΙ—e baki yasha….   Ko rabin cup Ι—in baishaba yakawar da kansa gefe alaman ya Ζ™oshi…
Duk yanda suka so yasha tea Ι—in sosai hakan ya gagara, Zaid yana da taurin kan tsiya, idan baiso abuba babu wanda ya’isa sanyasa yayi dole..   Allurai guda biyu Dr.Bilal yayi masa, haΙ—e da basa magunguna masu kashe raΙ—aΙ—i da zafin ciwo….   Jin gina bayansa yayi da jikin pillow haΙ—e da lumshe idanunsa,,  imagine fuskar Zahrah kawai yakeyi acikin idanunsa, kowani bugu Ι—aya na zuciyarsa tare da soyayyarta yake tafiya, soyayyar Zahrah yazame masa rayuwa da numfashinsa, soyayyar Zahrah yazame masa jini acikin jikinsa,  sai dai kuma baisan meyasa duk kwanan duniya Zahrah take Ζ™arayi masa nisa ba…

Labisat dake zaune a gefensa taΙ—an saci kallonsa, akaro na barkatai, tabbas ta fuskanci cewa yayanta yana cikin tarin damuwa, wanda damuwar ita ke haddasa masa faΙ—awa cikin matsala,  amma kuma a iya zurfin hankali da tunanin ta tagano cewa SOYAYYA ita kaΙ—aice damuwar da take Ι—aiΙ—aita nutsuwar Ι—an adam alokaci guda, itace abu mafi saurin ruguza rayuwar Ι—an adam, SOYAYYA bata da daΙ—i ko kaΙ—an, domin kuwa itama Soyayya ta Ι—aiΙ—aita mata rayuwa batare da Ζ΄an uwanta sun sani ba, har yau abun na ranta, takuma bunnesa acikin zuciyarta, sai dai kuma tana tsoron ranarda asirinta zai tonu, batasan wani kallo iyayenta zasu mata ba…

“Labisat!” Zaid yaΖ™ira sunanta.

Saurin dawowa daga duniyar tunanin da take tayi haΙ—e da amsa Ζ™iran da yayi mata.

“Ina wayana?”
Idanu Labisat tashiga warewa ko zata hango  wayartasa acikin Ι—akin amma bataga ko alamar taba..

“Bro bangantaba sai dai idan su Dad suka dawo saina tambayesu ko…….”
“Enough” Zaid yafaΙ—a ataΖ™aice bayan yaΙ—aga mata hannu.. saboda yasanta  yanzu saita cika masa kunne da cakwaikwaiwa.

Gum Labisat tayi da bakinta, haΙ—e da komawa mazauninta ta zauna, azuciyarta kuwa cewa take “Jarabansa baya taΙ“a Ζ™arewa yana a halin rashin lafiya ma amma baifasa gwada halin nasa ba”……..
*******

“Gaskiya Doctor yana Ζ™oΖ™ari sosai Zahrah, kinga yanzufa yakuma turo dubu Ι—ari da hamsin a account Ι—ina, kuma kinsan shekaran jiya yaturo dubu Ι—ari wai kuΙ—in lalle, nidai nagama gane Doctor Ι—in kinnan so kawai yake yajiki a hanunsa”
Murmushi Husnah tayi haΙ—e da cewa “Nima narasa yazanyi dashi Husnah two days Ι—innan yana min Ι“arin kuΙ—i, idan nayi masa magana kuma sai yace wai amarya dole saida kuΙ—i”
“Ae kumafa gaskia yafaΙ—a, kinga dole sai akwai money abubuwa zasufi zama mana dai dai, yanzu kinga gobe nefa za’afara miki gyara yakamata mu kammala abubuwan mu tun ayau..” Husnah tafaΙ—i haka tana me yafa mayafi ajikinta. Zahrah batakai ga bata amsa ba Momyn Husnah tashigo hanunta Ι—auke da wani Ζ™aton baΖ™in leda.
“Yanaga duk kunyi carko carko badai harkun gama hutawan ba?” Momyn Husnah ta tambaya, domin dama daga wajen me Ι—inki suke shine suka biyo ta gidan su Husnah akan zasu Ι—an huta..

“Eh Momy wlhy kinga yanzu Doctor yaturo mana da kuΙ—i Banki zamuje mu cire” Husnah tafaΙ—i haka ga mamanta.

“Ummm zancenki dai baya wuce na kuΙ—i ako da yaushe,  wato shine Zahrah kika biyewa wannan mai idon kuΙ—in kuketa Ζ™waΖ™ule wa bawan Allah aljihun sa ko?”
Dariya Husnah da Zahrah suka sanya Ζ™warai maganar Momy’n tabasu dariya.

“Momy wllhy ba haka bane, shine ma yake turowa ko tambayansa ma bamuyi ba” Zahrah tafaΙ—i haka tana murmushi..

Murmushi kawai Momy tayi haΙ—e da cewa “Aekuwa kun dai haΙ—u da Ι—an arziΖ™i ne, amma angwayen yanzu ae basa ba da wani kuΙ—i me yawa,,,  ungo wannan saikiyi maleji ko” Momy tafaΙ—i haka tana me miΖ™owa Zahrah Ζ™atuwar ledan dake riΖ™e a hanunta..

Idanu Zahrah ta waro ganin irin girman ledan amma kuma Momy tana cewa wai tayi maleji…
Husnah ce tayi saurin karΙ“an ledan haΙ—e da soma fito da kayan ciki, wasu tsala tsalan laces ne guda uku masu kyau da tsadar gaske, sai kuma wasu haΙ—aΙ—Ι—un kuloli masu kyau har guda uku, kuloline irin wanda suka amsa sunansu kula wanda gidan masu da akwai suke amfani dasu, dagani kai kasan kulolin sunja naira.. DaΙ—ine yakama Zahrah har batasan sanda ta faΙ—a jikin Momy ta rungumeta ba, sai kuma ta saki kuka.

“Kuka kuma Zahrah? share hawayenki wannan ai ba wani abubane da zai sanyaki kuka ba, kamar Ι—iyata Husnah haka na Ι—aukeki, share hawayen kinji” Momy takare maganar cike da lallashi..   Godiya sosai Zahrah tayimawa Momy wanda bazai faΙ—uba, sosai kyautan momy’n yafaranta ranta domin kuwa kayane na alfarama daga kan laces Ι—in har zuwa kan kulolin….

Momy nafita Zahrah ta rungume Husnah cike da jin daΙ—i..
Murmushi Husnah tayi haΙ—e da cewa “Ƙawata yanzu ba lokacin godia bane, dare zai mana idan bamuje bank Ι—innan ba” dariya Zahrah tasanya, domin ita wani lokacin Husnah daria take bata, komai yinsa take a gaggauce gaba Ι—aya tafi kowa Ζ™osawa ayi auren…
Koda sukaje Bank basu wani shawahala ba suka cire kuΙ—in, daganan kuma gidan su Zahrah suka dawo,,,,  suna dawowa suka samu Inna tamusu Ι—an wake, aikuwa ba Ι“ata lokaci suka shiga loda mawa cikinsu.  suna gamawa kuwa Zahrah tashiga haΙ—a abubuwan buΖ™atanta domin gobe da sassafe zata je gidan Hajiya Shuwa bakuma zata dawoba sai 7 na dare, haka Ζ™a’idan gyaran nasu yake sam ba’aso rana yana dukanka, saboda zafin rana zai iya Ι“ata gyaran da suka soma batare da sun kammala ba……….Tun adaren tagama haΙ—a gaba ki Ι—aya abubuwan da zata buΖ™ata.  Kwanciya tayi lamo akan katifarta tana me sauΖ™e nannauyar ajiyar zuciya, tun safe sai yanzu tasamu hutu, kai gaskia hada hadan aure babu sauΖ™i, ace mutum yazama busy saikace wani engine, itama mace kenan inga Dr.Sadeeq kuma, wanda haΖ™Ζ™in raba kati da sauran abubuwa yake kansa…+

Ajiyar zuciya takuma sauΖ™ewa akaro na barkatai,   “Ζ™addara kenan mai sauya al’amura da yawa, kana naka kuma Allah na nasa, koda amafarkine bata taΙ“a tunanin wai wani zai lalata mata rayuwa ya rabata da budurcinta ba, amma cikin ikon Allah saigashi haka ta kasance, lallai babu mai iya ja da’ikon Allah, idan yaturoma Ζ™addara babu wanda ya’isa hana ta zuwa gareka, siraran hawayen da suka biyo takan Ζ™uncinta ta sanya hanu ta share haΙ—i da gyara kwanciyarta, tunani cike da zuciyarta haka bacci Ι“arawo yayi awun gaba da’ita.

Asibiti….

Idanunsa ya tsaida Ζ™yam akan ceiling  Ι—in daya mamaye saman Ι—akin, gaba Ι—aya hankali da nutsuwarsa basa garesa, zuciyarsa tayi nisa akan  soyayyarta ta yanda bayaji baya kuma gani, kamar  dai yanda yayi nisa yanzu wajen tunaninta,, a hankali ya sauΖ™e idanunsa daga kan ceiling Ι—in haΙ—e da dawo da kallonsa ga Ζ™afarsa na dama wacce take naΙ—e acikin bandage, sosai Ζ™afar takeyimasa raΙ—aΙ—i jiyake tamkar ana barbaΙ—amasa barkono aduk saΖ™o da lungu wanda  ke Ι—auke da ciwo, hakanan yake  bakowani irin ciwo ne idan yaji zaiji zafinsa ba hartakai ga zafin ya hanasa sukuni, amma  kuma saigashi zafin wannan ciwon yakan iya hanasa motsa Ζ™afarsa,    amma kuma duk da wannan tsananin zafi da ciwon nasa keyi masa ko kwatan kwacin rabin zafin da yakeji azuciyarsa game da soyayyar Zahrah baikaiba,  ada yaΙ—auka so Ζ™aryane, sai ayanzu yafuskanci cewa so gaskiya ne musamman ma irin nasa salon soyayya’r ….       Lumshe idanunsa yayi haΙ—e da Ι—an matse lips Ι—insa,  idanunsa na Ι—okin ganinta, yayinda kunnuwansa ke Ι—okin jin muyarta, sai dai kuma yana acikin hali wanda bazai iya zuwa gareta ba,, haka yayita saΖ™awa da kuncewa shi kaΙ—ai har bacci yayi gaba dashi.

Washe Gari……

Da sassafe Zahrah tayi wanka haΙ—e da shirya kanta cikin wani jan yadi me sauΖ™in kuΙ—i, amma kuma yayi mata kyau sosai ajikinta kasancewarta  me farar fata,,, wani Ι—an madai daicin mayafi wanda kalansa yakasance ja irin kalan kayan dake jikinta ta yafa, a Ζ™agauce tayi karyawanta, domin kuwa Hajiya Shuwa tace tazo da wuri, inda Allah yataimaketama  sun samu hutu a makaranta da badon hakaba ma da batasan yanda zatayi ba…

Wayarta da Ι—an Ζ™aramin hand bag Ι—inta ta Ι—auka haΙ—e dayiwa Inna sallama domin kuwa Baffa bayanan yatafi yola. Adawo lafiya Inna tayi mata, da “Ameen” ta amsa haΙ—e da sakai tafice daga cikin gidan..

Tafe take tana Ι—an latsa wayarta number’n Husnah take Ζ™oΖ™arin Ζ™ira don ta sanar mata cewa tanaso su haΙ—u agidan Hajiya Shuwa,,, batakai ga dialing number’n Husnah’n ba wata baΖ™ar mota ta faka adai dai gabanta, da sauri taΙ—ago idanunta takai dubanta ga motar haΙ—e da Ι—an matsawa baya, take zuciyarta tashiga yi mata lugude..

BuΙ—e murfin motar yayi yafito fuskarsa Ι—auke da murmushi..

STORY CONTINUES BELOW

Baki sake Zahrah take kallonsa cike da mamaki…

“Auntyna!”  kyakkyawan saurayinnan daya fito daga cikin mota yafaΙ—i haka ga Zahrah  yana murmushi..

Kallon tuhuma Zahrah tashiga yi masa haΙ—e da Ι—an sake ja  baya dashi,  batasanshiba bata kuma san waye shiba, amma kuma lokaci Ι—aya ta shiga yimawa fuskarsa kallon sani kamar akwai wani wanda tasani wanda wannan Ι—in kekama dashi.

“Uhh sorry my kyakkyawar auntie, na tsorataki ko? kiyi haΖ™uri nafiso inyi miki surprise ne, shiasa na hana bro yasanar dake zuwana”  yaΖ™are maganar still  yana murmushi ..

“Waye kai?” Zahrah ta tambayeshi cikin Ι—ar Ι—ar.

“Sunana Samad” saurayinnan yafaΙ—i haka yana me bayyana murmushi akan fuskarsa, da’alama dai shi mutum ne me yawan fari’a. 

Kallonsa tashigayi domin taΙ—an gano wani abu atattare dashi, tun bata kai ga cewa komai ba wayarta  tasoma Ζ™ara alaman shigowar Ζ™ira, kallonta ta maida kan wayarta ta,  ganin sunan Dr.Sadeeq na yawo akan screen Ι—in wayar yasanyata Ι—aga wayar haΙ—e da  Ι—an sake matsawa gefe. 

“Brother na yazo wajenki kuwa?”  abun da Dr.Sadeeq yatambaya kenan bayan ya amasa sallaman da tayi masa.

Kallonta tamayar ga Samad dake tsaye, tabbas sai yanzu tagano kamannin watake gani akan fuskar saurayin..

“Eh bansaniba ko shine a tsaye a gabana yanzu, amma wannan yacemin sunansa Samad” Zahrah tafaΙ—a cikin Ζ™asa Ζ™asa da murya, domin batason wancan Ι—in yaji..

“Yauwa shine, please my dear kishiga yakaiki gidan gyaran jiki’n kinji,  ni zanzo na Ι—aukoki idan kuka gama, daga yanzu harzuwa bayan aurenmu banaso kina shiga motocin haya” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka ga Zahrah cike da kulawa.

Mamakine yakama Zahrah sosai domin ita sam bata faΙ—a masa ma zata fara zuwa gyaran jiki ba, to a ina yasamu labari?” tambayar da bata da amsarta,, jin da tayi alamar cewa yakashe wayartasa ne yasanya itama tacire tata wayar daga kan kunnenta… Murmushi tasakarmawa Samad haΙ—e da Ζ™arasowa garesa..

“Matsoraciya da kin Ι—auka saceki zanyi ko?” Samad yatambaya cike da tsokana.

Dariya taΙ—anyi me sauti haΙ—e da cewa “sosaima kuwa”

Dakansa ya zagayo ya buΙ—e mata murfin motar yana me cewa “Ashe dai Bro matsoraciya yasamomana”

Dariya sukayi dukansu,,  zama tayi acikin motar  haΙ—e da Ι—aura hand bag Ι—inta akan cinyarta,, zagayawa wajen zaman driver Samad yayi haΙ—e da kunna motar suka hau titi..

A hankali Samad ke tuΖ™a motar yayinda yake ta yiwa Zahrah hira, mintuna kaΙ—an Zahrah ta sake dashi suka soma hira, saboda  tafahimci cewa shi ba irin mutanen nan bane masu zafin rai, ya nada sauΖ™i tamkar yayansa gashi fuskarsa bata rabo da murmushi, sai dai kuma fa Dr.Sadeeq yafisa kyau duk da kuwa cewa suna kama, kuma shi Ι—inma balaifi yana da nasa kyau’n..

A Ζ™ofar gidan Hajiya Shuwa Samad ya faka motar haΙ—e da kallon Zahrah cikin sigar tsokana yace   “Yauwa Malama nakawoki sai ki bani kuΙ—i na ko” 

Dariya Zahrah tayi harsaida haΖ™waranta suka bayyana.

  ” Kabini bashi yanzu banda kuΙ—i” tafaΙ—i haka tana me Ζ™oΖ™arin buΙ—e murfin motar.

“To shikenan inabinki bashi” Samad yafaΙ—i haka yana Ι—an dariya.  Itama dariyan tayi kana tafice daga cikin motar. Murmushi kawai Samad yayi haΙ—e dayin reverse ya cilla motarsa kan titi.

Zahrah kuwa tana shiga gidan ta iske Hajiya Shuwa zaune a falo tana karyawa, gaisawa sukayi da Hajiyan kana takoma gefe ta zauna… Hajiya Shuwa kuwa tana kammala yin breakfast, ta dafa wani ruwan wanka wanda yasha turaren Ζ™amshi na jiki haΙ—e da wasu surrukan Ζ™amshi na mussaman,   ceda  Zahrah  Hajiya Shuwa tayi, tashiga cikin ruwan ta kwanta dayake acikin bathtub ta haΙ—a ruwan wankan, babu musu Zahrah tacire kayanta haΙ—e da shiga cikin bathtub Ι—in ta kwanta luf,, ajiyar zuciya tashiga sauΖ™ewa akai akai domin kuwa Ζ™amshin  haΙ—aΙ—Ι—en turaren da’aka sanya acikin ruwan shikaΙ—ai ya’isa yasanya maka nutsuwar zuciya.. Saida Zahrah tayi 30 minute acikin wannan ruwan,  kafun Hajiya Shuwa tabata izinin fitowa, wani ruwan wankan kuma aka haΙ—a mata takumayi, tana fitowa kuwa Hajiya shuwa tasoma mulke mata jiki da wani haΙ—aΙ—Ι—iyar dilka me kyau wanda take Ι—auke da wasu irin sinadarai masu gyara jiki dasanya Ζ™arin laushin fata… Gaba Ι—aya dai wunin yau Zahrah tayishine ba kaya daga ida sai wani Ι—an towel  domin kuwa wannan na bushewa tana wankewa za’ace takuma shafa wancan, wasu irin haΙ—in magunguna masu kyau Hajiya Shuwa ta bata tasha wasu sunmata daΙ—i wasu kuwa bauri suka mata, amma yata iya tunda ita takawo kanta yazama dole ta jure…

STORY CONTINUES BELOW

A asibiti kuwa Zaid ne yakafe kai da fata akan cewa lallai shi sai ambasa sallama duk da kuwa cewa yanajin ciwo ajikinsa amma yakafe akan cewa shi bazai iya jure zaman asibiti’n ba.. Alhaji Ma’aruf ne yasamu Dr.Bilal akan maganar sallaman da Zaid ya buΖ™ata……

Gyara zama Dr.Bilal yayi haΙ—e da maida kallonsa ga Alhaji Ma’aruf  cikin sigar da Alhj Ma’aruf Ι—in zai fahimta yasoma cewa…

“A gaskia zamansa anan Ι—in zaifi akan komawarku  gida, har yanzu akwai tarin ciwuka a jikinsa yana da buΖ™atar kulawarmu sosai, saboda haka inaga babu amfanin baku sallama kamar yanda ya buΖ™ata, yakamata ne ace sainan da sati guda sannan zaku karΙ“i sallaman ku”

Ajiyar zuciya Dad ya sauΖ™e haΙ—i  da cewa

“Shikenan badamuwa Doctor amma kuma yamaganan ciwon nasa babu wani magani da zaku Ι—aurasa akai wanda zai sanya cutar tafita daga jikinsa kwata kwata?”

“Eh to akwai magunguna da dama, amma kuma dole shima sai yakiyaye saboda yawan shangiya dakuma tunanin da yakeyi sukaΙ—ai sun isa sanya ciwon nasa yaΖ™ara faΙ—aΙ—a,  inafata kuma zaku guji shiga Ι“acin ransa, saboda idan ransa ya Ι“aci zuciyartasa zatana bugawa da sauri wanda hakan kuma zai iya kawo wata matsala ta daban” Dr.Bilal yaΖ™are maganar yana  me Ζ™oΖ™arin cike wani file dake gabansa..

Ajiyar zuciya Alhj Ma’aruf yakuma sauΖ™ewa akaro na barkatai,, cike da jimami yamiΖ™e daga zaunen da yake haΙ—e da miΖ™awa Dr.Bilal  hanu suka kumayin musabaha,, har bakin fita office Ι—in Dr.Bilal yaraka Alhj Ma’aruf daga nan sukayi sallama…

A hankali yake gutsuran green colour apple  Ι—in dake riΖ™e ahanunsa, zuwa yanzu bayajin daΙ—in komai, sannan duk abun dayaci baijin test Ι—in abun acikin bakinsa, apple kaΙ—ai yake iyaci sai kuma roasted fish,  amma bayansu baya iya cin komai.. Idanu Mom tazura masa Ζ™warai zuwa yanzu kam tagama karantar yanayinshi, damuwa ce kurum tayi masa yawa kuma bazata taΙ“a iya jurar ganin Ι—anta acikin damuwa ba…

“Zaid” mum taΖ™ira sunanshi cikin murya me taushi.

Kansa yaΙ—ago ya kalli mahaifiyartasa batare da ya amsa Ζ™iran da tayi masa ba.

Matsowa kusa da shi tayi haΙ—e da  kama hanunsa cike da kulawa tace

  “Meke damunka ne Zaid? inaso yau kasanar dani duka damuwarka ni mahaifiyarkace Zaid baikamata ace ka Ι“oyemin damuwarka ba”

Ajiyar zuciya Zaid ya sauΖ™e  haΙ—e da sake kwantar da kansa ajikin pillow.       “Inasonta Mum!” abun da Zaid ya’iya faΙ—a kenan cikin murya me rauni.

Ajiyar zuciya Mum ta sauΖ™e haΙ—e da kallon Zaid Ι—in da kyau

“Nayi tunanin zuwa yanzu kamanta da maganar wannan yarinyar Zaid, ka daure zuciyarka ka nemi wata wanda ta dace dakai”

Kallon Mum Ι—innasa yayi da’idanunsa wanda suka sauya kala alokaci guda, shikaΙ—ai yasan me yakeji acikin zuciyarsa aduk sanda yaji wata kalma dake masa nuni da ya haΖ™ura da Zahrah, duk wanda yace masa ya haΖ™ura da Zahrah gani yake tamkar basonsa yake ba…

Wani irin murmushi me ciwo Zaid yayi haΙ—e da kama duka hannayen mahaifiyartasa yasanya acikin nasa hanun.

“Banajin zan’iya cigaba da zama babu ita akusa dani Mum, inasonta sosai, amma kuma ita tsanar da tayi mini haryafi soyayyar danakeyi mata yawa, ina buΖ™atar taimakon ki Mum!” gaba Ι—aya muryarsa ta bayyana rauninsa,, take Mum taji zuciyarta ta karye yayinda tausayin Ι—annata yasake dira acikin zuciyarta..

“Insha Allah zanyi iyaka Ζ™oΖ™arina Wajen ganin kasamu cikar burinka kaji Zaid, ka kwantar da hankalinka, banason damuwarka!”  Mum tafaΙ—i haka cike da lallashi saikace wani Ζ™aramin yaro haka tashiga lallaΙ“a Zaid, Allah sarki uwa me daΙ—i sai gashi harya Ι—anji sanyi acikin ransa……

****

Sai Ζ™arfe 7 na dare Zahrah tasamu kanta daga gyaran da takesha wajen Hajiya Shuwa, a Ζ™agauce tayi sallan isha haΙ—e da cin abincin da Hajiya Shuwa ta kawo mata domin kuwa tuni Dr.Sadeeq yayi mata waya akan cewa yana kofar gidan Hajiya Shuwa’n yana jiranta..

Ita kanta daΙ—i da nutsuwane suke sauΖ™ar mata idan tashaΖ™i daddaΙ—an Ζ™amshin turaren da ke tashi ajikinta, inakuma ga wani na daban idan yaji…

STORY CONTINUES BELOW

Tafiya take cikin nutsuwa hartaΖ™araso inda yake tsaye yajingina a jikin motarsa…

“Kayi haΖ™uri na shanya ka ko?” Zahrah tafaΙ—i haka tana me gyara zaman jakarta dake rataye akan  faΙ—arta.

” Girmankine ae Ζ΄an mata na” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka yana me Ζ™oΖ™arin buΙ—e mata murfin motar. Kyakkyawan murmushi tasakar masa haΙ—e da shiga cikin motar ta zauna,   zagayawa yayi shima yashiga haΙ—e da tada motar suka hau kan titi.

Saida sukayi nisa da tafiya kafun yadawo da kallonsa gareta …

“Da ruwan zinare aka wanke kine naga gaba Ι—aya kin Ζ™ara kyau sai walwali kike” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka yana me binta da wani irin kallon shauΖ™i…

Dariya ne yaso Ζ™wacema Zahrah amma saita basar haΙ—e da Ι—aga masa kai alamar “Eh”

Murmushi yayi kawai  haΙ—i da jefa watermelon sweet acikin bakinsa.  

Tafiya suke babu wanda yace da Ι—an’uwansa Ζ™ala harsuka iso Ζ™ofar gidansu Zahrah…

Yana parking Ι—in motar yadannawa kowacce Ζ™ofar fita daga cikin motar lock. Saurin Ι—ago da kai Zahrah tayi ta kallesa , murmushi yasakar mata haΙ—i  da kashe mata idanunsa Ι—aya,   Ι—an Ζ™aramin bakinta taturo gaba haΙ—e da marairaice fuska cike da shagwaΙ“a tace “Please bacci fa nakeji duk nagaji kabuΙ—emin na fita”

“NaΖ™i wayon, so nake mota ta ta gama Ι—aukar  daddaΙ—an Ζ™amshinki wanda yake shirin rabani da nutsuwata kafun saina buΙ—e miki”

Hanu tasanya ta toshe bakinta gudun kada sautin dariyar da takeyi ya fito.

“Au dariyama kikemin ko? to ae ba iya motata bace kaΙ—ai nakeso taΙ—auki Ζ™amshin hardani kaina, saboda haka bana matso kusa dake sai nasamu wannan daddaΙ—an kamshin”

Da sauri Zahrah ta matsa gefe hartana manna jikinta da murfin motar…. “Please kazauna to a inda kake, ae nataho da turaren zan baka saika shafa” cikin zallan shagwaΙ“a tayi maganar..

Dariya Dr.Sadeeq yayi haΙ—e da girgiza kansa “Zahrah akwai tsoro, shi da wasa yake mata ma” yafaΙ—i haka acikin zuciyarsa.

Amma afili saiyace  “A’a ni naΖ™i wayon najikinki nakeso”

Sake takurewa tayi haΙ—e da noΖ™e jikinta “Dan Allah Yaya Sadeeq kabari Allah zan tsammaka turaren saika shafa” gaba Ι—aya tarikice kamar wanda yace zaiyi mata wani abun..

Dariya kawai yayi haΙ—e da cewa “Nifa wasa nake miki Ζ΄an mata babu abun da zanmiki, kiyi bacci lafiya gobe ma Samad ne zaizo ya kaiki” yaΖ™are maganar yana me cire lock Ι—in daya sanyawa Ζ™ofofin motar, aikuwa da sauri tabuΙ—e murfin motar ta fice, hartana manta Ζ΄ar Ζ™aramar Hand Bag Ι—inta. Ko wai wayoshi batayi ba tashige cikin gida da sauri… Dariyane yakamasa sosai,  dubi yanda  tafirgice  masa alokaci Ι—aya, lallai idan har haka take akwai aiki ja agabansa.

Da wannan tunanin yaΙ—auki hanyar komawa gida, bayan daddaΙ—an Ζ™amshin turarenta yagama kashemasa jiki yasanyashi jin wani irin shauΖ™i na musamman……

Zahrah kuwa tana shiga gida ta turo Ζ™ofar gidan  haΙ—i da sanyawa Ζ™ofar sakata,  direct Ι—akin Inna ta wuce can ta  sameta tana aikinta najin radio.  Kwanciya tayi akan wata doguwar kujera dake Ι—akin Inna’n, mintuna kaΙ—an baccin gajiya yayi  gaba da’ita…….

Dr.Sadeeq ne kwance akan makeken gadonsa  yayinda idanunsa ke kallon sama, amma azahirin gaskia idanunsa bawai sama suke nuna masa ba,   kyakkyawar fuskar Zahrah kawai suke hango masa, Ζ™warai matuΖ™a shi kam Allah yasani ko gobe da za’a Ι—aura aurensa da Zahrah yanaso, saboda  yana matuΖ™ar buΖ™atarta akusa dashi, sosai yakejin abubuwa dayawa agame da’ita wanda baicika jinsu akan sauran mata ba,  shidai yabarwa kansa cewa Zahrah ta musammance ko acikin Ζ™asaitattun mata kuwa samun kamarta sai an dage,  hand bag Ι—inta dake aje kan Ι—an Ζ™aramin drower’n dake kusa da gadonsa ya jawo haΙ—i da kai hand bag Ι—in kusa da hancinsa…. lumshe idanunsa yayi haΙ—e da sauΖ™e nannauyar ajiyar zuciya, sosai Ζ™amshin yayi masa daΙ—i irin Ζ™amshin jikinta hand bag Ι—innata ma keyi,  lallai shikam Ζ™amshin yayi masa daΙ—i sosai,  baiΖ™i ace ma ya kwana yana shaΖ™an daddaΙ—an Ζ™amshin ba, haka dai yayita tunani kala kala yana riΖ™e da hand bag Ι—innata bacci Ι“arawo yayi gaba dashi……

STORY CONTINUES BELOW

Zaid kuwa kwana yayi yana mafarkan Zahrah saidai kuma sam mafarkan basuyi masa daΙ—i ba,  saboda acikin mafarkin sam babu alamar zata zamo tasa, saima gudunsa dayaga tanayi, duk da cewa yasan harzuwa yanzu Zahrah tana sonsa amma kuma baiga alamar cewa zata saurara masa ba, amma shi awajensa duk wannan ba abun damuwa bane matuΖ™ar Zahrah zata amince ta auresa to shikuma zaiyi iyaka Ζ™oΖ™arinsa wajen ganin yamantar da’ita tsanarsa da tayi dakuma tarin laifukan daya aikata a gareta…..

****

Ahankali tagama ware idanunta akan robber ceiling Ι—in  daya mamaye duka saman Ι—akin  na Inna,, wani irin ajiyar zuciya ta sauΖ™e haΙ—i  da rumtse idanunta,,,  yau shine kwana na biyu kenan da Zaid yake zuwa mata  acikin mafarkinta, sai dai kuma ba’ahalin daΙ—i yake zuwa mata ba, sosai take ganin damuwa Ι—auke akan fuskarsa,  amma kuma sam batasamun daman yi masa magana acikin mafarkin nata,  duk da kuwa yanda take matuΖ™ar son faΙ—a masa wani abu, amma dazaran tabuΙ—i bakinta zatai masa magana saitaji harshenta yayi mata nauyi takasa cewa dashi komai,,, wannan shine babban abun dake damunta, ita kanta batasan me takeson faΙ—a masa ba…   Da Ζ™yar ta’iya tashi daga kan kujeran takoma nata Ι—akin bayan taΙ—auro alwalan sallan asuba.. tana idar da sallah’n asuba Ι—in ta Ι—auko Al’QUR’ANI  ta tasoma karantawa.   Ba’ita ta idar da karatun ba sai Ζ™arfe 7 na safe,  wanka tayi haΙ—e da shirya kanta cikin wani baΖ™ar abaya, ita kanta tasan tayi kyau, gashi rana Ι—aya kawai da soma gyaran jikin nata amma har  fatarta  ta murje tayi kyau… Yauma dai aΖ™ofar gidansu ta’iske Samad yana jiranta,,, haka suka tafi suna hira gwanin ban sha’awa, Samad yana da saurin sabo daga jiya zuwa yau harsun saba sosai…. Yauma dai gangariyan gyara tasamu daga Hajiya Shuwa, Ζ™amshi kawai jikinta ke fitarwa….

Agurguje.

Bayan sati Ι—aya….

Sosai Zahrah ta samu sanji ajikinta daga fara gyran jikin nata zuwa yanzu, wani irin walwali da sheΖ™i fatarta keyi gashi lokaci Ι—aya taΖ™ara haske komai nata yaΖ™ara zama abun burgewa dakuma sha’awa,, sai dai yanzu kwata kwata bata da wadataccen lokaci  saboda agidan Hajiya Shuwa take wuni, Husnah kuwa tuni ita da Doctor sun  gama tsara duk wani tsare tsaren su, duk da Zahrah tace bazatayi wani program ba, amma Husnah takafe kai da fata akan cewa sai sunyi shagali ko babu yawa ne ma, saboda haka tuni ta zayyana mawa Dr.Sadeeq cewa  ranar Laraba za’agudanar da tsantsarerren kamu wanda za ayi shi a wani babban katafaren Hall dake cikin garin abuja, ranar jumma’a kuwa zasu yi Ζ™ayataccen walima domin ranar asabar ne Ι—aurin auren, asabar Ι—in da dare kuma za’ayi diner…  Dr.Sadeeq baiji Ι—ar ba   haka yasakarmawa Husnah kuΙ—i  yace tayi duk wani abun daya dace…    anko kala uku Husnah ta fitar  kowani program da za’ayi da anko Ι—insa, ita dai Zahrah bata da tacewa, tasakar mawa Husnah komai…

MiΖ™ewa tsaye yayi  daga zaunen dayake haΙ—e da soma taka Ζ™afarsa wanda take Ι—auke da ciwo cikin nutsuwa.  Ahankali yake takawa yana me rumtse idanunsa da’alama dai yanajin zafin ciwon… Dai dai yakusa isa Ζ™ofar fita daga Ι—akinne Dr.Bilal yaturo Ζ™ofar Ι—akin yashigo..

“Ka kasa hakuri ko?” Dr.Bilal yatambayi Zaid cike da kulawa.

Ɓata fuska Zaid yayi haΙ—e da sanya hanunsa yadafa jikin bango gudun kada ya faΙ—i

  “Ina fata kataho da takardan sallama na?” abun da yafito daga bakin Zaid kenan cike da zaΖ™uwa..

Murmushi Dr.Bilal yayi haΙ—e da jinjina kansa baisan wani irin dalili ne yasanya Zaid keson barin asibitin batare da ya tsaya yaji sauΖ™i ba, kofa tafiya me nisa baya iyawa, amma kuma gaba Ι—aya yatashi hankalinsa  akan sai anbasa sallama.. 

“Kwantar da hankalinka Zaid yanzuma nazo ne nataimaka maka domin su Dad Ι—inka suna jiranka a waje yau kwanan gida zakayi”  Sai alokacin Zaid ya’iya sake ransa, sakamakon jin dayayi cewa kwanan asibitiya Ζ™are masa…

Da taimakon Dr.Bilal Zaid ya iya takawa harzuwa inda motar su Dad ke jiransa..  A gidan baya ya zauna haΙ—e da kwantar da kansa ajikin kujera,  bakomai ne ya sanya sa matsawa da sai an sallamesa ba face marari’n da idanunsa keyi masa nasan kallon fuskar Zahrah, ya Ζ™osa matuΖ™a yasanyata acikin idanunsa… Harsuka isa gida Zaid tunanin Zahrah yakeyi..  

Yana shiga Ι“angarensa ya faΙ—a bathroom  haΙ—e da  sakarmawa kansa ruwa,  yajima tsaye agaban shower ruwa na dukansa kafun daga bisani ya yi wanka…  sharp sharp ya shafa mai ajikinsa haΙ—e da feshe jikinsa da turaruka masu daΙ—in Ζ™amshi.  3 guater combat jeans yasanya wanda yatsaya masa iyaka guiwarsa, kasancewar kalan wandon nasa baΖ™ine yasanya rigar polo shirt Ι—in dake jikinsa  takasance fara Ζ™al.   Sosai yayi kyau duk da kuwa cewa rama ta bayyana ajikinsa sai dai kuma hakan bai sanya faffaΙ—an surar jikinsa komawa ba..

Ahankali yakejan Ζ™afar tasa har ya iso compound Ι—in gidan nasu, driver na ganinsa ya kwaso aguje haΙ—e da Ζ™arasowa wajen Zaid Ι—in da sauri,,,    “Barka da fitowa ranka ya daΙ—e, fita zamuyi ne?”  driver yatambaya cike da girmamawa.

Kai kawai Zaid ya’iya gyaΙ—a masa, aikuwa ba Ι“ata lokaci Driver yafiddo da wata farar range rover  daga cikin parking space, yazo ya faka adai dai inda Zaid ke tsaye…  A daddafe haka Zaid ya buΙ—e murfin motar yashiga yayinda driver yayiwa motar key suka bar cikin gidan…    Bayan sun hau kan hanyane Zaid yafaΙ—ama driver’n inda yakeso ya kaisa….. Kamar yanda Zaid ya faΙ—amasa inda zai kaisa, bai Ζ™araba bai kuma rageba, adai dai Ζ™ofar gidan yatsaya da motar cak..   Cike da halin isa Zaid yace da driver’n ya sauΖ™a yanemamasa yaro,, babu musu kuwa driver yabuΙ—e murfin motar yafita, wani yaro yagani da’alama aika zashi,  baiyi wata wata ba ya Ζ™ira yaron,  yaron kuwa bawani nuΖ™u nuΖ™u yaΖ™araso wajen da motar take tsaye… Cike da girmamawa driver’n yace “Oga ga yaro nasamu” sauΖ™e glass Ι—in motar Zaid yayi haΙ—e da kallon yaron.  Nuni Zaid yayi masa da gidansu Zahrah yace yaje yace ana kiranta… Mintuna kaΙ—an yaron yafito daga gidansu Zahrah haΙ—e da sanarmawa Zaid cewa ance batanan..  Har yaron yatafi Zaid bai iyacewa komai ba, wani iri yaji acikin zuciyarsa baiso ace masa batanan ba, amma yazaiyi dole zaije yaΖ™ara dawowa….

Tundaga wannan ranar kusan kullum Sai Zaid yazo gidansu Zahrah amma maganar Ι—ayane  batanan, gaba Ι—aya kansa ya kulle yashiga damuwar rashin ganinta sosai,  tabbas yana da buΖ™atar sanin inda take zuwa,   watarana  idan akace masa batanan haka zaizauna zaman jiranta amma kuma harya Ζ™araci zamansa yatafi  koda me kamanninta  ne bai gani ba….

Shirye shiryen aure yasake kankama, hakan yasanya amarya da ango suka shiga busy,  koda yaushe Zahrah  tana gidan Hajiya Shuwa, wasu abubuwa na hidiman bikin ma  Husnah Zahrah ta barwa, saboda ita  bata da wani ishashshen lokaci,,, Ɓangaren Dr.Sadeeq ma dai yanda  Zahrah tazama busy haka shima ya shiga busy hidima sosai  yakeyi,  hakan yasa ko haΙ—uwa da junansu basayi sai dai suyi waya wannan ma bako da yaushe ba.  Yanzu Samad ne ke Ι—awainiyar kaita duk inda zataje shike kuma Ι—aukota….

Yau Aurensu yakasance saura sati guda kenan ita da Dr.   Tafe take tana zuba sauri burinta Ι—aya shine tasamu abun hawa wanda zai kaita gida, saboda  yau Samad yabata excuse akan cewa bazai samu daman zuwa Ι—aukota ba…  Ƙarfe bakwai da rabi na daren yau kenan, yau ta makara sosai wajen dawowa gida,  atsorace take matuΖ™a saboda  gaba Ι—aya arean unguwar su Hajiya Shuwa’n yaΙ—auki shiru…  Tafe take ta sunkuyar da kanta Ζ™asa, bata ankara ba saijinta tayi tayi karo da mutum, da sauri ta matsa baya haΙ—e da sanya hanu ta dafe goshinta… Kallonta ta mayar ga mutumin da tayi karo dashi…  take ta Ζ™ara ware manya manyan idanunta,  sakamakon ganin wanda ke tsaye a gabanta da tayi,, sosai gabanta yatsananta faΙ—uwa yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da sauri sauri…

Wani irin Ζ™ayattacen murmushi yasakar mata wanda ya bayyana asalin kyawunsa, haΙ—e da buΙ—e duka hannayensa alamar ta taho garesa…….

Kyakkyawan murmushinsa ne Ι—auke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.+

Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me Ζ™arfi, haΙ—e da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma  sai yaji saΙ“anin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi,  sai gani yayi ta raΙ“a ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba.      Cikin hanzari yasha gabanta haΙ—e da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haΙ—i da rumtse idanunta,,  a hankali ya zame guiwowinsa Ζ™asa, ya durΖ™usa mata,  duka hannayenta ya kama ya riΖ™e acikin nasa hanun….

Cikin murya me Ι—auke da matuΖ™ar rauni yace da’ita…… “Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki  ba, dan Allah  inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani,  haΖ™iΖ™a nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haΖ™uri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alΖ™awari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me Ι—orewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba,  inasonki Zahrah so irin wanda bantaΙ“a yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuΖ™ar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah  hakan kaΙ—ai ya’isa bayyana miki irin tsananin Ζ™aunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!..” gaba Ι—aya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana…  A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuΙ—e famfo sannan  kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda  harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun.   Bazatace yaushene ko kuma tayayane  itama ta tsinci kanta  da zamewa Ζ™asa ba, ta dai tsinci kanta  da kafa guiwowinta a Ζ™asa.  kukane  yaci Ζ™arfinta  bazata kuma iya cewa ga abu Ι—aya dake damunta ba…    Hanunta tashiga Ζ™oΖ™arin cirewa daga cikin nasa hanun, amma kwata kwata Zaid yaΖ™i bata daman hakan saima Ζ™ara matsowa kusa da’ita da yakeyi… 1

“Zahrah!”  yaΖ™ira sunanta cikin wata irin murya da bata fita sosai…

Manyan manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta Ι—ago haΙ—e da  waresu akansa,  batare da tace dashi komai ba,, wani irin kallo yakeyi mata wanda yake Ι—auke da tarin ma’anoni masu yawan gaske..  Hanunta dake cikin nasa hanun  ya shiga murzawa  haΙ—e da langwaΙ“ar da  kansa gefe yana me cigaba da kallon fuskarta.   Hawayene yaziraro daga cikin idanun ta zuwa kan Ζ™uncinta,  sam bata taΙ“ayin zato ko tsammani ba, saijin sauΖ™ar bakinsa tayi akan Ζ™uncinta, yayinda yasanya harshensa yana me lashe ruwan hawayen  dake gudu akan Ζ™uncin nata.  wani irin bugawa zuciyar Zahrah tashigayi da sauri, yayinda numfashinta keshirin Ζ™wace mata batare da tashiryawa hakan ba,,  cikin Ι—an kuzarin daya rage mata tayi saurin tureshi gefe  haΙ—i  da miΖ™ewa tsaye, Ζ™oΖ™arin kama hanunta  yakuma yi amma saidai baisamu daman hakan ba domin kuwa tuni harta fara tafiya.     “Zahrah”   yakuma Ζ™iran sunanta amma sai dai ko waiwayosa batayiba balle yasaran zata amsa masa..    Jefa Ζ™afarta kawai take batare dako da ganin gabanta tanayiba, gaba Ι—aya Ζ™walla suncika mata idanu,  yayinda Ζ™irjinta ke mata luguden duka kanta kuwa tamkar anΙ—aura mata gungumen ice haka takeji yamata nauyi…2

STORY CONTINUES BELOW

Cikin Hanzari Zaid yarufa mata baya, yana me Ζ™iran sunanta amma kuma bata amsa masaba, haka kuma bata tsayaba, dai  dai lokacin wani me taxi yazo wucewa da sauri Zahrah taΙ—aga masa hanu, aikuwa take yatsaya,, ganin haka yasanya Zaid yaΖ™ara sauri don yaga alamar tafiya zatayi batare da ta tsaya ta sauraresa ba,, amma ina yamakaro domin mai taxi Ι—in yana tsayawa Zahrah    ta buΙ—e murfin motar tashige haΙ—e da cewa mai taxi Ι—in yatada motar sutafi..    Zaid na Ζ™arasowa wajen, me taxi Ι—in kuma na figar motar ya cillata kan titi.. Wani irin iska me zafi Zaid ya fesar daga cikin bakinsa, sam baiso haka ba, yaso ace yaji koda kalma Ι—ayane daga bakinta, amma kuma duk da haka yamatuΖ™ar jin daΙ—in ganinta, gashi kuma har kusa da’ita yasamu yazo, babban abun farincikin kuma shine har numfashinta ya shaΖ™a. Take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi, yayinda daΙ—i da kuma nutsuwa suka cika masa ruhinsa.. Cike da farinciki haka yakoma  inda yabar motarsa…..

Zahrah kuwa ko acikin taxi hawayenta kasa tsagaitawa sukayi, saima kara tuttulowa da suke tamkar ana hankaΙ—osu…   Ahaka har mai taxi Ι—in yakawota Ζ™ofar gidansu. KuΙ—insa tabasa ko canji bata tsaya karΙ“a ba ta wuce cikin gida.. A zauren gidan nasu ta tsaya haΙ—e da sanya hanu ta share hawayenta, sam bataso kowa yasan halin da take ciki, ta barwa Allah dakuma zuciyarta…

Tana shiga cikin gida Inna tayo wajenta da sauri 

“A’ina kika tsayane Zahrah? gaba Ι—aya duk kinsa hankalinmu yatashi, munsan bakya kaiwa iwar haka baki dawo ba”  Inna tafaΙ—i haka tana me Ζ™aremawa yanayin Zahrah’n kallo.

“Bansamu abun hawa bane Inna, yau Samad yana da wani uzuri shi yasa baisamu daman Ι—aukoni ba” Zahrah tafaΙ—i haka tana me Ζ™waΖ™ulo murmushi ta aza akan fuskarta..

Da kallon tuhuma  Inna tabi ta harta shige cikin Ι—akinta, tana shiga cikin Ι—akin ta dannawa Ζ™ofarta sakata, a hankali tazame  Ζ™asa  haΙ—e da jingina bayanta da Ζ™ofar, kana ta cusa kanta cikin cinyoyinta, wani irin kuka tashiga rerawa me tsananin bantausayi,   Yazatayi da rayuwarta ne itakam, da badon kada tayi saΙ“o ba da sai tace  wannan Ζ™addaran nata yayi mata girma dayawa, amma sai dai kuma ba’aja da ikon Allah, haΖ™iΖ™a tayi imani cewa komai zaizo yawuce, domin kuwa komai yayi farko yana da Ζ™arshe, amma kuma sai dai tana da yaΖ™inin cewa kafun  nan wataΖ™ila zuciyarta tayi  bindiga ta tarwatse,,   “yazatayi da abun da takeji acikin zuciyarta?” tambayar da kullum saitayi mawa kanta kenan, amma kuma zancen Ι—ayane shine bata da amsar da zata bawa kanta..  Tana cikin kukan taji wayarta na Ζ™ara, amma ko Ι—ago kanta batayiba haka wayar  taΖ™araci tsuwanta har Ζ™iran ya katse, wani Ζ™iran ne yakuma shigowa  still har wayar ta katse batako  Ι—aga ido ta duba taga waye yake Ζ™iranta ba..  Kuka tayi sosai kafun tatashi daga durΖ™ushen da take takoma kan katifarta,,,, kwanciya tayi luf tana me sauΖ™e ajiyar zuciya akai akai, yayinda tsikar jikinta ke yawanta tashi, idan tatuno kusancin da suka samu Ι—azu ita da Zaid,  bakomai ke dagula mata lissafi da kuma hautsina mata Ζ™waΖ™walwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa Ι“acewa daga cikin idanunta,,,  batasan me Zaid yakeso a tattare da’ita ba,  wataΖ™ila rayuwarta yakeso, wataΖ™ila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi  aduk sanda taΙ—aura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buΖ™atar samun wani wanda zata faΙ—awa gaba Ι—aya damuwarta, tana da buΖ™atar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buΖ™atar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauΖ™i da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi…..

Zaid ne kwance akan  wata haΙ—Ι—Ι—iyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka Ζ™awatasa da kayan Ζ™yale Ζ™yale dakuma more rayuwa.    Murmushine Ι—auke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauΖ™i me tsanani yakeji a tattare dashi,  a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba Ι—aya damuwarsa ne,   idanunsa yasake lumshewa haΙ—e da  sake shaΖ™an daddaΙ—an Ζ™amshin da yakeyi masa yawo acikin hanci,  Ζ™amshin da tun Ι—azu yakasa barin  hancinsa, “wani irin daddaΙ—an Ζ™amshine haka Zahrah’nsa keyi?”  ya tambayi kansa,,  tabbas zai so ace  iyanzu Zahrah na kusa dashi,  dakuwa kwana zaiyi manne da’ita yana shaΖ™an wannan daddaΙ—an Ζ™amshin nata,  sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha’awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,,   a hankali yasanya harshensa ya lashi laΙ“Ι“ansa haΙ—e da sanya hanu yashafi  Ζ™wantaccen beard Ι—in sa wanda koda yaushe yake Ζ™ara Ζ™awata masa fuskarsa,,    a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauΖ™ar maka da kasala…  Laptop Ι—in dake kusa dashi ya Ι—auka, haΙ—e da buΙ—ewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop Ι—in,, murmushi yayi haΙ—i da sanya hanu yashafi kan screen Ι—in laptop Ι—in..

STORY CONTINUES BELOW

“Inasonki Zahrah!” 

ya faΙ—i haka cikin wata irin murya me Ι—auke da matsanancin shauΖ™i.  Take yaji yana matuΖ™ar sha’awan kallon vedion dayayi mata Ι—azu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa.   Wayarsa da vedion ke ciki ya Ι—auka haΙ—e da kunnawa,  kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma  kuma kwata kwata saΖ™onnin da suke shigowa ta Email Ι—insa sun hanasa sakat..   Kai tsaye fita daga Ι“angaren vedion yayi ya kutsa cikin Email Ι—in nasa,  saΖ™onnin abokanan business Ι—insa ne, sama sama yakaranta saΖ™onnin, haryana shirin fita daga cikin Email Ι—in sai kuma idanunsa suka sauΖ™a akan    saΖ™on  Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaΙ—an faΙ—i saboda  yasan duk saΖ™on da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,,   buΙ—e saΖ™on yayi haΙ—e da Ζ™urawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu..  Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maΖ™oshi, yayinda idanunsa suka kaΙ—a sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiΖ™e,   wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin Ι—aurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba Ζ™arya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaΙ“e ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin Ζ™ara Zaid yayi haΙ—e da yin cilli da  wayartasa, take ta bugi bango  takuma faΙ—owa Ζ™asa lokaci Ι—aya ta tarwatse.. Cikin matsanancin Ι“acin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin  zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci Ι—aya wani irin tari  ya tasomai,  take yasoma tari babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taΙ“a gani ba arayuwarsa,,  da Ζ™yar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka Ζ™irjinsa bai daina yi masa Ζ™una ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haΙ—e da rumtse jajayen idanunsa,    numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuΖ™ar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa  haka ya daddafa zuwa cikin Ι—akinsa,  Ζ™aramin drower’n dake gefen gadonsa ya jawo haΙ—e da ciro magungunansa,  tsabar Ι—acin da yakeji a maΖ™oshin sa da Ζ™yar ma ya iya haΙ—iye magungunan… Kwanciya yayi  akan gado haΙ—i da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba,  baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba… Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba Ζ™afun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba……

*****

Zahrah kuwa yau  da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi,  gaba Ι—aya  idanunta sunyi luhu luhu dasu,  da gani kai kasan cewa kuka tasha ta Ζ™oshi. 

Yau ya kasance  aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana Ζ™irgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba Ι—aya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq Ι—in ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata Ι—inkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baΖ™on al’amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya.     Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba  tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je Ι—in zaifiye mata…    Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda  tasan cewa yanzu haka Samad na Ζ™ofar gida yana jiranta… ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a Ζ™ofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haΙ—e da Ζ™arasawa wajen motar…  “Allah sarki Samad yana da haΖ™urin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya Ζ™irata a waya” tafaΙ—i haka a zuciyarta dai dai sanda taΖ™araso gaf da motar, buΙ—e murfin motar tayi tashiga bakinta Ι—auke da sallama,  “Kayi haΖ™uri Samad nabarka kana ta jira”  tafaΙ—i haka tana me Ζ™oΖ™arin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad Ι—in ke zaune ba.

Tana rufe murfin motar   tadawo da kallonta wajen zaman driver  fuskarta Ι—auke da murmushi,,   a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da’alama dai ganinsa yabata mamaki sosai…10

STORY CONTINUES BELOW

 Murmushinsa me kyau yayi mata haΙ—e da kafeta da idanunsa wanda suke sauΖ™ar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta..      Itama murmushin tayi masa haΙ—e da shagwaΙ“e fuska….

“Ni dai nayi fushi!”  tafaΙ—i haka a shagwaΙ“e…     2

“Tuba nake”

Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa..   alaman ban haΖ™uri.

  “Ni dai naΖ™i wayon”  tafaΙ—i haka  tana me kaΙ—a idanunta..     Murmushi yayimata haΙ—e da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun,  lumshe idanunsa yayi alokaci guda haΙ—e da buΙ—ewa

“Nayi kewarki sosai Zahrah na!” yafaΙ—i haka cikin wata murya me sanyi. 

Ɗan guntun murmushi tayi haΙ—e da soma Ζ™oΖ™arin janye hanunta  daga cikin nasa  hanun, amma kuma  bata samu daman hakan ba.    “Meyasa jiya kika Ζ™i Ι—aga wayana?”  yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki.     Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga  missed calls Ι—insa, sanann kuma bata bi bayaba,, Ζ™aΖ™alo murmushi tayi haΙ—e da cewa ” Kayi haΖ™uri nayi bacci ne alokacin” 

Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faΙ—a ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi.    Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo Ι—aya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka,  dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa… Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauΖ™e ajiyar zuciya Ζ΄aΙ—e da kifa kansa akan steering motar,    “meke damun Zahrah ne?”   ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa….    A jiyar zuciya yakuma sauΖ™ewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar Ζ™ofar gidan……. Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu Ζ™arfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta  wanda kai tsaye za’a iya Ζ™iransa da suna sha’awa,  ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala  ma baya daΙ—ewa ajikinta yake karyewa  saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma Ι—aya daga cikin aikin magungunan Ζ™arin ni’iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haΙ—i me matuΖ™ar kyau…… (su Doctor za’asha nice??)

Tunda bacci ya Ι—aukeshi da asuba bashi yafarka ba sai Ζ™arfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaΙ“i yatashi, wanda ya zamana ko Ι—aga kansa ba ya’iyawa  hatta numfashima da Ζ™yar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin  ne yaji anturo Ζ™ofar Ι—akin nasa, bai iya Ι—ago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin Ι—akin…   Dasauri Alhj Ma’aruf   yaΖ™araso garesa…

“Lafiya Zaid meke damunka?” Alhaji Ma’aruf yafaΙ—i haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid Ι—in domin kuwa jiyayi jikin Zaid Ι—in yaΙ—au zafi rau kamar wuta.   “Subahanallah, bana Ζ™ira Doctor yanzu” Dad yafaΙ—i haka yana me Ζ™oΖ™arin ciro wayarsa daga cikin aljihu,,   bugu biyu Dr.Bilal yaΙ—auki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa.. 

Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid Ι—in,  gaba Ι—aya yarasa mekeyi masa daΙ—i, sosai matuΖ™a cutar Zaid ke damunsa, yana matuΖ™ar Ζ™aunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid Ι—in yana Ι—auke da ciwon zuciya me tsanani… Mintuna kaΙ—an Dr.Bilal yaΖ™araso gidan, babu wani Ι“ata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu Ζ΄an gwaje gwaje,  drip  yaΙ—aura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaΙ“i da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci,  saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taΙ“a barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike Ζ™ara sawa ciwon yayi tsanani…    Bayan sun fito compound Ι—in gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haΙ—e da  duban Alhaji ma’aruf,, bayani  yashiga yimawa Alhaji Ma’aruf Ι—in sosai agame da ciwon Zaid Ι—in.   Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma’aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake Ι—aukansa……

STORY CONTINUES BELOW

*****

Rana bata Ζ™arya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike Ζ΄an uwan Inna sun tattaro Ζ™wansu da Ζ™warΖ™watansu sun garzayo, don haka tuni gida yaΙ—auki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take Ζ™unshe a Ι—aki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen Ι—ebe mata kewa ta hanyar zama da’ita…..

Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya Ι—inke da mutane, ciki kuwa hadda Ζ΄an matan school Ι—insu  wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu Ζ™awaye Husnah ce kaΙ—ai Ζ™awarta…  Kowacce ka kalla acikin Ζ΄an matan nan  tasha kyau cikin kayan anko Ι—inta.    Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman Ι“aΙ“atu akan cewa Zahrah’n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds Ι—insa waΖ΄anda zasu kaisu shagon yin meckup Ι—in suna ma jiransu aΖ™ofar gida,,  ita dai Zahrah yau jitayi gaba Ι—aya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta.  Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta Ι—aukar mata haΙ—e da kama hanunta suka fice daga cikin gidan.  Wasu haΙ—aΙ—Ι—un motoci suka shiga  kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup….    

Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup Ι—innan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci Ι—aya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita Ι—in ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi,    kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau..    Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take  kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan,  sosai Ι—inkin yayi kyau yakuma amshi jikinta,  zama tayi aka tsantsara mata  haΙ—aΙ—Ι—en Ι—aurin Ι—ankwali akanta, yayinda  aka nannaΙ—e mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata,   daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma Ι—an karamin fos Ι—in dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones Ι—in kayanta suka kasance farare,   lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haΙ—e da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga Ι—aukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka Ζ™araso don Ι—aukar Ζ™awayen amarya,, duka Ζ΄an matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaΙ—ai saboda Ango yace shi dakansa  zaizo yaΙ—auki amaryarsa…   Ζ˜awaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma Ζ™ara,, murmushi tayi haΙ—e da kallon Zahrah adai dai lokacin da taΙ—aga wayar takara akan kunenta,    “To ranka shi daΙ—e gamunan fitowa” abun da Husnah tafaΙ—a kenan haΙ—e da miΖ™ewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haΙ—e da miΖ™ar da’ita tsaye..

“Angonki yaΖ™araso yace nafito masa dake”  murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta Ζ™asa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan Ζ™asa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaΙ—an Ζ™amshin turare,,  gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau Ι—in..

Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuΖ™ar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili….. Har Husnah ta buΙ—e murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai Ι—auke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta,  kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe Ζ™awatuwa..   A hankali ya sauΖ™e wata irin ajiyar zuciya haΙ—e da lumshe idanunsa,,,  Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta Ζ™asa tana me wasa da yatsun hanunta,,    Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin… 

“Zahrah!” Dr.Sadeeq yaΖ™ira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauΖ™ar da nutsuwa.    Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluΙ“eta.  

   

“Kinyi matuΖ™ar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa’a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!”

Sai alokacin Zahrah ta Ι—ago kanta, haΙ—e da sakar masa Ζ™awataccen murmushi,  jiyayi gaba Ι—aya ta kashesa  da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da’ita haΙ—e da kamo hannayenta duka biyu ya riΖ™esu gam acikin nasa,  wani irin soyayyartane yaji yana Ζ™ara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai  sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa….  Harsuka iso katafaren hall Ι—in daya cika maΖ™il da jama’a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai Ι—auke idanunsa akan abar Ζ™aunarsa ba, wani abun daya Ζ™ara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi…   Motarsu na’isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun Ζ™araso, take guri yasake Ι—aukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waΖ΄anda suka zo wajen dan gulma suka sake miΖ™a wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan Ζ΄ar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu Ζ™warΖ™wata….   Habeeb ne ya buΙ—ewa Dr.Sadeeq Ζ™ofar motar yafito,  yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buΙ—e mawa Zahrah  nata Ζ™ofar,,, cikin nutsuwa ta zuro Ζ™afafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta Ι—aya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,,  wajene yaΙ—auki shewa masu murna nayi masu baΖ™inciki ma sunayi, haka masu Ι—aukar amarya da ango hoto da vedio’s ma duk sunayi,,  gaba Ι—aya family’n Dr.Sadeeq Ζ™amewa sukayi Ζ™am  ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taΙ“a tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da’ita amma kuma sai suka ga saΙ“anin tunaninsu, lallai ba’abanza ba Dr.Sadeeq ya liΖ™e akan cewa  shi dole sai’ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma…  Har amarya da ango suka Ζ™arasa mazauninsu  mutane basu daina yimusu vedio’s ba, haka kuma idanu bai Ι—auke daga kan suba………Sunkuyar dakai Ζ™asa Zahrah tayi  gaba Ι—aya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taΙ“a shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron,   ba abun dake damunta kamar yanda idan taΙ—aga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waΖ΄anda suka santa haddama waΖ΄anda basu santa ba,,    matso da kansa yayi kusa da’ita haΙ—e da kawo bakinsa wajen kunnenta  “Anan ma kunya zaki nuna?” Ζ™asa Ζ™asa yayi maganar.    satan kallonsa tayi haΙ—e da Ι—an sakin murmushi  amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da Ι—auka yayinda….. Hmmmm kamu dai yayi kamu  yakuma Ζ™awatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a Ι—ari Ι—ari takeyinsa,  abu biyune suka haΙ—e mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taΙ“a zuwa irin waΖ΄annan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai,  su Husnah sunyi rawa sosai sun raΖ™ashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata’iya ba gaba Ι—aya nauyi da kunya sun hanata sakat…. sai gab da magrib aka tashi  daga kamu kowa yasamu abun arziΖ™i ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka…    Yanzu kam mota Ι—aya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban…  Jingina bayanta tayi da kujera haΙ—e da kwantar da kanta akan kafaΙ—an Husnah, duk hiran da  Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC’n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaΙ“i, haka dama ita take matuΖ™ar ta shiga  hayaniya to kanta sai ya Ι—anyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita Ι—anyi zazzaΙ“i..  Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi…  Fitowarta a wanka kenan,  sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..+

“Wai ke da waye ne haka?  a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da’alama dai munsamu Ζ™aruwa” Zahrah tafaΙ—i maganar cikin sigar tsokana… Dariya Husnah tayi haΙ—e da Ι—age giranta sama.    “Ƙwarai kuwa tawan, wallahi Ι—azu na haΙ—u da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai”

Dariya Zahrah ta sanya haΙ—e da neman guri ta zauna akusa da Husnah haΙ—i da kwantar da kanta akan kafaΙ—an Husna’n….

“Husnah kinsan ya so yake?”  tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..

Mamaki tambayar da  Zahrah tayi mata  ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba…

“Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa  bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!” Husnah tafaΙ—i haka tana me wasa da wayar hanunta, da’alama sunan Yazeed kaΙ—ai da ta ambata yasanyata cikin shauΖ™i..

Ajiyar zuciya me Ζ™arfi Zahrah ta sauΖ™e haΙ—e da Ι—ago kanta daga kan kafaΙ—ar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da  Husnah “Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so?  sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take Ζ™oΖ™arin sake son wanda yacutar da’ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon mamaki haΙ—e da Ι—aurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, Ζ™warai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?

“Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina  babu amfanin  zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaΖ™i dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da’irin Ζ™arfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taΙ“a fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake Ζ™ira da Ζ™auna, ita Ζ™auna kuma idan zafinta yatashi Ζ™ona ka, to  Ζ™unan yakan kasance me tsananin zafi da raΙ—aΙ—i bakamar na so ba,   ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?” Husnah tafaΙ—i haka tana murmushi.. Wasu siraran  hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan Ζ™uncinta.

“Zahrah kuka kuma?” Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka  acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah’n ce tafara Ι—ago maganar ba wai ita ba.

Hanu tasanya ta share hawayenta haΙ—e da sakin murmushi,  “Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunΙ—azu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana Ι—an kwanta, idan kingama ki rufe mana Ζ™ofa” Zahrah tafaΙ—i haka fuskarta Ι—auke da murmushin dole..

Har Zahrah  ta kwanta Husnah bata Ι—auke idanunta daga kanta ba,  sosai ganin hawayen Zahrah’n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da’ita a Ζ΄an kwanakinnan gaba Ι—aya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah…

Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taΖ™i tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taΙ“a bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haΙ—iye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaΙ—ai, koda kuwa damuwartata zata kasheta,  tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai Ι“oyu ba, amma kuma zatayi iyaka Ζ™oΖ™arinta wajen ganin ta maidashi Ι“oyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya Ι—auketa, tana bacci babu jimawa kuwa Ζ™iran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da Ζ™iran ne yasanya Husnah Ι—aga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haΙ—e da ajiye wayar..   

Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe  yayinda tausayinta yakuma Ι—arsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da  sabgoginsu…… 

Kafe cak idanunsa  suke akan haΙ—aΙ—Ι—en zanen POP’n dake mamaye saman Ι—akin wanda aka Ζ™awatasa da ado me matuΖ™ar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin  Zahrah’nsa fiye da komai,  yanzu kenan saura kwana uku a Ι—aura mawa Zahrah’nsa aure da wani bashi ba,   rumtse idanunsa yayi da sauri haΙ—e da haΙ—iye wani irin yawu me Ι—aci daya tsaya masa a maΖ™oshi, abu kamar wasa saiga Ζ™walla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid,  hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauΖ™ar Ι—umin wani abu kamar ruwa,,  ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuΖ™ar ciwo,  rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, Ζ™addara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haΖ™iΖ™a SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso Ι—in ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa,   tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi  ba sha’awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan,  idan yace zai  misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaΙ—e  zuwa yau to tabbas yayi Ζ™arya, ya cutar da’ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta Ζ™ishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba,  saurin rumtse idanunsa yayi haΙ—e da dunΖ™ule hannayensa da Ζ™arfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba  face tunowa da yayi  lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da Ζ™arfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,,  kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,,  ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba Ι—aya idanunsa sun kaΙ—a sunyi jajur dasu,   Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom Ι—insa, cikin sauri hartana haΙ—awa da tuntuΙ“e tanufi Ι—akin nasa,, kwance tagansa akan gado yaΙ—aura duka hannayensa akansa yana wani irin Ζ™ara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..3

STORY CONTINUES BELOW

“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, Zaid! Zaid!!” Mom taΖ™ira sunansa cikin matuΖ™ar ruΙ—ewa,,   girgiza sa Mum tashiga yi  cike da ruΙ—ewa sunansa kawai take Ζ™ira, a tunaninta Zaid Ι—in nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom Ι—insa acikin kunnensa yatashi a zabure haΙ—e da faΙ—awa cikin jikin mahaifiyartasa,  abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani Ζ™aramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid Ι—in tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin Ι—a ba?.

“Zaid” Mum takuma Ζ™iran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni Ζ™walla harsun cika mata ido…   “Please help me Mum, i don’t want to lost her!”  abun da Zaid ke faΙ—a kenan yana kuka,,  mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum  wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taΙ“a bari tanaji tana gani Ι—anta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani….

Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace “Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haΖ™uri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?”

Kai Zaid ya kaΙ—a tamkar wani Ζ™aramin yaro.  

“Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da’ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!”

Mum ta Ζ™are maganar cike da lallashi..

Kansa ya kwantar akan kafaΙ—an mahaifiyartasa lokaci Ι—aya yashiga sauΖ™e ajiyar zuciya irin dai yaro Ζ™arami yayi kuka ya Ζ™oshin nan…. Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da’alama dai bacci ne ya Ι—aukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid Ι—in yayi bacci ta tattaro duka Ζ™arfinta  haΙ—e da  zameshi akan kafaΙ—anta ta kwantar da kansa bisa kan pillow’n sa haΙ—e da ja masa bargo ta rufeshi,   kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu’a  ta shafa masa akan fuskarsa,  cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin Ι—akin, gaba Ι—aya zuciyarta tayi rauni……1

*Washe Gari*

Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya Ι—aukarwa su Zahrah bayan yabiyata maΖ™udan Ζ™uΙ—aΙ—e tazo gidan,, zanen jan lalle me matuΖ™ar kyau aka tsantsarawa  Zahrah akan hanu da Ζ™afarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,,   lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya Ζ™ara Ζ™awata farar fatarta gwanin sha’awa. Wayarta dake ringing ta Ι—auka haΙ—e da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace “Amaryata”       murmushi tasakar masa me sauti haΙ—e da cewa “Umm”     Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haΙ—e da cewa “Ki Ι—an bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki”  ya Ζ™are maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta.     Ajiyar zuciya Zahrah tayi haΙ—e da cewa “Gani nan zuwa”  tana aje wayar   ta Ι—auki wani haΙ—aΙ—Ι—en mayafi wanda aka masa ado da  fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haΙ—aΙ—Ι—en gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa ta cikin mayafin..

Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haΙ—e da kashe mata ido Ι—aya, dariya suka sanya su duka domin sukaΙ—ai suka san ma’anar hakan…. Murmushi yayi haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,,  buΙ—e murfin motar tasa tayi tashiga bakinta Ι—auke  da sallama,, cikin murya me Ι—auke da kasala ya amsa mata sallaman haΙ—e da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake Ζ™ara mata kyau akoda yaushe tayi masa haΙ—e da Ι—an tsaida idanunta akansa,,,,    shiΙ—inma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta’iya tsaida idanunta akan sa a yau Ι—in, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.  

“Namiki kyau ne Ζ΄an mata?” yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,   

“Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!” yafaΙ—i haka yana me Ζ™oΖ™arin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,,  saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haΙ—i  da  cewa “Sai an biya kuΙ—i me yawa sannan ake kallon wannan zanen”    murmushi yayi me sauti, ba Ι“ata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuΙ—i yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya Ι—aura mata akan cinyarta.

“Karki hanani gani please” yafaΙ—i maganar yana me marairaice fuska,   

“NaΖ™i wayon kuma ni wannan kuΙ—in sunmin kaΙ—an” tafaΙ—i haka cikin sigar wasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi,  kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta Ζ™oshi sannan tace “Kasan baka da kuΙ—i kuma kakeson ganin zanen lallena?”

Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin Ι—ago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taΙ“a ganinta ba, murmushi kawai tayi haΙ—e da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.

“Zahrah na!”  yaΖ™ira sunanta cikin wata irin murya me sanyi.  Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..

YabuΙ—e baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma Ζ™ara,,

“Hajiya”

shine sunan dake yawo akan screen Ι—in wayar, dakatawa da maganar yayi haΙ—e da Ι—aukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na Ι“acin rai tace

“Kana’ina ne?”

“Ina wajen Zahrah Hajiya” yabata amsa cike da girmamawa.

“Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka” tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.

A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haΙ—e da sauΖ™e ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haΙ—e da Ι—an sakin murmushi.

“Hajiya nason ganina yanzu, ki riΖ™e wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!” yafaΙ—i haka yana me miΖ™a mata wasu kuΙ—aΙ—e masu yawa daya ciro daga cikin wata Ζ΄ar loka dake cikin motar. 

“A’a ae bana buΖ™atar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready,  sannan kuma  inada kuΙ—i a wajena ka….”

“Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karΙ“a kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci” yafaΙ—i haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta Ζ™arisa ba,,   badon ranta yasoba ta amshi kuΙ—in haΙ—e dayi masa godiya kana ta buΙ—e murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar Ζ™ofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin Ζ™iran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba,  idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haΖ™uri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa…

Fuska Ι—auke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa   “tafasa aurena kuma Hajiya?”

“Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba’aje ko inaba kana nuna banbanci Ζ™arara, gashi  abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!” Hajiya tafaΙ—i haka cikin Ι“acin rai.

Sunkuyar dakai Ζ™asa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi Ζ™aunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma Ζ΄ar uwarsa ta jini.

“Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuΙ—in auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaΙ“a ma ni tashi kabani waje !”

Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa  cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon…

Yana shiga Ι—akinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daΙ—i kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da Ι—aya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaΙ—aima ta’ishesa rayuwa,   yaji daΙ—in fasa wannan auren Ζ™warai… 

*Zaid*

Gaba Ι—aya jikinsa yaΖ™i daΙ—i duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba Ι—aya  baiyishi cikin daΙ—i ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa  da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah….

*Friday*

Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haΙ—aΙ—Ι—en sari da aka Ι“ata lokaci wajen naΙ—a mata shi ajikinta,  yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faΙ—a, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,,  motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za’a gudanar da walima,,,   walima fa ya Ζ™ayatar saboda Malami aka Ι—auko na musamman yagudanar da wa’azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaΖ™ara da wa’azi me ratsa jiki  harsaida amarya tayi  kuka,,  bayan anΖ™are walima ne kuma aka soma rabon abinci  haΙ—e da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai.  Walima fa yaΖ™ayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka  aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar  kuma take Ι—aurin aure?.Yauma dai kamar jiya agajiye take matuΖ™a,  suna komawa gida ta yi wanka da ruwa me zafi sai alokacin ta Ι—anji ta samu nutsuwa a jikinta.  Kwanciya tayi luf akan katifarta  haΙ—e da jawo wayarta tasoma buga game, tayi hakanne  gudun kada tunani ya samu daman bijiro mta acikin zuciya…+

“Kinada baΖ™o a waje fa Zahrah” maganar da tafito daga bakin Husnah wacce shigowarta Ι—akin kenan..

“BaΖ™o kuma Husnah?” Zahrah tatambaya cike da mamaki.

“Ƙwarai kuwa amma sai dai gaskiya inaga ba ya Ι—aya daga cikin abokan Doctor, yakamata kije ki gansa dan naga kamar yamatsu dason ganinki” Husnah tafaΙ—i haka bayan tayi mawa kanta masauΖ™i akan katifar da Zahrah take kwance…

Cike da mamaki Zahrah tamiΖ™e tsaye haΙ—e da Ι—aukar mayafi ta rufa ajikinta, hakanan taji  tamatsu da taga waye ne ke neman nata…..

Tana fita waje tasoma raba idanu ko zata hango wanda akace yana Ζ™iranta, sai dai kuma bata ga kowa ba…

“Zahrah” taji anΖ™ira sunanta daga bayanta,, da sauri ta juya don ganin kowaye.

Wani kyakkyawan saurayi handsome guy tagani tsaye a bayanta yana ta zuba murmushi,  kallo Ι—aya zakayi masa kafahimci cewa shiΙ—in cikekken Ι—an gaye ne, kuma Ι—an hutu, domin kuwa fatar jikinsa da kuma kayan dake sanye ajikinsa kaΙ—ai sun isa tabbatar maka da hakan..

Takowa yashigayi  gareta, har saida yazo kusa da’ita kafun ya ja ya tsaya,  kallon kallo suka shiga yiwa juna,  Zahrah kallon mamaki da kuma al’ajabin me ya kawosa wajenta take yayinda shikuma yakeyi mata kallon Ζ™urilla,, wani yawu ya haΙ—iya a maΖ™oshinsa bayan yagama Ζ™are mata kallo daga samanta har Ζ™asanta…    “Zahrah ko?” yafaΙ—i haka yana me nuna ta da yatsarsa…

Kai kawai Zahrah ta’iya jinjina masa alamar “Eh” still amma kuma idanunta nakansa..

Murmushi yakuma yi mata haΙ—e da gyara tsayuwarsa  “Naji daΙ—in ganinki Ζ΄an mata, sunana Abid, nasan baki sanni ba amma kuma idan babu damuwa me zai hana muje mota sai muyi maganan, saboda nazomiki da wata magana ce  me mahimmanci”  yafaΙ—i haka yana me sake dubanta da kyau…

Kallon sa itama ta sakeyi sosai kafun ta ce. “KafaΙ—i duk abun da zaka faΙ—a anan inaji, amma bana buΖ™atar shiga cikin motarka” ta Ζ™are maganar tana me Ι—age kanta sama.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi Abid yakumayi akaro na barkatai “lallai ba’a banza ba Zaid yakasa magance matsalarsa yarinyar akwai taurin kai” yafaΙ—i haka acikin zuciyarsa…

“I’m sorry bacutar dake zanyi ba, kada kiji tsorona, nazo miki da magana ne me matuΖ™ar mahimmanci, nasan abune me wahala amma kuma keda kanki  zakiso ace kinzamo silar ceto rayuwar da take shirin gushewa, nasan bazakiso ace ta sanadiyarki Zaid ya rasa rayuwarsa ba,  kina da tausayi Zahrah, me yasa bazaki yarda ki aure sa ba?” abunda ya fito daga bakin Abid kenan..

Kallon baka da hankali Zahrah tashiga bin Abid dashi, da Ζ™yar ta’iya cewa   “Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba,  da bantsaya Ι“ata lokacina wajen saurararka ba, don bazan Ι“ata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya Ζ™yaleni  na huta, domin kuwa  ko maza sun Ζ™are a duniya bazan taΙ“a auren Zaid ba!” Zahrah tafaΙ—i haka cikin dakiya dakuma Ι“acin rai…

“Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faΙ—a ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haΖ™iΖ™a nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid Ι—in dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa Ζ™waΖ™walwa, wallahi ke kaΙ—aice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki,  akan ki Zaid yafara sanin menene Ζ™unci, akanki yafara sanin menene  Ι—acin soyayya dakuma zaΖ™inta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaΙ—aice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!” Abid yaΖ™are maganar cike da raunin murya sosai yake matuΖ™ar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba Ι—aya yafita hayyacinsa…

Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haΙ—e da sanya haΖ™oranta tacije lips Ι—inta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta

“Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daΙ—i na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama,  yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama,  nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waΖ΄annan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama,  domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah,  inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haΖ™iΖ™a ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen Ζ™addarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haΙ—a rayuwata da ta Zaid!”  hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haΙ—e da juyawa tasoma tafiya…2

“Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aΙ—aura da Zaid nasan iyayenki zasu amince,  shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki,  ki amince ki aure sa, wallahi namiki alΖ™awari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buΖ™ata nabaki zan baki,  amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI”  Abid yana kaiwa nan azancensa  yabuΙ—e murfin motarsa, wata Ζ΄ar madaidai ciyar jaka ya Ι—auko,  takawa yashigayi harsai da yazo kusa da’ita kafun ya tsaya… “Ki amshi wannan jakan idan kika buΙ—e laptop Ι—in dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI’N SONKI”  Abid yafaΙ—i haka yana me miΖ™a mata jakar..   Tsintar kanta tayi da kasa Ζ™in karΙ“an jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta Ι“ule Zahrah na tsaye sororo hanunta riΖ™e da jaka,,,   saurin share hawayenta tayi, haΙ—e da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin Ι—akinta, abun yayi mata daΙ—i sosai   data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haΙ—e da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki,   kanta ta Ι—ago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haΙ—e da buΙ—eta,  a hankali ta zaro laptop Ι—in dake cikin jakar, saida ta Ζ™arewa laptop Ι—in kallo kafun ta buΙ—eta,    tana danna wani madanni laptop Ι—in takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop Ι—in, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka Ι—auketa hoton ba, Ζ™urawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai,  bata Ι—auke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen Ι—in laptop Ι—in ya gaji dan kansa ya Ι—auke..  Ajiyar zuciya me Ζ™arfi ta sauΖ™e haΙ—e da sake kunna laptop Ι—in, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga Ι“angaren hotuna,, tana kutsawa Ι“angaren hotuna,  hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop Ι—in, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta Ζ™waya Ι—aya bata dashi acikin wayarta,,,,  bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata,  hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faΙ—uwa yayinda Ζ™irjinta yashiga dokawa da sauri..  da Ζ™yar ta’iya view Ι—aya daga cikin tarin hotunan nasa,   sanye yake da wandon jeans baΖ™i dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuΖ™a a hoton domin kuwa fuskarsa Ι—auke take da wannan Ζ™awataccen murmushin nasa wanda yake Ζ™ara masa kyau ako da yaushe…   Ζ˜ura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiΙ—inne da kansa agabanta,  batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan Ζ™uncinta ba,,  tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta,  Ι“angaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma Ι—aga mata hankali,,  Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu Ζ™arafan na’urori akan Ζ™irjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon Ι—an abu kamar computer’n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haΙ—e da  rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop Ι—in akan Ζ™irjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin Ι—akin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buΙ—e idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raΙ—au acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haΙ—e da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah.   “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?” Husnah ta tambaya cikin ruΙ—ewa…   Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faΙ—a jikin Husnah ae kuma saita Ζ™ara volume Ι—in kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, “Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru” Husnah tafaΙ—i haka acikin zuciyarta.18

STORY CONTINUES BELOW

“Kiyi shiru dan Allah Zahrah, kinga dai yanzu dare ne sokike kowa saiyaji gunjin kukan ki? kiyi shiru kisanar dani meke faruwa” Husnah tafaΙ—i haka ga Zahrah cike da damuwa…   Yau Zahrah tsintar kanta tayi da kasa daina kuka, ji ma take tamkar Husnah ingizata take da ta Ζ™ara volume,,    sororo haka Husnah tayi ganin Zahrah taΖ™i daina kukan,  zame ta tayi daga jikinta haΙ—e da nufar inda  aka aje musu ledan ruwa na pure water,  guda Ι—aya ta zaro acikin ledan haΙ—e da fasawa ta tsiyaya acikin cup,, dawowa tayi ta zauna haΙ—i dakai kofin ruwan bakin Zahrah,  babu musu Zahrah ta amshi kofin takai bakinta, gaba Ι—aya ruwan dake cikin kofin tashanye tas haΙ—e da aje kofin agefe, ajiyar zuciya tasoma sauΖ™ewa akai akai amma na kuka,,,  kwanciya tayi luf haΙ—e da sanya hanu ta dafe kanta dake matuΖ™ar sara mata,,, idanu kawai Husnah ta zuba mata tana me mamakinta, gaba Ι—aya aΖ΄an kwanakinnan talura Zahrah ta maida kuka abinci da kuma ruwan shanta,  ita yanzu hartama fara tunanin ko aljanune suka shiga jikin Zahrah’n,,   bayan kamar minti goma Husnah taΖ™ira sunan Zahrah,, amma kuma saitaji shiru Zahrah bata amasa mata ba, hakan ne yasanya tayi tunanin cewa Zahrah’n tayi bacci,  raΙ“awa gefen Zahrah’n itama tayi ta kwanta, mintuna kaΙ—an bacci yakuma surarta, Zahrah na jin sauΖ™ar numfashin Husnah nafita a hankali ta tabbatar da cewa Husna’n tayi bacci,  ahankali ta ware idanunta dasuka cika tab da Ζ™walla,  sarai tanaji sanda Husnah taΖ™ira sunanta, taΖ™i amsawa ne gudun kada ta tonawa kanta asiri, saboda batason wannan sirrin yafita daga cikin zuciyarta, har abada tafiso ta bunneshi ita kaΙ—ai batare dakowa yaji koya gani ba, ada tana ganin cewa ita mahaukaciya ce datakeson wanda ya zalunceta, sai ayanzu ta sake tabbatarwa kanta cewa shi so babu ruwansa, idan zai shiga jikinka baya duba wani cancanta ko matsayi haka nan yake faΙ—a ma, ashe da fari tayi Ζ™arya da tace zatayi yaΖ™i da soyayyar Zaid a zuciyarta, ashe ba’a iya yaΖ™i da soyayyar da take acikin jini da tsoka,,  ada tana tunanin cewa zuciyarta bata kyauta mata ba, ashe itace bata kyautawa kanta ba, yanzu ta gamsu cewa so ne ya lalata mata rayuwa ba wai Zaid ba, ashe so shine ya yaudareta, ashe so shine yaci amanarta, ashe Zaid bai aikata mata wani babban laifi ba So ne ya aikata mata laifi me girma, inama da ana ganin so, to da tayi masa roΖ™o takuma yi masa magiya akan cutarwar da yayi mata daya barta haka,,   itakuma SO shine Ζ™addaranta, ada ta Ι—auka idan tafaΙ—awa mutane cewa tanason mutumin dayayi sanadiyar rugujewar rayuwarta, kowa zai Ι—auketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaΙ—an baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci Ζ™anΖ™ani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaΖ™anci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaΖ™anta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuΖ™ar haΙ—ari sannan yafi kowani abu saurin Ι—aiΙ—aita tunanin meyinsa, SO shikaΙ—aine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,,  hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago Ζ™asa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaΖ™auracemawa idanunta…..9

(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haΖ™iΖ™a Zaid ya cancanci Zahrah taΖ™isa mugun Ζ™i mawa kuwa, amma kuma SO bazai taΙ“a barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba,  nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauΖ™i, sannan kuma zafinsa yanada matuΖ™ar illa, ba’akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taΙ“a gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haΖ™iΖ™a idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaΙ—e kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani? nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka?)2

STORY CONTINUES BELOW

Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin Ζ™arfin tunanin Doctor’s domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauΖ™i saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba Ι—aya hankalin Alhj Ma’aruf yakai Ζ™ololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma’aruf yanke hukuncin tattara Zaid Ι—in sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi Ζ™arfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid  cikin aman jini yake, lokaci Ι—aya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba

Zaid ba…..11

Washe Gari (Asabar)

*ƊAURIN AURE*

Tun Ζ™arfe 8 na safe  gidansu Zahrah yake acike yayinda Ζ΄an uwansu na nesa suka soma hallara don Ι—aurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan…

Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki…

Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai Ι“oye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaΙ—auki zafin zazzaΙ“i zau..

“Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba” Husnah tafaΙ—i haka ga Zahrah cike da lallami..

Kai kawai Zahrah ta’iya kaΙ—awa alamar “A’a bazata sha ba” komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaΙ—a kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau Ι—in,, duk yanda Husnah takaΙ—a ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani Ζ™iyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta Ζ™yaleta..1

10:30 tuni Ζ™ofar gidansu Zahrah yasake cika da jama’a  bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka Ζ™araso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata  haΙ—aΙ—Ι—iyar gezina milk colour me matuΖ™ar kyau da tsadar gaske, Ι—inkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya Ι—aura tsadadden agogo a hanunsa na dama,  takalmin Ζ™afarsa kuwa Ζ™irar kamfanin GUCCI ne me matuΖ™ar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiΙ—in ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk Ζ™waΖ™wan mutum babu ta’inda zai kushesa, yahaΙ—u iya haΙ—uwa sonkowa Ζ™in wacce ta rasa?,  bakin ango fa yaΖ™i rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taΙ“a iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haΖ™iΖ™a yau yana cikin nishaΙ—i dakuma jin daΙ—i, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biΙ—ar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana… Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,,     11:00 am   dai dai dandazon jama’a suka shaida Ι—aurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu Ι—ari,,  masha Allah ana kammala Ι—aurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haΙ—e da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa… Bayan angama musabahane kuma aka Ι—unguma zuwa wani babban hotel wanda anan za’a gudanar da receiption….16

Lokacin da labari Ι—aurin auren ya’isa ga kunnen Amarya wani irin faΙ—uwar gaba wanda bata taΙ“a jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor,  zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har Ζ™irjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluΙ“e mata jiki,ae kuwa sai neman Ι—an kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba Ι—aya gaΙ“oΙ“inta sun mutu laΖ™was kamar ansassare mata su,, sake duΖ™unΖ™unewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti,  ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaΙ—an, amma kuma tarasa meke damun Ζ™waΖ™walwa da zuciyarta….

STORY CONTINUES BELOW

(Kuyi haΖ™uri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba Ι—aya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita Ζ™addara bata taΙ“a sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota? yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya Ζ™are?)9

Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba….1

Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniΖ™an sai dai godiyar Allah da sanya albarka…

Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaΙ—ai ke tsaye akanta tana bata kulawa. 

“Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koΙ—an sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za’a zo Ι—aukarki!” Husnah tafaΙ—i haka tana me Ζ™oΖ™arin tada Zahrah dake kwance zaune.

Da taimakon Husnah Zahrah taje banΙ—aki tayi wanka, koda tafito wata haΙ—aΙ—Ι—iyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuΖ™ar yi mata kyau ajiki, da Ζ™yar Husnah ta lallaΙ“ata tashafa mata powder haΙ—e  da man leΙ“e, sai kace wata Ζ™araman yarinya,,,   komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa  (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole ?)…7

Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin Ι—aukar amarya suka shiga fakawa a Ζ™ofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don Ι—aukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..

Zahrah na zaune wata Aunty Ladi Ζ΄ar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin Ι—akin babban mayafi  me kyau ta Ι—auka haΙ—e da rufe Zahrah dashi, miΖ™ar da’ita tsaye tayi cikin farinciki tace

“Allah yayi yauzaki tafi Ι—akinki amarya muje Ι—akin Inna’n taki aimiki nasiha”

aitun kan aΖ™arasa Ι—akin Inna Zahrah ta Ι“arke da kuka wiwi,  (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daΙ—in gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan ??)1

Nasiha Inna da sauran matan dake Ι—akin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda Ζ™afa inayi bari na bari, komin Ζ™anΖ™antan Ι“acin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taΖ™i ji tagani taΖ™i gani,  takuma riΖ™i haΖ™uri don shine tubali kuma gini haka Ζ™inshiΖ™in zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a’a watarana dole sai kunΙ“atawa juna, dole sai kunyi haΖ™uri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daΙ—i, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har Ζ™asa ta duΖ™a tabasa haΖ™uri, domin kuwa har kullum shine sama da’ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiΙ—ewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daΙ—i tafiyan Zahrah’n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol ?.

Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da’ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faΙ—a jikinsa haΙ—e da sake Ζ™ara volume Ι—in kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye,  daΖ™yar ya’iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar Ι—ayace shine tabi mijinta sau da Ζ™afa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haΖ™uri akan dukkan komai, sannan kuma yaroΖ™i yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata?

Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah  tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za’a zo a Ι—auketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin?…

Anasa amarya acikin mota sauran Ζ™awaye da Ζ΄an uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane  motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa…1

Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner…

Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaΙ—an bata nuna musu Ι“acin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baΖ™aunarsu sukeyi ba, Ι—aki guda aka warewa amarya, balaifi Ι—akin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah,  mintuna kaΙ—an da shigowansu Ι—akin wasu Ζ΄an mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor……

Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke Ζ™iran nata yasanya ta Ι—aga wayar bawani Ι“ata lokaci 

“Bestie’n mu how far?”  abunda wanda yaΖ™irata acikin wayar yafaΙ—a kenan..

Dariyane yakamata amma saita taΖ™aita dariyan haΙ—e da cewa “I’am fine sai dai gaskiya na gaji”

Murmushi shima yayi haΙ—e da cewa “Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da’ita fa tun ranan alhamis” Dr.Sadeeq yafaΙ—i haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa…1

“Kamar kuwa kasan kainaketa so kaΖ™ira, wallahi yau tun safe Zahrah taΖ™icin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature Ι—inta ya hau sosai”  Husnah tafaΙ—i haka ga Dr.Sadeeq.

“Subahannallah, keda su waye aΙ—akin?” Dr. yatambayi Husnah cike da zaΖ™uwa..

Kallon waΖ΄anda ke cikin Ι—akin Husnah tashiga yi kafun tace

“Gaskiya munada Ι—an yawa”

“Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters  kinji”

“To shikenan zan kawota insha Allah”

Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta’ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riΖ™eshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taΙ“aci da yaudara………

Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 9 BY FATYMA SARDAUNA"