TAWA TA SAMENI CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
TAWA TA SAMENI CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI TAWA TA SAMENI CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA nayi zurfi a tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wlh mama ni ban taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta yanxu ma ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace m…