SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Cikin rashin kuzari yamiƙe haɗe da nufar hanyar barin falon, ko kaɗan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye ɓangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani. Gaba ɗaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuƙar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haƙiƙa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu ɗaya. shine Doctor Sadeeq sam basa’an auren ta bane, yafi ƙarfinta. Yau kimanin kwana huɗu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan da…