SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin rashin kuzari yamiΖe haΙe da nufar hanyar barin falon, ko kaΙan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye Ιangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani.
Gaba Ιaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuΖar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haΖiΖa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu Ιaya. shine Doctor Sadeeq sam basa’an auren ta bane, yafi Ζarfinta. Yau kimanin kwana huΙu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan daren kuwa harzuwa yau, Dr baisake zuwa gareta ba, saidai fa kullum safiya, yana turo drivern sa akan yaΙauketa yakaita makaranta. amma zancen dai Ιayane, bata taΙa yarda tashiga motar, koma sauraran driver’n nasa batayi.
Dariya sosai Mahmud yashiga yi, a lokacin da yagama jin matsalolin abokin nasa, haΖiΖa Sadeeq yabasa dariya, ko da wasa bai taΙa tunanin wai Namiji kamar Sadeeq zaiji tsoron furtawa mace kalmar soyayya ba.
Tsuka Dr Sadeeq yaja haΙe da Ιata fuska cike da takaicin dariyan da Mahmud Ιin ke masa yace
” Bawai nafaΙa maka matsalata bane don kasani a gaba kayita min dariya ba, mafita nake nema Mahmud, gaba Ιaya kaina ya kulle, inasonta banakuma tunanin zan’iya barinta, amma kuma naga alamomin cewa zan rasata a fili!” Dr Sadeeq yafaΙi maganar cikin son abokinnasa ya Ζarfafa masa guiwa.
ΖoΖari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haΙe da gyara zama
“Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaΙan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai Ζalubale a gabanka!” Mahmud yaΖare maganar yana mai waina pen Ιin dake riΖe a hanunsa.
“Wani irin Ζalubale kenan Mahmud?” Dr Sadeeq yatambaya cike da zaΖuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.
“Nasara ko kuma akasinta, sune babban Ζalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaΙu sosai, saboda nasan abokina ya’iya zaΙe!” Mahmud yafaΙi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.
“Bazaka taΙa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki.” Dr Sadeeq yafaΙi hakan yana mai shafa suman kansa.
Ζ³ar Ζaramar dariya Mahmud yayi haΙe da Ιaukan cup Ιin juice Ιin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.
“Babu amfanin Ζara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake Ιago mata da zancen inaga haka zaifi!” Mahmud yafaΙi hakan cike da son Ζarfafamawa abokinsa guiwa.
STORY CONTINUES BELOW

ΖaΖΖarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauΖe, haΙe da haΙiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba Ιaya kansa ne ya kulle.
“Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taΖi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!” Dr Sadeeq ya faΙi haka cikin Ιar Ιar.
Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaΙai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma Ιar Ιar.
“Yanaga jikinka gaba Ιaya yaΙau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?” Mahmud yatambaya cike da shaΖiyanci.
Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haΙe da miΖewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baΖin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.
“Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka Ζoshi, ai nine nakawo kaina office Ιinka, kana da right Ιin da zaka iyamin komai” Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit Ιin dake jikinsa.
Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office Ιin Mahmud Ιin.
Cikin Ιan kuzarin da yasamu yake tuΖa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haΙe da shirya kansa cikin wani haΙaΙΙen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaΙan Ζamshin turare. Makullin motarsa ya Ιauka haΙe dasakai yafice daga cikin Ιakin.
Zaune take akan Ζ΄ar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da’alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta Ιauke yake da danshin ruwa. Kallo Ιaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba Ιaya ta zabge ta faΙa, hips da breast Ιin tane kawai suke a cike a jikinta. A hankali take shafa Vaseline Ιin dake riΖe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline Ιin idan ka gani, kace dole akai mata. tana gama shafa mai Ιin, ta murza powder kaΙan akan fuskarta, haΙe da shafa kwalli a cikin idanunta, take fuskarta ta tasakeyin fayau, yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.
Kallonta tamayar kan Ιan Ζaramin agogon bangon dake Ιakin nata, Ζarfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miΖe haΙe da Ιaukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa atamfar mai sauΖin kuΙi ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba. Wani irin zazzaΙi takeji yana sanΙan jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alΖawarin cewa zata zo yau Ιin ba, to tabbas da ta Ιage zuwa gidansu Husna’n saboda bata wani jin daΙin jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.
Inna ce tashigo cikin Ιakin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab Ιinta.
“Au ashema kinsan da zuwansa kenan?” Inna tatambaya tana mai Ζarewa Zahrah kallo.
“Banganeba Inna, zuwan waye kuma?” Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna’n suka dosa.
“Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!” Inna tafaΙi hakan tana mai ΖoΖarin barin Ιakin.
“Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?” Zahrah takuma tambaya cike da son Ζarin bayani.
“Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike Ιinnan, ai sai dai shiΙin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa Ζasa a idanu!” Inna taΖare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin Ιakin.
STORY CONTINUES BELOW

Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faΙa, babu wani mai nemanta sai shi Ιin shi kaΙai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaΙa, ashe dagaske ne itakam Ζaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta, saurin share hawayenta tayi haΙe da sakai tafice daga cikin Ιakin.
Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duΖe a Ζasa, Ιan makullin motarsa ce riΖe a hanunsa yana kaΙawa, wannan karon kam sosai yake yaΖi da zuciyarsa don bayaso tasake sanya masa tsoro kokuma ΙarΙar.
A hankali take taku cike da nutsuwa har ta Ζaraso garesa, Ιan nesa dashi ta tsaya haΙe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.
Lumshe idanunsa yayi haΙi da buΙesu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.
“ZAHRAH!” yaΖira sunanta cikin murya marar fidda ΖaΖΖarfan sauti.
“Um!” Zahrah ta amasa masa batare da ta’iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duΖe yake tunda tazo bata’iya Ιaga kai ta kallesa ba.
Kallonta yashiga yi tundaga Ζasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba, take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.
“Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buΖatar zama!” yafaΙa cike da Ζosawa da tsayuwan da yakeyi.
Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai Ιauke idanunsa daga kanta ba, “Wallahi Zahrah ta haΙu, komai nata mai kyau ne!” yafaΙi hakan a fili, cike kuma da shauΖin soyayya.
Jim kaΙan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta, “Kashigo!” kawai ta’iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da’ita haka suka doshi cikin gidan.
Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can Ζarshen tabarman ta takure waje Ιaya, tamkar amaryar da aka kaita Ιakin miji yau yau, lol.
Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni, dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.
” Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba’abun da nakeyi, ko na taΙa miki wani abune ?” Dr yafaΙi hakan cike da kulawa.
Saurin Ιago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba Ιaya ya sauya wasu Ιabi’un nasa.
Giransa Ιaya yaΙage sama, haΙe da cewa “Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?”
Girgiza kanta tashiga yi ita kaΙai tamkar Ζadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.
“Matso kusa dani mana!” yafaΙa cikin sanyin murya, mai Ιauke da lallashi.
Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haΙa jikinta duka ta takure waje Ιaya.
Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauΖe haΙe da sanya hanunsa yashafi Ζasumbar dake kwance akan fuskarsa.
“Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ΖwaΖwalwa, please banso kina wahalar da ΖwaΖwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!” Ιanjim yayi kana yaci gaba da cewa…” Kiyi haΖuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji Ζanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani Ιan adam yana da Ζ΄anci, kema kina da Ζ΄anci, saboda haka ki daina kuka kinji Ζanwar Likita!” Yanayin yanda yaΖare maganar kaΙai ya’isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.
STORY CONTINUES BELOW

Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta’aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta Ιago idanunta da suke Ιigan hawaye tamaida kallonta garesa, wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma Ζwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haΖuri akan abun da tayi masa ba.
Cike da damuwa ya dawo kusa da’ita, har suna iya juyo Ζamshin turaren juna.
“Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faΙamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haΖuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haΖuri Zahrah haka bazata….” Kasa Ζarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.
“Dan Allah kada ka ΖasΖantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haΖuri ba, nice yakamata na baka haΖuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haΖuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaΙi, kayafemin!” Zahrah ta Ζare maganar cikin kuka, haΙe da karyewar zuciya.
Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.
A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.
“Kinaso nayi haΖuri?” Dr yatambayeta.
Kaitashiga kaΙawa cikin kuka alamar “Eh”
“To kidaina kuka, domin kuwa daina kukanki shikaΙaine zaisanya nayi haΖuri nakuma manta da komai, kuma ko dama ni Zahrah batayi mini laifi ba, Ζanwata bata laifi a wajena, saboda haka share hawayenki kinji!” yaΖare maganar yana me miΖomata wani farin handkerchief wanda yafito dashi daga cikin aljihun wandonsa.
KarΙan handkerchief Ιin Zahrah tayi, cike da shagwaΙa tashiga share hawayen dake gudana akan fuskarta, ajiyar zuciya kawai take sauΖewa akai akai domin kuwa ko ba komai tarage wani nauyi dake maΖare a gefen zuciyarta.
“Yauwa Ζanwata, kinga kinfi kyau idan kina murmushi dakuma dariya, inaso akoda yaushe kikasance cikin farinciki!” Dr yafaΙa cikin nishaΙi, domin kuwa sosai yaji daΙin yanda Zahrah ta sauΖo daga fushin da takeyi dashi.
Tana gama share hawayen nata ta miΖamasa handkerchief Ιinnasa.
Kai yagirgiza alamar a’a haΙe da gyara zamansa “Nabaki kyauta, ki ajiye a wajenki, ko saboda gaba, domin naga ke kuka baya baki wahala, kinga duk lokacin da kika soma koke koken ki saiki share hawayenki da shi!”
Hararan wasa ta jefesa dashi, haΙe da murguΙa masa Ιan Ζaramin bakinta.
Dariya yayi domin sarai yana lure da’ita kuma yaga abun da tayi masa.
“Inazakije kikaci uban kwalliya haka? gashi kuma kinzo kinΙata shi da kuka.” YafaΙi maganar alokacin dayake ciro wayarsa daga cikin aljihunsa.
Turo bakinta tayi gaba, cike da ΖunΖuni tasoma motsa bakinta, da’alama wani abu takeson faΙa, “wai a hakanne nayi kwalliya, kawai dai yace banyi masa kyau ba” Zahrah tafaΙi hakan a cikin zuciyarta.
“Wayace miki hakane a zuciyata? ni na’isa nace kyakkyawar Ζanwata batayi kyau ba, to ma duk cikin garin Abuja wayakai ki kyau ne? babu fa!”
Dariya tasanya, wanda tajima batayi shiba, cab aikuwa ko da acikin makarantarsu akwai waΖ΄anda suka fita kyau dayawa, balle kuma duka garin Abujan baki Ιaya.
Tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyan, komai tayi Ζara kyau take.
Hanunsa ya sanya acikin aljihun wandonsa haΙe da ciro wani haΙaΙΙen choculate, Ιare ledan choculate Ιin yayi haΙe da miΖo ma ta. Kyawawan idanunta ta Ιago haΙe da watsa masa su, girgiza kanta tayi, alamar bata buΖata.
STORY CONTINUES BELOW

KwaΙe fuska Dr Sadeeq yayi haΙe da marairaice idanunsa, take taji tsikar jikinta ya zuba, yayinda gabanta yayi wani irin mummunan faΙuwa, domin kuwa hakan da yayi yasanya fuskarsa ta koma yanayi da fuskar Zaid, saurin Ιauke kanta tayi daga garesa, haΙe da sauΖe idanunta Ζasa, yabuΙe baki zaiyi magana kenan wayarsa tasoma Ζara, alamar shigowar Ζira, cike da girmamawa yaΙauki Ζiran ganin cewa Ζiran daga Hajiyarsa ce.
“Kana’ina?” Hajiya tatambaya a kausashe.
Baikai ga bata amsaba taci gaba da cewa “Koma mekakeyi kabari, Inaso kaje gidansu Salima yanzu, umarni ne ba shawaraba!” Ζit takashe wayan batare da tajira taji mai zai ceba.
Ajiyar zuciya ya sauΖe haΙe da maida kallonsa ga Zahrah.
“Wani uzuri yatasomin, zantafi kikula da kanki!” yafaΙi maganar yana me miΖewa tsaye.
MiΖewa itama Zahrah tayi batare da tace dashi komai ba tashiga naΙe tabarman da suka tashi akai.
Wani irin kallo haΙe da murmushi mai tsayawa a zuciya yayi mata, kana yasa kai yafice daga zauren gidan nasu, yana fita yafaΙa motarsa yayi mata key.
Tanajin Ζaran tashin motarsa ta sauΖe a jiyar zuciya haΙe da komawa cikin gida.
Kamar yanda mahaifiyarsa ta umarcesa hakan yayi domin kuwa yaje gidan su Salima sungana da’ita, yarinyar bata da wani aibu, amma kwata kwata jininsa danata baizo Ιaya ba, domin kuwa sam bata burgesa kasancewarta mace mai rawan kai da shegen girman kan tsiya, har gwamma masa Zabba’u akan Salima, domin dai shikam Salima batayi masa ba. Haka dai suka gaisa sama sama, ko minti 20 baiyiba yabaro gidan nasu..
Bayan Sati Ζaya.
Kusan ko da yaushe sai Doctor Sadeeq yazo gidan su Zahrah, amma kuma tundaga wannan lokacin baisake koda Ιago wani zance makamancin wancan ba, sai dai yana’iya ΖoΖarinsa wajen bata kyakkyawan kulawa. Sannan kuma dake ita Ιin me raunin zuciya ce take ta sake bashi yardanta akaro na biyu.
Ζangaren gidansu Dr Sadeeq kuwa harsun fara shirye shiryen bikinsa, domin kuwa Hajiyarsa wannan karon bada wasa take ba, tace acikin 3 weeks takeso ayi bikin. Shi dai Dr Sadeeq idanu kawai ya zuba musu, domin kwata kwata baijin auren a jikinsa, da za’afasa auren to dazai fi kowa murna, saboda Zahrah yakeso Zahrah ce muradinsa, amma kuma haryanzu yakasa samun wani gamsashshiyar amsa daga gareta.
Ζarfe 3 dai dai jirginsu ya sauΖa a babban airport Ιin dake cikin garin Abuja, motoci ne iri da kala har guda shida suka zo tarbansa, ciki kuwa hadda Dad Ιinsa, a hankali yake sauΖowa daga cikin matakalar jirgin sanyen yake da kayan sanyi hadda hula, yayinda fuskarsa ke ΙauΖe da wani haΙaΙΙen baΖin glass na maza, sosai yaΖara kyau da fari, kallo Ιaya zakai masa katabbatar da cewa yakai cikekke kuma gwarzon namiji, a gaskia yana da kyau da kuma kwarjini, uwa uba kuΙaΙe sun samu mazauni a jikinsa. Bakowacce mace bace zatayi tozali da haΙaΙΙen namiji kamar Zaid, kuma takau da idanunta ba, saboda Zaid yahaΙa duk wani abu da kowacce mace zata so awajen Ιa namiji, shidai matsalan sa Ιaya munanan halaiyansa. Yanda yake tafiya cike da izza shiyafi komai Ιaukar hankali, dakuma jan hankali zuwa garesa. Cike da farinciki Alhaji Ma’aruf yarungume Ιa’nnasa, duk da cewa babu wani shaΖuwa me Ζarfi a tsakaninsu amma yana matuΖar son Zaid.
Mota Ιaya suka shiga shida Dad Ιinsa, yayinda guard Ιinsu suka mara musu baya a cikin sauran motocin. Kwanciya yayi lamo ajikin kujeran motar haΙe da lumshe idanunsa, wani irin sanyi yakeji acikin zuciyarsa, koda wasa baitaΙa tunanin haka zai kasance dashi ba, kamarshi Zaid ace tunanin mace yahanasa sukuni harsaida yabaro duka abun da yakeyi ya dawo zuwa gareta, amma zaiyi maganin abun a yau bawai sai gobe ba yake da buΖatar ganin sugar baby’nsa, sai dai kuma wannan lokacin bada wasa yazo ba…
Zahrah ne keta kai kawo a tsakiyar Ιakinta, tabbas tayarda da duk wani shawara da zuciyarta ta bata, zuwa yanzu yakamata ace tayi abunda ya dace. Wayarta ne yasoma Ζara alamar shigowar Ζira, tana Ιaga wayar Dr Sadeeq yace “Gani na’iso ina Ζofar gida!”
“To” tace haΙe da aje wayar, ajiyar zuciya ta sauΖe haΙi da cije lips Ιinta, dama Ιaya kawai take dashi kuma tabbas idan tarasa wannan daman to zaiyi mata wahala tasake samun wani daman.
Hijib Ιinta ta sanya, koda tafito tsakar gida bata taradda Inna ba tana kuma da tabbacin cewa bama ta gidan.
Zaune yake acikin motar tasa, dagani kasan cewa yana cikin damuwa, domin gaba Ιaya har rama tasoma bayyana a jikinsa. Murfin motar tabuΙe tashiga, bakinta Ιauke da sallama, amsa mata sallaman nata yayi haΙe da gyara zamansa yafuskance ta ” Baki taΙa min irin wannan Ζiran ba, naΖosa naji wace maganace zaki faΙamin mai matuΖar mahimmanci haka” gaba Ιaya hankalinsa ya tattara zuwa gareta.
“Dagaske kake Zaka aure ni?” Zahrah tajefo masa tambayar
dabai taΙa zata ba balle tsammani.
Kansa yashiga kaΙawa muryarsa har rawa take yace “Dagaske nake Zahrah, wallahi auren ki nakeso nayi, samunki a matsayin mata shine babban burina a yanzu.” yafaΙi hakan da iya gaskiya’rsa
“So na kakeyi kokuma tausayina?” Zahrah takuma jifansa da wata tambayar.
“Sonki nake Zahrah, inamiki so mai tsanani, wlh inasonki da duka zuciyata!” Dr Sadeeq yabata amsa, cike da kulawa.
“Nayarda na Amince Zan aureka, muyi zama na har abada!” Abun da yafito daga bakin Zahrah kenan bayan tagamajin amsar da take buΖata daga garesa, cikin tsananin mamaki Dr Sadeeq yashiga kallonta, jin sauΖar maganarta yayi tamkar daga sama, kodai kunnuwan sa basu jiye masa dakyau bane?….Kasa motsa koda laΙΙansa yayi balle har yakai ga furta wata kalman, “dagaske ne abun da kunnuwansa suka jiye masa kokuwa mafarki yake?” yafaΙi hakan a cikin zuciyarsa.+
“Kada kayi kokonto kokuma shakka, dagaske nake, na amince da aurenka, amma ina mai roΖon wata alfarma a gareka”….”Dan Allah kada ka wulaΖantani aduk yanda kasameni, kada kuma ka tozartani, nasan cewa tausayina yafi yawa acikin zuciyarka fiye da soyayya ta, saboda haka ina da tabbacin cewa ko gaba zaka iya sake samun wata mace,wacce itace zata kasance zaΙinka, kada haka yasa ka wulaΖantani dan Allah, kada kuma kacutar da rayuwata!” cikin sanyin murya ta Ζare maganarta ta, yayinda hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta,suna sauΖa akan Ζuncinta.
Jiyayi gaba Ιaya wani irin matsanancin farinciki ya lulluΙesa, gani yake tamkar wasa Zahrah take masa, amma kuma ba’abun mamaki bane, saboda babu abun da yagagari Allah.
“Bansan ta’ina kokuma tayaya zan fara godemiki ba Zahrah, kin gusarmin da duk wata damuwa dake damuna, kinbani farinciki cikin Ζ΄an mintuna Ζalilan, kiyarda dani Zahrah, inamiki Soyayyace ta gaskiya bawai, irin soyayyarnan tako oho ba, zan’iya sadaukar da duk wani abu nawa akanki Zahrah, soyayyar da nake miki, yasanya bana ganin laifi ko kuma aibun duk wani abun da kikamin, burina da fatana shine murayu tare dani dake amatsayin miji da mata, kuma aΖarΖashin inuwa Ιaya, Inasonki Zahrah, kuma namiki alΖawari komai wuya komai tsanani bazan taΙa gujemiki ba, ZANRAYU DAKE Zahrah!!” Dr Sadeeq yafaΙa cike da matsanancin farinciki, jiyake tamkar yajawo Zahrah jikinsa yabata kyakkyawan runguma.
Kuka Zahrah ta fashe dashi, wanda batasan dalilin yinsaba, ita ta amincewa kanta cewa zata auri Dr Sadeeq amma saitakeji tamkar dole tayimawa kanta.
Batayi zato ba saiji tayi Dr Sadeeq yajawota jikinsa haΙe da sanya hannayensa duka biyu ya rungumeta. “Inasonki Zahrah, kuma nayi maki alΖawarin bazantaΙa wulaΖanta ki ba har’abada, kidaina kuka kinji princess Ιina!” yaΖare maganar tasa cikin sigar lallashi.
DaddaΙan Ζamshinsa shiyaso birkita mata tunani don haka tayi saurin janyewa daga jikinsa, tana mai yin Ζasa da kanta.
Sam shikam ma yamanta da cewa hakan da yayi ba’abu bane mai kyau, gaba Ιaya murna yacika masa zuciya.
“Uh sorry baby, gaba Ιaya kece kikamantar dani komai!!” Dr Sadeeq yafaΙi hakan yana mai dafe goshinsa.
Ζasa Ζasa Zahrah tayi murmushi haΙe da kawar da kanta gefe, hakanan taji wani irin nauyin Dr Sadeeq Ιin yaΖaru acikin zuciyarta, haka kuma yaΖara girma acikin idanunta.
Wani irin kallo Dr Sadeeq yashiga yimawa Zahrah duk dacewa takau da kanta gefe, sai yanzu nema yake Ζara ganin haΙuwarta fiye da da, tabbas da Zahrah bata amince dashi ba to da ya tabka babban rashi, domin kuwa Zahrah tahaΙu, macece ita da kowanni Namiji zaiyi fatan mallaka.
STORY CONTINUES BELOW
Sam batayi tunanin kallonta yake ba, don haka taΙan juyo dan itama ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauΖa akan najuna, da sauri Zahrah tayi Ζasa da kanta haΙe da cusa fuskarta tsakan kanun cinyoyinta.
Dariya Dr Sadeeq yayi cike da shauΖi haΙe da shafa sajen dake kwance akan fuskarsa. “Yaushe kika farajin kunyana? lallai zamu Ιata idan harkinajin kunyana!” ya faΙi hakan cike da zolaya.
Ζan Ζaramin bakinta taturo gaba, haΙe da marairaice fuska cike da shagwaΙa tace “To bakaine kaketa kallo na ba, saikace baka sanni ba!”
Lumshe idanunsa yayi haΙe da buΙesu a lokaci guda, irin wannan salon shagwaΙan ai saita sashi bacci batare da yashiryawa hakan ba,lol.
“Ki faΙamin laifi ne don nakalli abar sona? saidai kiyi haΖuri amma kallonki yanzuma na fara, tunda kinamin kyau, kina kuma burgeni!” yanayin yanda yayi maganar abun burgewa ne, ga macen da tasan daΙin soyayya.
“Nidai kada ka wani ce inada kyau, daΙin bakine kawai nasan kakemin!” still da yanayin shagwaΙa tayi maganan.
Lumshe idanunsa yayi haΙe da fitar da iskan numfashi daga bakinsa, yanayin shagwaΙan Zahrah yafi komai burgesa a tattare da’ita, haka kuma sosai yake sauΖar masa da kasala. “Princess!!” yaΖira sunanta dawani irin murya mai taΙa zuciya.
A hankali ta Ιago idanunta ta kallesa, batare da ta amsa masa ba, ganin idanunsa a rufe, yasanya taΙan tsaya Ζaremawa fuskarsa kallo. “Duk kallona Ιaya da zaki yi bazai tafi a banza ba, sai kin biya kuΙi, gwamma ma kisani!” Dr Sadeeq yafaΙi haka batare da ya buΙe idanunsa ba.
Saurin Ιauke kanta tayi daga kallonsa haΙe da cewa “Niba kallonka nake ba”
“Zaki iya rantsewa cewa bani kike kallo ba?” yaje fo mata tambayar da batayi zato ba.
kanta tashiga girgizawa haΙe da cewa “Ai bankalleka sosai ba, kaΙan nakalleka!”
Dariya Dr Sadeeq yasanya wanda harsaida dimple Ιinsa suka bayyana, yanzu yayarda cewa Zahrah yarinyace Ζarama, kuma zakayi saurin kamata idan tamaka laifi.
ΖoΖarin buΙe murfin motar Zahrah tasomayi, cikin mamaki Dr yace “ina zaki?”
“Zankoma gida ne, dama magana zan faΙa ma, shiyasa na Ζiraka, kuma nafaΙa ma, inada karatu, gobe muna da test a makaranta” Zahrah tafaΙi hakan dai dai lokacin da ta gama sanya Ζafafunta waje.
“Shikenan to My Princess kikulamin da kanki kinji, inasonki sosai!” Dr Sadeeq yafaΙa cike da kulawa.
Wani irin muguwar kunyarsace takama Zahrah, bashiri ta wuce cikin gida tana mai rufe fuskanta da tafukan hanunta.
Shima Dr Ιin murmushi yayi cike da jindaΙi, lallai idan ya auri Zahrah yakasance mutum mai sa’a, acikin satinnan insha Allah, zai sanarda Ζanin mahaifinsa azo a nemamasa auren Zahrah, a wajen Baffa.
“Aurenka da Salima fa?” Wata zuciyar ta jefo masa wannan tambayar, wani irin bugawa yaji Ζirjinsa yayi, gaba Ιaya amincewa dashi da Zahrah tayi yasanyashi manta halin da yake ciki na batun auren sa da Salima. Jiyayi gaba Ιaya jikinsa yayi sanyi, tabbas akwai Ζalubale a gabansa, domin kuwa yanada tabbacin cewa Hajiyarsa bazata taΙa sanja maganarta ba, gashi har ansoma shirye shiryen bikinsa da Salima, kuma shi a tsarinsa bai sha’awar auren mata biyu, Zahrah ita kaΙai ta’ishesa rayuwa, amma kuma tabbas yasan zai fuskanci matsaloli da yawa daga Ζ΄an uwansa, matuΖar ya jajirce akan cewa Zahrah yakeso ba Salima ba, to amma dole zai jarraba sa’ansa, domin a gaskiya baijin cewa zai’iya haΖura da Zahrah.
Cike da sanyin jiki yayimawa motar tasa key, haΙe da nausawa kan titi.
Suna isa katafaren gidannasu, adai dai parking space motar tasu ta tsaya.
Bawani jinkiri Zaid yabuΙe murfin motar yafito, batare da yatsaya sauraran Mahaifinnasa ba, yanufi Ιangarensa kai tsaye.
STORY CONTINUES BELOW
Komai dake cikin Ιangaren nasa a gyare yake tsab, tamkar akwai wani wanda ke rayuwa a cikinsa, hakan kuma yasamo asaline da yawan gyara part Ιin da akeyi duk bayan kwana biyu, kasancewar Zaid mutum ne da bayason Ζazanta.
Direct bedroom Ιinsa yanufa, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, rigan wanka irin na maza mai gashi gashi a jiki yasanya, haΙe da sanya badroom slippers a Ζafafunsa, kai tsaye wajen fridge Ιin dake aje cikin Ιakin yanufa, maltina can yaciro haΙe da Ιalle Ιan Ζarfen da aka rufe bakin can Ιin dashi, yakai bakinsa, tunda yakai maltina can Ιin nan bakinsa bai Ιauke ba harsaida yatabbatar da cewa bakomai ciki ya shanye, cikin dustbin Ιin dake aje a Ιakin ya jefa can Ιin. Bathroom ya wuce haΙe da sakarmawa kansa shower. Wanka yakeyi amma gaba Ιaya tunaninsa baya garesa, yanaga shugar baby’nsa, amatuΖar matse yake da sha’awarta, haryanajin bazai iya daurewa yakai zuwa wani Ιan lokaci mai tsawo batare da’ita ba.
Bayan yafito a wanka yashiga shirya kansa cikin, haΙaΙΙun riga da wando masu kyau da tsadar gaske, gaskia komai na Zaid me kyau ne, domin kuwa kowani kaya yasanya saiya yi kyau, bakuma kayanne yake masa kyauba, shi Ιin kansa ne yake mawa kayan kyau,lol.1
HaΙaΙΙen takalminsa sau ciki Ζiran kamfanin Gucci yasanya, aΖafansa, bayan ya Ιaura tsadadden agogon nan na Rolex a hanunsa mai kyau da burgewa. DaddaΙan Ζamshi ne kawai ke fita daga jikin shi, Ζamshine mai wahalar mantawa.
Black facing cap, yasanya akansa, domin kuwa yanayin garin ana Ιan busa sanyi, duk dakuwa cewa daga cikin sanyin yafito.
Wayarsa yaΙauka haΙe da car key Ιinsa, kai tsaye yafice daga cikin Ιakinnasa. Ζangaren Mom Ιinsa yanufa. Hajiya Safara’u ne tsaye a gaban Ζatoton teburin cin abinci, yayinda Alhaji Ma’aruf ke zaune tana serving Ιinsa, batasan da shigowarsa ba saiji tayi ya rungumeta ta baya haΙe da Ιaura kansa akan kafaΙarta, cike da soyayyar mahaifiyarta sa yace “Barka da gida Momy!”
Cike da tsananin farinciki itama ta rungumesa haΙe da basa sumba a kan kumatunsa, “Barkanka da dawowa my son, ya gajiyar hanyar?”
“Alhmdlh!” Zaid yafaΙa a taΖaice, bayan ya janye jikinsa daga na mahaifiyartasa. ΖoΖarin juyawa yakeyi, Mom tace “Inakuma zaka my son ba abinci kazo ciba?” cike da kulawa ta tambayesa.
Ζan Ιata fuska Zaid yayi haΙe da cewa “Banajin yunwa Mom, idan nadawo zanci!” baijira jin maizasu ceba yasakai yafice daga cikin falon.
Da kallo kawai Mom tabisa har yafice, fuskarta Ιauke da damuwa, itakam ta rasa wani irin haline da Zaid, sam ba’a iya gane gabansa da bayansa.
“Miye abun shiga damuwa Hajiya Safara’u? zuwa yanzu yakamata ace duk wani hali na yaronnan Zaid kin gama saninsa!” Alhaji Ma’aruf yafaΙi hakan cike da nuna kulawa ga matar tasa.
“Nasan halinsa Alhaji, amma kuma ace mutum shi baya taΙa sanjawa, ko da yaushe fa Zaid bayason zama a cikin mu, sannan kuma sam baya sakewa damu!” Mom tafaΙi hakan cike da damuwa.
“Zauna muci abincin mu, aishi ba Ζaramin yaro bane, yasan me yakeyi!” Alhaji Ma’aruf yafaΙi hakan yana mai kama hanun Mom yazaunar da’ita a kusa dashi.
Zaid kuwa yana fita daga Ιangaren mahaifiyartasa, kai tsaye wajen motarsa yanufa, koda driver yanemi da yabarsa ya tuΖasa, Ιaga masa hanu yayi alamar baya buΖata, shida kansa yayimawa motar key, ya harbata zuwa kan titi.
Tafiya yake cikin nutsuwa yayinda airpiece ke saΖale a kunnuwansa, wayarsa ce tasoma Ζara alamar shigowar Ζira, ganin cewa babban manager’n company’nsa dake nan gida Nigeria ne ke Ζiransa yasanya shi Ιaga Ζiran. Banji mai Manager’n nasa yace masa ba, sai gani nayi ya’aje wayan, haΙe da buga dogon tsaki, lokaci Ιaya yakarkata akalar motar tasa zuwa wata hanya daban saΙanin hanayar daya nufa, wanda zai sadasa da unguwar su Zahrah.
Dr Sadeeq kuwa yana barin unguwar su Zahrah kaitsaye gidansu yanufa, acewarsa gwamma yayi maganin matsalarsa tunkafun tayi nisa.
Usaina mai aikin Ιangaren Hajiyarsa yasanya tane ma masa iso awajen Hajiyar tasa, domin kuwa bai isketa a falo ba.
Da sallama yashiga cikin Ιakin Hajiyar tasa, fuskarta Ιauke da fari’a ta amsa masa sallaman da yakeyi. Zaune take akan gado, yayinda take duba wasu kayayyaki dake zube a gabanta.
“Barka da huwatawa Hajiya!” yafaΙa cike da ladabi.
“Yauwa barkanka, kamar kuwa kasan ina nemanka, wai me kake nufi da auren nan ne Sadeeq? har yanzufa banga kana wani cuku cuku ba, kayan lefe ma saini kabarmawa Ιawainiyar haΙasu, gashi kuma Salima tacemin tunda kaje sau Ιaya baka sake zuwa ba, mai ke damunka ne wai?” Hajiya tatambayesa cike da kulawa.
Kansa yashiga sosawa haΙe da sake yin Ζasa da kansa, “Am…dama Am….” “Dakata banson wani kwana kwana, kafaΙi abunda zaka faΙa kai tsaye kawai” Hajiya ta katsesa daga kame kamen maganan dayake ΖoΖarin yi mata.
“Hajiya kamar dai yanda na faΙamiki ne, wallahi Hajiya dagaske nake, yanzu nasamu wacce nakeso kuma idan harkin yarda aurenmu bazai wuce nan da Sati uku ba, kamar yanda kikeso!” yafaΙi hakan cike da ladabi.
Sororo haka Hajiya ta tsaya tana kallonsa, “anya kuwa Sadeeq yana lafiya? ” tatambayi kanta.
“Inagadai bakasan mekake cewa ba Sadeeq, wato nikakeson watsamawa Ζasa a cikin idanu ko, ya yi maka kyau, to inaso kabuΙe kunnuwanka da kyau ka saurareni, wallahi ko da wasa kakuma zuwamin da irin wannan zancen saina Ιata maka rai, nagama baka duk wata dama dazan baka, bakuma zan sake baka wata daman ba, tashi kabani waje, tunda nalura kai baka da tunani!” Hajiya ta Ζare maganan cikin faΙa.
Cikin rashin kuzari haΙe da sanyayewar guiwa Dr Sadeeq yamiΖe daga gaban mahaifiyartasa, haΙe da nufar Ζofar fita daga cikin Ιakin,
Saida yakai ΙaΖin Ζofar fita ckafun yatsaya cak, haΙe da juyo da kallonsa ga Hajiyar tasa cikin murya mai rauni yace “Hajiya dan Allah..”
“Fita kabani waje nace!!” Hajiya takuma faΙa cikin Ιacin rai tanamai yi masa nuni da Ζofar fita daga Ιakin…Cikin sanyin jiki Dr Sadeeq yafita daga cikin Ιakin mahaifiyarta sa. Gaba Ιaya jiyayi zuciyarsa ta cika da Ζunci. Yana isa Ιangarensa ya zube akan Ιaya daga cikin kujerun falonnasa, “yanzu wazai je yasamu da wannan matsalar? tabbas yasan Hajiyarsa mutum ce mai kafiya, idan tace eh zai yi wuya ta dawo tace a’a”
hanunsa yasanya cikin sumar dake kwance akansa haΙe da yamutsa ta, sunan Aunty Raliya ce yafaΙo masa arai, tabbas ita kaΙaice Ζ΄ar uwarsa da zai kai mata matsalansa har ma ta tayasa magancewa, sai dai kuma yanatunanin itama ra’ayinta Ιayane da Hajiya, amma yasan idan yayi mata kyakkyawan bayani zata fahimcesa, zumbur yamiΖe daga zaunen dayake.
Ko bedroom baishiga ba yakuma ficewa daga cikin falon, mota ya koma, haΙe da kunnata, mai gadi ne ya wangale masa gate Ιin gidan yafice.
Hajiya najin Ζarar ficewar motarsa daga cikin gidan ta sauΖe ajiyar zuciya.
“Gaba Ιaya tunaninta ya kulle, batasan wani irin abu Sadeeq keshirin shigo mata dashi cikin gida ba, kusan sau uku kenan tana bashi dama, akan yafito da matar aure, amma dazaran lokacin da ta ibar masa yacika, sai ya farayi mata kame kame, yanzu da tagaji da sakarcinsa ta zaΙa masa mata, sai yake nema yawatsa mata Ζasa a idanu, bakuma zata lamunci hakanba.
Direct Dr Sadeeq gidan Aunty Raliya yanufa, domin baida wata Ζ΄ar uwa da ta wuce ta a duniyar nan.
Yanashiga gidan tunbai gama fitowa daga cikin motarsa ba, su Meenal da Affan Ζ΄aΖ΄an Aunty Raliya, suka rugo da gudu zuwa garesa, dama wasan ball suke a farfajiyan gidan nasu, hakan yasa duk wanda yashigo da kuma wanda zaifita zasu gansa.
Rungumesu yayi a jikinsa, haΙe da shafa kawunansu, “Oyoyo babies Ιina, ashe girma yazo muku, har wasan ball kukeyi!” yafaΙi hakan cike da nishaΙi.
“Eh Uncle ai harma nafita iyawa!” Affan yafaΙi haka cike da zumuΙi.
“Ζaryayake Uncle baifini iyawa ba” Meenal tafaΙi hakan tana mai kama Ζugu, alaman Ζarya Affan Ιin yakeyi.
Murmushi kawai Dr yayi haΙe da sake shafa kansu, “kuyi wasa da kyau, idan nafito zan baku alewa!” yafaΙa yana mai nufar kofar da zata sadashi da babban falon gidan. Yayinda yabar su meenal sunata tsallen murna saboda yace zai basu alawa.
Da sallama Ιauke a bakinsa yashiga cikin falon.
Aunty Raliya dake zaune tana kallon tv, ta amsa amsa masa sallamar tasa, fuskarta Ιauke da fari’a, haΙe da yi masa iso.
Ζarasowa yayi yazauna akan kujera, haΙe da sauΖe ajiyar zuciya, gaba Ιaya a gajiye yakejinsa, domin tun safe yau baisamu nutsuwa ya huta ba.
Aunty Raliya da kanta, ta jere masa kayan fruit da juice agabansa, cikin tsokana tace dashi
“Ango kasha Ζamshi, duk gajiyar shirye shiryen bikinne haka?”
Ζan Ιata fuska yayi haΙe da Ιaukan apple Ζwaya Ιaya ya kai bakinsa.
“Ango labari ya sauya salo” yafaΙi hakan bayan ya cinye gutsuren apple Ιin dake bakinsa.
Cikin mamaki Aunty Raliya tace “bangane ba mekake nufi?”
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya yasauΖe haΙe da gyara zamansa.
“Akwai matsala Aunty!” yafaΙi hakan lokacin da gaba Ιaya yanayin fuskarsa ya sauya.
“Matsala! wace irin matsala Uncle?” Aunty Raliya tatambaya cike da Ιaurewar kai.
“Akwai wacce nakeso na aura, yarinyar tana matuΖar buΖatar taimakona, nayi ΖoΖarin na fahimtar da Hajiya hakan, amma taΖi saurarata, yanzu haka daga gida nake, nasoma yi mata bayani, tace natashi na bata waje, gaba Ιaya kaina yakulle bansan yazanyiba Aunty Raliya!”
Ya faΙi haka cikin damuwa.
ΖaΖΖarfan ajiyar zuciya Aunty Raliya ta sauΖe “TurΖashi, lallai kuwa kazo da babbar magana, amma maiyasa tunda baka bayyana wacce kake so Ιinba, sai yanzu da komai yariga da yayi nisa? kafasan Hajiya da kafiya balallai ne ta fahimce ka ba, shawarata a gareka shine, kamabar wannan zancen, domin balallai kasamu abun da kakeso ba!” Aunty Raliya tafaΙi hakan da’iyaka gaskiyarta.
Cike da rauni Dr Sadeeq ya kalli Yayartasa. “Dan Allah taimakona zakiyi Aunty, kije kisameta kibata baki, wallahi inamatuΖar son Zahrah, sannan kuma yarinyar tana buΖatar kulawata, nikaΙai nasan matsalarta, please Aunty!!” yafaΙi haka yana me marairaice fuska, hadda haΙa hannuwansa biyu ga Aunty Raliya’n alamar roΖo.
Kallon mamaki Aunty Raliya tashiga binsa dashi, “wai yaushe Sadeeq yazama bawan soyayya ne?” ta tambayi kanta.
“Abune me matuΖar wuya amincewar Hajiya, amma zan jarraba, saidai kafun naje gareta, dole sainasan wacece yarinyar kuma su waye iyayenta, saboda kada aje Hajiya ta amince, akuma zo asamu wani mummunan labari akan ta”
Wani irin bugawa Ζirjin Dr Sadeeq yayi, domin kuwa anzo wajen, lallai baizama dole kowa yafahimcesa ba domin sanin sirrin Zahrah, zai iya sanyawa kowama yaΖi amincewa da aurensa da’ita, wanda shi a wajensa baiga ta’inda aurensu zai zamanto rashin dacewa ba, amma ba’a Ζ΄ar Ιoye a harkan aure, domin koda anΙoye tofa sai ya bayyana.
“Sunanta Zahrah, a unguwar Maraba take, sannan kuma marainiyace bata da uwa bata da uba, baffanta ne yake riΖonta, yarinyar tana da hankali sosai Aunty, sannan kuma tana da tarbiya, bata da wani aibu ko abun kushewa a tattare da’ita, saidai kuma…” kasa Ζarasa maganar yayi, domin kuwa baisan yanda yayartasa zata Ιauki maganar ba.
“Umm inajinka saidai kuma me?” Aunty Raliya tatambayesa cike da zaΖuwa.
“Ζaddarace kuma tana kan kowa, haka kuma babu wanda ya’isa ya tsallake mata idan har tafaΙo kansa, akwai wani tsohon saurayinta da ya yaudareta yayi mata fyaΙe, watannin baya da suka wuce, wanda hakanne ma sanadin haΙuwata da’ita, amma ni banΙauki hakan amatsayin wani abu ba dazai hanani aurenta, kasancewar kowa da’irin tasa Ζaddaran a rayuwa!”
Sororo haka Aunty Raliya ta hangame ido da baki tana kallon Dr Sadeeq har ya idar da zancensa mai kama da tatsuniya.
Salati Aunty Raliya tasanya cike da tsantsar mamaki haΙi da al’ajabi, lallai Sadeeq baisan meyake faΙa ba.
“FyaΙe! fyaΙe fa kace Sadeeq, anya kuwa kansan mekake faΙa? yanzu kai saboda rashin hankali irin naka, karasa wacce zaka gani kace kanaso, sai yarinyar da taraba budurcinta wa Ζattin maza, yarinyar da wani yagama sanin sirrinta!” Aunty Raliya ta faΙi haka cike da Ιacin rai.
Saurin rumtse idanunsa yayi domin jin magananganun Aunty Raliya’n yake tamkar sauΖan aradu, a kunnuwansa.
Cigaba tayi da cewa ” Lallai yanzu na tabbatar dacewa ba lafiyanka lau ba, taya kana cikekken namiji mai hankali da kuma kamala, karasa wacce zaka aminta da ta zamo uwar Ζ΄aΖ΄anka sai wacce wani Ζato ya haiΖemawa, yazama dole kasanja tunani Sadeeq, wannan ma ai zancen banzane, to gwarama kasani wannan yarinyar ba zaka taΙa aurenta ba matuΖar mu jininka ne!” Aunty Raliya ta Ζare maganar cikin hargowa.
STORY CONTINUES BELOW
“Haba Aunty maikikeson cewa ne? dan Allah kada kimin haka, nafaΙamiki matsalatane don bani da wacce tafiyemin ke, dama nasan za’a samu rashin fahimta, domin zakuga kamar Zahrah ba kamemmiyar mace bace, alhalin kuma bahaka take ba, tsautsayine yafaΙa mata, amma ni nayarda na amince zan aureta a haka, kada fa kimanta duk wanda yarufa asirin wani to Allah zai rufa masa nasa asirin, kitaimaka mu inganta rayuwar Zahrah, kitaimaka mucireta daga Ζunci, musanyata cikin farinciki!” yafaΙi haka cike da rauni.
Wani irin kallo Aunty Raliya tashiga yimasa, lallai Sadeeq baya cikin hankalinsa.
Murmushi mai ciwo Aunty Raliya tayi haΙe da cize laΙΙanta cikin takaici ta ce dashi.
“Kuskurenka na farko a rayuwa shine yarda dakayi cewa da gaske fyaΙe aka mata, shin ka ko san Ζ΄an matan yanzu kuwa Sadeeq? to bari kaji wani abu, a shegen son kuΙi irin na Ζ΄an matan yanzu, su da kansu suke saida budurcinsu ga wani daban, idan suka samu makahon da’idanunsa ya rufe ruf har yazo musu da zancen aure, sai su taΖarΖare su zabgamasa Ζarya kan cewa fyaΙe akamusu, bayan suda kansu suka kasa budurcin nasu a faifayi suka kai tallanshi kasuwa, ni Ζ΄ar uwarka ce ta jini bazan taΙa son wani abun da zai cutar da kai ba, saboda haka tun muna mubiyu nidakai, mubunne maganarnan anan, tun kafun ma yaje ga kunnen Hajiya, domin kasan idan taji cewa wacce kake shirin kawo mata ita amatsayin suruka, ba mutumiyar Ζwarai bace to zatayi mugun saΙa maka!!”
Take idanun Dr Sadeeq suka kaΙa sukayi ja, bakomaine ya sanya hakan ba face irin munanan kalaman da Aunty Raliya ta dinga jifan Zahrah dashi, tabbas yasan cewa mafi Ζ΄awancin Ζ΄an matan yanzu suna sayarda budurcinsu saboda abun duniya, amma banda Zahrah’nsa aciki, yasan Zahrah macece mai kamun kai, kuma duk wanda yayarda da Ζaddara dole ne ya tausayawa mata masu tsintar kansu a irin halin da Zahrah ta tsinci kanta a ciki.
“Ita bakamar yanda kike tunani bane Aunty Raliya, ki saurareni saina baki gaba Ιaya labarinta, marainiyace ta cancanci a tausaya mata, nima Namiji na tausaya mata balle ke mace, kuma dama ance ciwon Ζ΄a mace na Ζ΄a mace ne!” Dr yafaΙi hakan cike da son ganar da Yayarta sa, cewa ba bu wani aibu agame da aurensa da Zahrah.
Gaba Ιaya duk iya abun da yasani agame da Zahrah, bai Ιoye mata ba, sai da yasanar mata, atunaninsa hakan zai sanya Aunty Raliya ta Ζaunaci Zahrah, amma me sai gani yayi tana taΙe baki haΙe da kawar da kanta gefe alamar ma ta’inda maganar tasa take shiga tanan take fita.
Yana idar da zancen ta dubeshi haΙe da Ιata fuska tace “Kagama? kai a tunaninka zaka bani wata hujja dazata sanya naga dacewar aurenka da’ita ne, hmm niba yarinya bace Sadeeq, yakuma zama dole kasanja tunani, kakuma manta da maganar wata wai ita Zahrah, idan kuma kafison kafuskanci Ιacin rai daga wajen Hajiya, to kaci gaba da zama akan bakan ka harmaganan takai ga kunnen Hajiya!!” tanakaiwa nan a zancenta ta miΖe fuuu tawuce cikin Ιakinta tabarshi zaune.
Hannayensa yasanya duka biyu ya tallafi kansa, lallai akwai babban Ζalubale a gareshi, agun Aunty Raliya ma kaΙai ga’irin Ιacin ran daya fuskanta, inaga Hajiyarsa kuma.?
MiΖewa yayi daga zaunen da yake tamkar wanda Ζwai ya fashewa a jiki haka yake tafiya, gaba Ιaya ΖwaΖwalwarsa tasake dagulewa, yazone don yasamu mafita amma sai gashi abubuwa sun sake dagulewa.
Da Ζyar yake iya tuΖa motar tasa. Haka yanufi gida cikin rashin kuzari, sai dai fa haryanzu bai saduda da maganar Auren Zahrah ba, yanaji ajikinsa cewa Zahrah zata zamo matarsa Insha Allah.
Gagarumin meeting su ZAID suka gudanar mai zafi, a babban hotel Ιin nan wato SHERATON, sosai aka samu riba dakuma Ζarin buΙi a Ιaya daga cikin company’n nasa da suke Nigeria, hakan yasa yaΖarawa gaba ΙaΖ΄a ma’akatansa albashi.
Sunjima suna meeting Ιin dan haka amatuΖar gajiye suka fito dukansu, lokacin har dare yasoma rufawa. Kallon agogon dake Ιaure a tsintsiyar hanunsa, yayi yaga karfe 6 daidai na yammaci, Ιan Ζaramin tsuka yayi haΙe da soma yunΖurin cire rigan suit Ιin jikinsa wada yaΙaura akan kayan dake jikinsa,
saboda gajiyan da yayi bai iya tuΖi da kansa ba, sai driver’nsa yaΖira yayi driving Ιinsa.
STORY CONTINUES BELOW
Gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran motar haΙe da lumshe idanunsa, wani irin sarawa kansa keyi masa, daga wani Ιangare na zuciyarsa kuwa sosai meeting Ιinnan ya Ιata masa rai, domin kuwa ya hanasa Ζarasawa ga ZAHRAH’nsa, wacce saboda itane ma gaba ki Ιaya yadawo Ζasar, yayi missing din Zahrah sosai, yayi missing kyakkyawan murmushinta haΙi da kyawawan idanunta, yayi missing kallon kyawawan laΙΙanta masu daΙin tsotso. Gaskiya dole ya killace Zahrah tayanda zata zama nasa shi kaΙai.
Suna isa gida kai tsaye Ιangarensa ya wuce, a gajiye yashiga bathroom yayi wanka, koda yafito a wankan, direct masallaci ya wuce donyin sallan magriba. Sai da yajira aka yi sallan isha tare dashi a masallaci, kafun ya siΙaΙo yadawo Ιaki ya kwanta, yau ko abar Ζaunar tasa wato wine baisha ba bacci Ιarawo yayi gaba dashi.
Zahrah ce kwance akan katifarta sai juyi take ta kasa bacci, gaba Ιaya kanta ya kulle zuciyarta cike take da tarin tunanuka kala kala. “Anya banyi sauri kokuma gangancin yarda da kuma amincewa da soyayyar Dr da nayi ba?” zuciyarta ta tambayeta.
Zumbur haka ta miΖe zaune, haΙe da soma girgiza kanta
” A’a banyi kuskure ba, tabbas bayan shi babu wani maiso da nuna tausayi gareni!” tabawa kanta amsa a bayyane.
Wayartace takawo haske alamar shigowar Ζira, kasancewar ta sanya wayar a silent hakan yasanya wayar batayi Ζaraba.
“Doctor” shine sunan dake yawo akan screen Ιin wayar.
“Shima baiyi bacci ba kenan” tafaΙi hakan a bayyane.
Saida wayar ta kusa katsewa kafun Zahrah ta Ιaga Ζiran haΙe da kara wayan akan kunnenta.
“My princess bakiyi bacci ba kenan?” Dr Sadeeq yatambayeta cikin muryarsa mai Ιauke da damuwa.
“Um, kaifa me yahanaka bacci” Zahrah itama tatambayeshi.
“So da Ζauna dakuma tunaninki susuka hanani bacci! kefa mai yahanaki bacci?” yatambaya cike da son jin amsar da zata fito daga bakinta, “Allah yasa itama tunani na ne ya hanata bacci” yafaΙi hakan a zuciyarsa.
Kunyane yaΙan kamata amma sai ta basar haΙe da sauΖe ajiyar zuciya “A’a nikam karatu nake, shiyasanya banyi bacci ba, amma yanzuma zanyi baccin.” tafaΙi hakan a taΖaice.
Ko kaΙan baiji daΙin amsar da ta basa ba, amma yasan cewa wataran dole zatayi tunaninsa kamar yanda shima yake nata tunanin.
“Naji daΙi sosai da kika amince dani Zahrah na! hakan yasa na Ζara jin sonki sosai da sosai a cikin zuciyata!!” cikin shauΖin so yafaΙi maganar.
“Umm banji mai ka faΙa ba!” Zahrah tafaΙi hakan cikin wani irin salo wanda batasan ma tayi shi ba, duk da kuwa cewa taji mai yace, iskancine kawai irin nata.
Lumshe idanunsa yayi da suka soma sauya kala, sosai yanayin yanda tayi maganar ya sauΖar masa da kasala.
“Bacci kika farane Zahrah na?” yatambayeta cike da kulawa, domin kuwa shi anasa zaton dagaske batajisa ba.
“Um!” Zahrah ta basa amsa a taΖaice cikin Ζasa Ζasa da murya, domin kuwa tanaso yayarda cewa baccin takeji, saboda har yanzu, bata gama amanna dacewa sonsa take ba, kuma koda za’a kasheta tasan cewa ba sonsa take ba, kawai dai ta tsinci kantane da amince masa, amma batun soyayya kam babu shi.
“To kiyi bacci mai daΙi kinji My princess, inasonki sosai, ki kulamin da kanki, banson koda Ιigon wani a bune ya raΙe ki!” Dr ya faΙi haka cikin shauΖin SO (Sisters kujisafa su likita ashe an iya kalaman love, lol.)
“Uhumm sai da safe.” Zahrah tafaΙa a taΖaice bayan ta zare wayar daga kunnenta.
“Gaskiya abune mai matuΖar wahala koyawa zuciya So’n abun da bata so, ya Allah kataimakeni, haΖiΖa banajin tsanarsa haka kuma banajin soyayyarsa a zuciyata, sannan kuma inaji ajikina cewa zan’iya rayuwa dashi, to me hakan ke nufi, ba so bane kuma ba Ζi bane to menene?” tatambayi kanta a bayya ne, saidai kuma bata da amsar da zata bawa kanta.
Komawa tayi ta kwanta bayan ta kashe wayarta ta gaba Ιaya.
Cike da saΖe saΖe bacci yayi awungaba da ita.
Ζangaren Dr Sadeeq ma, sai da yajima yana saΖawa da kuncewa, ba abun da yake Ιaure masa kai, kamar yanda ya kasa fahimtar cewa Zahrah, na son sane ko bata sonsa. da Ζyar dai shima bacci ya’iya Ιaukarsa.
Washe Gari.
Yau tun saven thirty suke da lecture, dan haka da wuri tasoma shirya kanta, sosai tayi kyau cikin shigar jar abaya haΙe da jan hijab Ιin dake jikinta, hand bag Ιinta ta rayata a bisa kafaΙanta. Kana tafice zuwa tsakar gida. Zama tayi akan taburma haΙe da jawo farantin Ζosai da kuma kofin kunun da Inna ta aje mata tasoma sha. Baffa ne yafito daga cikin Ιakin sa yanaganin Zahrah yace
“Yauwa kinfito ko, tun Ιazu kuwa likita yake jiranki a waje”
“Eh Baffa nafito” tabashi amsa cike da mamakin jin cewa wai Dr yajima da zuwa, yanama jiranta a waje, amma kuma bai Ζira ta a waya yasanar mata ba.
AΖagauce taci abincin kasancewar har bakwai tayi.
Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushi, itama murmushin ta sakarmasa bayan tagama Ζaremawa kwalliyarsa ta yau kallo.
“Kinyi kyau my princess!” yafaΙa cike da nishaΙi, domin kuwa sosai tayi masa kyau, jan kayan da tasa ya karΙi kalan fatarta.
“Kaima haka” tabashi amsa a taΖaice.
Murmushi yakumayi haΙe da buΙe mata murfin motar nuni yayi mata da hanunsa alamar tashiga, wani murmushi mai tsayawa a zuciya tayi masa haΙe da shigewa cikin motar tayi mawa kanta mazauni.
Tafe suke suna hira cike da nishaΙi, wanda gaba Ιaya yawan hiran Dr ne maiyi mata shi.
A haka har suka iso cikin makarantar, ΖoΖarin buΙe murfin motar ta soma yi.
“Ya haka? baki sallameni ba fa, kike ΖoΖarin tafiya” Dr Sadeeq yafaΙi hakan cikin sigar zolaya.
Murmushi Zahrah tayi masa haΙe da yin fari da’idanunta “Bangane ba” tafaΙi haka cikin salo.
Lumshe idanunsa yayi haΙe da sanya hanu yashafi sajensa, “Inanufin bakice kina sona ba”
Dariya haΙe da kunyane suka kama Zahrah sai kawai ta buΙe murfin motar tayi ficewarta, domin kuwa bazata iya masa abun da yakeso ba.
Saida yaga shigewarta cikin hall kafun yaΙauke idanunsa daga kanta, yanason mace mai kunya gashi Zahrah takasance me kunya. Cike da tarin tunaninta yabar cikin makarantar.
Ita da Husnah suna fitowa a lecture sukayi mawa kansu ma zauni a inda suka saba zama ko da yaushe.
Cike da tsananin farinciki Husnah tace “Naji daΙi Ζwarai Zahrah da kika amincewa Dr, wallahi gayen ya haΙu da yawa Ζawata, tabbas idan kika auresa kin more don nasan za kisha madaran soyayya!”
Hararan wasa Zahrah ta wurgamawa Husnah, cike da son basar da zancen tashiga shafa cikin ta ” Nifa yunwa nakeji” tafaΙa tana mai turo baki gaba.
“Kada dai kice zakimin sakalci, domin niba Doctor bane” Husnah tafaΙa cikin tsokana. dukan wasa Zahrah takai mawa Husnah, da sauri Husnah ta kauce.
Cafeteria suka nufa acan suka cika cikinsu, daganan suka sake shiga cikin wani lecture’n.
Jikin wata bishiya dake kusa da Ζofar fita daga makarantar yayi parking motar sa, gyara zama yayi haΙe da duba agogon dake Ιaure a tsintsiyar hanunsa. Kallonsa ya mayar zuwa bakin tangamemen gate Ιin makarantar tasu, hakanan yakejin ba zai iya fuskantar ta gaba da gaba ba.
AmatuΖar gajiye su Zahrah suka fito a lecture. Tare suke tafe ita da Husnah, domin yau zataimawa Husnah rakiya ne zuwa super market. kai tsaye suka nufi Ζofar fita daga makarantar kasancewa driver’n gidansu Husnah najiransu a waje.
Wani irin faΙuwar gaba taji, ya risketa adai dai lokacin da ta fito daga cikin makarantar.
Daga Ιanagaren Zaid kuwa zuciyarsa ne tashiga dukan uku uku, alokacin da’idanunsa suka sauΖa akan Zahrah, hanu yasa ya murje idanunsa domin tabbatarwa da kansa cewa ita Ιince kokuwa gizo idanunsa suke masa.
Tabbas itaΙince Zahrah’n sane, har yanzu tananan da kyawunta, dakuma surarta mai Ιaukar hankalin duk wani lafiyayyen Ιa Namiji.
“ZAHRAH!” yaΖira sunanta a bayyane, duk da kuwa yasan cewa bazata ji sa ba. dai dai lokacin daya soma yunΖurin buΙe murfin motarsa don yaΖarasa gareta, dai dai lokacin itakuma ta shige cikin mota tare da Husnah.Cikin Hanzari ya buΙe murfin motar tasa ya fito, sai dai baikai ga Ζarasawa garesu ba, motar su ta gangara kan titi haΙe da Ιaukar hanya.+
Hannayensa duka biyu yasanya ya kama Ζugunsa, haΙe da furzar da iskan numfashi ta bakinsa, sam baiso haka ba, amma babu yanda ya’iya dole binsu zaiyi.
Kallonsa yamaida ga sauran cincirindon Ιaliban da suke tsaye a bakin gate Ιin makarantar.
Gani yayi gaba Ιaya sun saki baki da hanci suna kallonsa, sai kace wanda suka ga baΖon halitta, bama kamar Ζ΄an matan dake tsaye a wajen.
Tsuka mai sauti yayi haΙe da komawa cikin motarsa, da gudun gaske ya cilla motar tasa kan titi, haΙe da rufa mawa motar su Zahrah baya.
“Yadai, naga lokaci Ιaya duk kinyi wata iri dake?” Husnah tatambayi Zahrah wacce tazama silently lokaci Ιaya.
A jiyar zuciya ta sauΖe haΙe da maida kallonta ga Husnah ” FaΙuwar gaba nakeji Husnah, ban kuma san dalilin hakan ba” Zahrah ta faΙi haka cikin damuwa.
“To fa, Allah dai ya tsare, amma ki yawanta addu’a, domin hakanne zaisa koma mene ne yazo da sauΖi” inji cewar Husnah.
“Insha Allah!” Zahrah tafaΙi hakan tana mai kwantar da kanta a jikin kujeran motar, tanajin Husnah tace da Driver’n ya karkata akalar motar, ta sanja shawara shoprite kawai zasuje, bamusu kuwa ya sanja hanya zuwa Shoprite Ιin. Itadai Zahrah batace dasu komai ba.
Basu wani jima suna tafiya ba, suka iso tangamemen Shoprite Ιin. “Muje ko” Husnah tace da Zahrah tana mai ΖoΖarin buΙe murfin motar.
Cikin sanyin jiki Zahrah, tafito daga cikin motar suka nufi cikin shoprite Ιin.
Basket biyu Husnah ta Ιauka nata Ιaya na Zahrah ma Ιaya, acewarta Zahrah ta zaΙi duk wani abun da take so, sam bahaka Zahrah tasoba amma babu yanda ta’iya, domin kuwa Husnah kafiya gareta, idan tace kayi abu tofa wai dole sai kayi.
Kayan shafa suka soma Ιauka, kafun suka garzaya zuwa kan su jaka da takalma Ζ΄an yayi, basu tsaya anan ba hadda kayan ciye ciye sai da suka Ιauka.
Cike da gajiyawa Zahrah ke tura Basket Ιin da kayanta ke ciki, ita mamaki ma take yanda Husnah tasa suka jidi kaya mai yawa har haka, amma idan tayi la’akari da irin gata da kuma kuΙin da mahaifin Husnah ke dashi, to sai tagama ba wani abun mamaki bane, kuma kuΙin kayan bazai mawa Husnah wahalar biya ba, domin kuwa anshagwaΙata sosai agida.
Daki daki aka lissafa kayan nasu, inda Zahrah ta Ιauki kayan dubu ishirin Husnah kuwa na dubu ishirin da biyar ta eba, ΖoΖarin miΖa wa Cashier ATM card Ιin dake hanunta Husnah ta soma yi. Amma sai Cashier’n yayi murmushi haΙe da cewa
“Ai Hajiya ba’a buΖatar kuΙin ku, domin kuwa an riga da an biya muku, tunkafun ku kammala sayayyan, sannan wanda yabiya muku yace idan ma kuna da buΖatar Ζari, to kukoma ku Ζara, duk shi zai biya kuΙin”
Cike da mamaki Zahrah da Husnah suka shiga kallon juna.
“Anbiyamana fa kace Cashier? shin ka kosan me kake cewa?” Husnah tatambayeshi cike da mamaki.
STORY CONTINUES BELOW
“Ζwarai kuwa nasan me nake cewa, kudai ku Ιau kayanku kawai kuje, sannan ku gode mawa Allah, don shi yaje fo muku tsuntsu daga sama gasashshe ” Cashier’n nan yafaΙi haka yana mai washe baki, kasan cewar shima anbarmasa kyautan ragowan canjin su.
Mamakine ya lulluΙe su Zahrah domin su a iyaka sanin su basu da wani wanda zai biya musu kuΙin siyayyan da sukayi, domin kuwa basu zo da kowa ba banda driver, inakuwa driver zaisamu maΖudan kuΙaΙe irin haka har ya biya musu kuΙin siyayya alhali shima yana fama da kansa.
“Kozaka iya faΙamana wanda ya biya mana kuΙin ?” Husnah ta tambaya.
“A gaskia bansan saba, sai dai da duk kan alamu irin larabawan nan ne da suke zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci” Cashier Ιin nan yafaΙa musu haka, domin shi a yanda yafahimta, da dukkan alamu wanda.yabiya musu kuΙin baiyi zubi da Ζ΄an nan gida Nigeria ba, duk da kuwa cewa muma muna da kyawawan maza amma kuma kyawun wani ya Ιare na wani.
Idanu Zahrah da Husnah suka zaro atare, sakamakon jin abun da Cashier yace.
“Balarabe fa kace?” Husnah ta sake tambaya cike da mamaki.
“Eh Balarabe, kece Zahrah ko?” Cashier’n nan ya tambaya yana mai nuna Zahrah da hanunsa.
“Ya’akayi kasan sunana ?” Zahrah ta tambayesa cike da mamaki.
Murmushi kawai yayi haΙe da miΖa mata wata farar takarda.
“Ungo yace inbaki”
Cikin tsoro Zahrah ta karΙi takardan da Cashier ke miΖo mata, haΙe da buΙewa.
_”KiΙauki duk wani abun da kikeso MY ZAHRAH! ban damuba koda duka Shoprite Ιin zaki ce kinaso, zan iya mallaka miki kome kikeso a duniyar nan, ko da kuwa dukiyata zata Ζare”_ abun da aka rubuta a jikin takardan kenan.
Wani irin bugawa Zahrah taji Ζirjinta yayi, “To waye?” tatambayi kanta a fili.
“Yadai me aka rubuta acikin takarda’n?” Husnah ta tambayi Zahrah cike da zaΖuwa.
Bata takarda’n Zahrah tayi domin batasan me zatace da’ita ba.
Husnah tana gama karanta takarda’n tasaki murmushi haΙe da kallon Cashier’n nan daya zura musu idanu… “Mungode sosai, idan ka haΙu da wanda yabiyamana kuΙin, ka isar mana da saΖon godiya” daga haka ta kama hanun Zahrah suka fice daga cikin Shoprite Ιin, bayan sun Ιau ledodin siyayyarsu.
“Saida sukazo bakin mota kafun Husnah ta saki hanun Zahrah, still fuskarta Ιauke da murmushi tace “Mekika fahimta game da wannan takardan, da kuma biya mana kuΙin sayayya da akayi?”
Cikin Ιaurewar kai Zahrah tace “Ni ban fahimci komai ba, sai ma tsananin mamaki da nake, taya haka zata kasance, anya kuwa ba wata maΖarΖashiyan ake shirin Ζulla mana ba Husnah?”
Dariya sosai Husnah ta kwashe dashi, domin kuwa maganar Zahrah takai a dara.
“MaΖarΖashiyan soyayya ba, babu wani aljanu, kawai dai inaga wani ne yaganki kuma ya yaba, shine kawai” Husnah tafaΙa tana mai danne dariyanta.
“Bangane ba me kike nufi?” Zahrah ta tambaya cike da ruΙu, domin ita kwata kwata ma bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba.
“Kada ki damu zaki gane mushiga mota”
Jiki a sanyaye Zahrah tabuΙe murfin motar tashiga, a gidan baya sukai mawa kansu masauΖi ita da Husnah..
Suna shiga driver yayi mawa motar key suka Ιauki hanyar Suleja unguwar su Zahrah.
(yauwa kuyi haΖuri jiya nayi mistake sunan unguwar su Zahrah ba Maraba bane, sunan unguwarsu Zahrah Suleja ne, kainane ya Ιau charge shiyasa)
Yanaganin tafiyarsu yasaki Ζawataccen murmushinsa, “Haryanzu tananan da halinta na tsoro, yayi imani Zahrah bazata taΙa sanjawa ba”
” komai naki yana burgeni Zahrah, inason komai naki!” Zaid dake cikin motarsa yafaΙi haka cike da shauΖi.
STORY CONTINUES BELOW
“Nifa gaba Ιaya kaina ya kulle, kimin bayani mana Husnah, me takardan nan take nufi ne?” Zahrah tafaΙi haka cikin zaΖuwa.
“Ki kwantar da hankalinki Ζawata, kawai dai bazai wuce irin mutanen nan masu alkhairi bane suka aikata hakan, wayasani ma ko Dr Sadeeq ne” Husnah tafaΙi hakan tana mai kallon Zahrah.
“Mene? kinanufin wai Doctor ne zaiyi haka? gaskiya banjin cewa shi ne, domin idan da shi ne, dole zai bayyana kansa na gansa, kodai ke akeso amawa wannan hidiman akayi mistake aka ambaceni” Zahrah tafaΙi haka cikin kokonto.
Dariya Husnah takuma sawa, haΙe da dafa kafaΙan Zahrah..
“Wai lafiyanki kuwa Zahrah? kinga yanda kika firgice lokaci Ιaya sai kace wacce ta aikata aikin rashin gaskiya, to ni miye ma abun damuwa ne don wani yabiyamana kuΙin sayayya? kinga bafa mu muka sa sa ba, ko ma waye shi yasanya kansa, kishare kawai Ζawata” Husnah taΖare maganar ta ta bayan ta Ιare sweet ta jefa acikin bakinta.
“Hmmm” kawai Zahrah ta’iya cewa, haΙe da mai da kanta jikin kujera, itakam gaba Ιaya kanta ya kulle, taya za’ace bakasan mutum ba, amma kuma ya biyamaka kuΙin siyayyan da kayi, irin haka ne mutum sai yaje ya jefa kansa a matsala.
Tafiya suke amma Zahrah ta kasa cewa komai, sai ma Husnah ce keta ΖoΖarin janta da hira, amma jefi jefi take amsa mata, domin kuwa wannan faΙuwar gaban da takeji har yanzu baidaina ba.
A haka har suka iso Ζofar gidan su Zahrah’n… Har cikin gida Husnah tayimawa Zahrah rakiya, kana ta fito tashiga mota suka tafi.
Zama tayi akan katifarta haΙe da zubawa kayan siyayya da sukayi ido, sam zuciyarta bata kwanta da wanda yabiya musu kuΙin kayan ba, zuwa yanzu ya kamata ace tayi hankali, domin sarai yanzu tasan salon yaudaran maza baida Ζarshe, suna iya yimaka komai don su samu biyan buΖatarsu, wannan yana Ιaya daga cikin babban dalilin da yasanya ta amince da auren Dr Sadeeq, ko ba komai idan ya aureta ta tsallake wani babban siraΙi na daga yaudaran da Maza sukeyi mawa Ζ΄an mata a wannan zamanin.
Ζaran wayartane yakatseta daga tunanin da takeyi, cikin sanyin jiki ta Ιaga Ζiran nasa, haΙe da kara wayar akan kunnen ta.
“Barkanki da hutawa My Princess!”
Dr Sadeeq yafaΙa cike da tsantsar kulawa.
Ζan guntun murmushi tayi haΙe da cewa “Kaima barkanka dai ya aiki?”
Ζata fuska yayi tamkar dai tana ganinsa haΙe da cewa “Aiki ba daΙi kokaΙan, ya kundawo a super market Ιin kenan?”
“Eh” tabashi amsa a taΖaice. Domin tsabar gajiyan da ta kwaso har wani bacci bacci takeji.
“Naga kamar kingaji da yawa, ki samu ki Ιan huta, zuwa anjima zanzo gida, inaso na samu Baffa, idan yabani dama zanturo magabata na ayi maganar auren mu, domin banso akai nanda wata Ιaya ban mallakeki ba!” yaΖare maganar cikin yanayin shauΖi.
Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, sakamakon jin abun da Dr Sadeeq yace. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki, wanda baza’a Ζirasa da farinciki ba, ba kuma za’a Ζirasa da yanayin baΖin ciki ba.
“Zahrah na!” yaΖira sunanta jin cewa tayi shiru batace dashi komai ba.
“Umm” ta’amsa masa a kasalance.
“Naji kinyi shiru, ko dai bakiyi farinciki da hakan bane?”
Yajefo mata tambayar da batayi zaton zai mata shi a yanzu ba..
“A’a nayi farinciki mana, kawai dai kainane ke Ιan min ciwo” tafaΙi haka don ta kare kanta, gudun kada yafuskanci wani abu.
“Ayya kiyi haΖuri, anjima idan zanzo zan tahomiki da magani ko, yanzu ki kwanta ki huta, nasan ma stress ne, insha Allah zuwa anjima zaki ji ki normal” yafaΙi hakan cike da kulawa.
STORY CONTINUES BELOW
“To” kawai ta’iya cewa dashi, haΙi da zare wayar akan kunnen ta.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauΖe, haΙe da share ruwan hawayen da suka fito daga cikin idanunta. “Yazama dole nakoyi soyayyarka Dr Sadeeq, domin bayan kai babu wani wanda zai bani kulawa kamar haka, ya Allah kamin maganin matsalolina!” tafaΙi hakan a bayyane, bayan ta Ιaga idanunta zuwa sama.
Da ΖΖ΄ar ma ta’iya cusa abincin da Inna ta bata, domin kuwa hakanan taji zuciyarta ta cunkushe.
Kwanciya tayi akan katifarta tana Ζ΄an tunani, take bacci Ιarawo ya siΙaΙo ya Ιauketa, batare da tashiryawa hakan ba….
Zaune yake akan wata haΙaΙΙiyar kujera, wanda take ita kaΙaice kuma na mussaman acikin bedroom Ιinsa, dake cikin guest hause nashi. Ιan Ζaramin table ne aje a gabansa, wanda samansa ke Ιauke da zungureriyar kwalbar wine da kuma glass cup.
Wayar sace riΖe a hanunsa, gaba Ιaya hankalinsa akan wayartasa yake, murmushine Ιauke akan fuskarsa, yayinda yake playback Ιin vedi’on daya mata Ιazu fitowarta daga cikin shoprite, batare da ta sani ba.
Harzuwa yanzu bai tantance mai yakeji a jiki da zuciyarsa ba a game da Zahrah, abu Ιaya yasani shine, yasan cewa “yana matuΖar buΖatarta a kusa dashi, fiye da tunanin mai tunani, yakuma Ιauki haka, amatsayin fitinanniyar sha’awarta da yake” sake playback Ιin vedion yayi bayan yakai Ζarshe akaro na barkatai domin kuwa yayi playback Ιin vedi’on yafi sau goma daga zamansa a wajen zuwa yanzu.
Wani irin sanyi haΙe da kewarta ne suke ratsa zuciyarsa alokaci guda.
“A hankali zankuma cimma burina akanki Zahrah, akaro na biyu ma ina da tabbacin cewa zanyi nasara akan ki, domin niban kasance Loser ba, bakuma zantaΙa kasancewa Loser ba, har abada !” yafaΙi haka cike da son Ζarfafamawa kansa guiwa.. A taΖaice dai haka Zaid yayita playback na vedio Ιin da yayi mawa Zahrah yana kallo, zuciyarsa cike da nishaΙi, abu Ιayane zai hanasa zuwa gareta a yanzu, shine plan Ιin daya shirya mata, bakuma zai je gareta ba, harsai ya tabbatar da cewa ta gama rufzawa cikin tarkonsa, da ya Ιana mata a karo na biyu….
(?)
Doctor Sadeeq ne tsugune a gaban Baffa Amadu, wato Ζanin mahaifinsa. Bayan ya gama kora masa bayanin duk abun dake faruwa, hatta fΖ΄aΙe’n da akayimawa Zahrah bai Ιoye masa ba, domin kuwa a yanzu Baffa Amadu shine Uba a garesu, kasancewarsa Ζanin mahaifi’nsu.
Ajiyar zuciya Baffa Amadu yasauΖe, haΙe dayin gyaran murya irin tasu ta manya…
“HaΖiΖa kazo da babbar magana Sadeeq, amma kuma duk na fahimceka, bakuma zanyi Ζasa a guiwa ba wajen ganar da mahaifiyarka dakuma Ζ΄ar uwarka, amma kuma kasan dole sai an haΙa da haΖuri, kasan su mata koda yaushe tunaninsu baya zurfafa, bakuma ko da yaushe suke gane abun da ake so su fahimta ba, amma tunda kakawo matsalan nan wajena, ka kwantar da hankalinka, ni nan zanje har gida na samu mahaifiyartaka, zamu tattauna akan matsalan!”
Wani irin sanyin daΙi ne yashiga huda zuciyar Dr Sadeeq, sai yanzu yakejin nutsuwa na sauΖar masa, yanzu fatan sa Ιaya, shine Allah yasa mahaifiyarsa ta amince, amma tabbas Zahrah itace burin ran sa…
Daga haka sukayi sallama da Baffa Amadu, bayan ya tabbatar masa cewa lallai zaice yasamu mahaifiyartasa da batun…
Cike da farinciki Dr Sadeeq yabaro gidan Baffan nasa, kai tsaye gidansu ya nufa….
Zama yayi dirshan akan kujeran dake falonsa, haΙe da soma cire safar Ζafansa, fuskarsa cike take da annuri dagani kai kasan yanacikin farinciki…
Turo Ζofar falon nasa akayi da Ζarfin gaske, wanda hakan yatilasta masa Ιago kansa da sauri, don ganin ko waye.
Dammm haka yaji Ζirjinsa yabuga, sakamakon ganin fuskar Hajiyarsa da yayi babu ko Ιigon annuri akanta, saima wani irin mugun kallo da take jifansa dashi.
STORY CONTINUES BELOW
Cike da girmamawa yace “Hajiya Barkanki da…..”
Saurin Ιaga masa hanu tayi, alaman batason jin komai daga garesa..
Cikin Ιacin rai da tuΖuΖin zuciya Hajiya tasoma cewa….
“Lallai ka haifu Sadeeq, tunda har zaka iya kai Ζarana wajen Ζanin mahaifinka, yanzu akan wata watsatstsiyar yarinya, ka ke neman ka bijirewa auren Ζ΄ar uwa kuma aminiyata da aka baka? Ashe dama wacce kake ikirarin kana so Ιin, ba cikakkiyar mace bace, sauran layine? kaban mamaki Ζwarai Sadeeq, amma bakomai ni na sakema har haka ta faru, kuma tabbas zanΙauki ΖwaΖΖwaran mataki akan ka, daga kai har sakaryar yarinyar da ka bawa soyayyarta amanna, bansan cewa rashin hankalin naka har yakai haka ba, ashe har zuwa kamun Ζafa wajen mutane kakeyi, akan cewa azo a bani baki, nabarka ka auri wacce tagama raba budurcinta ga mazan layi, hmmm wallahi kasaurari hukuncin da zan yanke, kuma tun wuri ka gaggauta cire tunanin auren wannan yarinyar aranka, domin kuwa bamai yi wuwa bane!” fuuu haka Hajiya ta juya ta fice daga falon nasa ranta amatuΖar Ιace…
Kalmar “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!”
Shine abun da yafito daga bakin Dr Sadeeq, wanda yasanya hannayensa gaba Ιaya ya dafe kansa… “Me yasa Aunty Raliya? meyasa zakimin haka?” yatambayi kansa cikin takaici dakuma Ιacin rai. Tabbas yasan Aunty Raliya ce ta sanar da Hajiyansa komai, domin kuwa lokacin da yake gaban Baffa Amadu ta Ζirasa, bai Ιoyemata ba kuma yashaida mata cewa yana gidan Baffa Amadu’n, ashe ita harta gane mai yakawosa, shine kuma tasanar da Hajiyarsu komai… Take idanunsa suka kaΙa sukai ja,, ba abun da yake masa ciwo kamar aibata Zahrah da akeyi, kowa idan yatashi sai yajefeta da sunan wacce ta watsar da mutumcinta a waje, alhalin kuma itama ba laifinta bane, Ζaddarace dakuma tsautsayi, domin kuwa shi kansa sheda ne akan abun da yafaru da’ita, tunda har kusan haukacewa tayi. Rasama me yake masa daΙi yayi, da wanne zaiji ne? da soyayyar Zahrah, ko kuma da fushin da Hajiyarsa keyi dashi. Gaba Ιaya ma ji yayi zazzaΙi nason kamasa don haka kawai sai ya koma Ιakinsa ya kwanta, ba abunda yake ambata sai sunan Allah, domin kuwa shi kaΙai ne zai iya kawo masa Ιoki,, dama kuma mu dashi muka dogara shine mai kowa kuma mai komai, sarkin da babu kamarsa, Allah kenan buwayi gagara misali, maiyin duk yanda yaso mai kuma Ζwacewa da kuma bayarwa alokacin da yaso, ga kuma duk wanda yaso…..
Zahrah kuwa tunda ta faΙa duniyar bacci ba’ita tafarka ba, sai gaf da’ana Ζiraye Ζirayen sallan magriba.. Kaitsaye banΙaki ta wuce taje tayi wanka haΙe da Ιauro alwala tazo ta kabbara sallan magriba.
Kayanta marar nauyi tasanya haΙe da ΙauΖan wayarta dakuma ledan da kayan siyayyanta ke ciki, tafito farfajiyar gidan nasu, zaune ta iske Inna tana faman ΖoΖarin kunna redio’nta, wanda koda yaushe take tare dashi kamar jaraba.
“Barka da dare Inna” Zahrah tafaΙa lokacin da tayi mawa kanta mazauni a kusa da Inna’n.
Inna bata amsata ba, saima kafe ledar dake hanun Zahrah’n da tayi da ido, Allah Allah take taga mene acikin ledar, domin dama bakinta ya bushe neman abun lasawa takeyi, kasancewar tuwo ta tuΖa abincin dare, bakuma tajin cinsa, tafison tasamu Ζwalam taΙan lasa, like o’o da o’o lol.
Tun Zahrah batakai ga buΙe ledar ba inna tayi gajen haΖuri haΙe da fusge ledar daga hanun Zahrah tashiga dubawa.
Ganin cewa tarkacen su Chocolate’s da kuma su biscuit’s ne acikin ledar yasanya Inna jan uban tsuka haΙe da bankamawa Zahrah harara.
“Aikin kenan gayyar tsiya, mutum yasan bakacin abu, amma saboda tsinannen baΖinciki dakuma mugunta, ko da yaushe shiyake saya bini bini, bazai sayo abun da duka gida za’a amfana ba mcheeww!” cikin Ζufula Inna taΖare maganar, domin kuwa ita duk wannan shirmen banzan basonsu take ba, tafiso taga daΖwalen kaza, kokuma gasheshshen nama mai zafi, yauwa tanan tafi kauri, amma kwata kwata kayan kantin nan ita ba zaΙinta bane.
Da Ζyar Zahrah ta iya danne dariyan Inna dake cikinta aciki.
BuΙe ledan tayi gaba Ιaya haΙe sa sanya hanunta taciro wani Ιan madaidaicin cake wanda daganinsa kasan yasha madara.
“Ungo wannan Inna shikan nasan zaki iyaci, saboda kema nasayoshi” Zahrah tafaΙi haka tana mai miΖamawa Inna cake Ιin.
“Yauwa kokefa, amma da kya bani wasu tarkacen banza”
Take Inna ta Ιare cake Ιin, tahau ci har lumshe idanu take, domin dai sosai cake Ιin yamata daΙi.
Murmushi kawai Zahrah tayi haΙe da gyara zamanta, tasoma latsa wayarta….
Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa Ιauke da sallama, atare Inna da Zahrah suka amsa masa.
“Wai ana Ζiran Zahrah a waje” inji cewar yaron..
Wani irin faΙuwa Zahrah taji gabanta yayi harsaida tasanya hanu ta dafe Ζirjinta……Wani irin faΙuwa Zahrah taji gabanta yayi har saida ta sa hanu ta dafe kirjinta daya fara dukan uku uku…..+
“Jekace tana zuwa” Inna tace da yaron,, bamusu yaron yajuya yafice daga cikin gidan…
“Yadai lafiyanki kuwa naga kinwani dafe Ζirji?” Inna tatambayi Zahrah, wacce lokaci Ιaya yanayinta ya sauya.
“Bakomai” Zahrah tafaΙa a taΖaice domin kuwa ko tayi ΖoΖarin ganar da Inna halin da take ciki tofa bazata gane ba…
“Tashi maza kije, ba kyau yin watsi da baΖo, wata Ζilama da alkhairi yazo miki, domin na lura keΙin baki da Ζashin tsiya” Inna tafaΙi hakan lokacin da ta miΖe daga zaunen da take.
Cikin sanyin jiki Zahrah takoma Ιaki ta Ιauko Ζaton hijab Ιinta ta sanya.
Tun kafun ta Ζarasa fita daga zauren gidannasu zuciyarta tasoma bugawa, wanda batasan dalilin hakan ba.
Wata mota ce tagani fake a Ζofar gidan nasu, kasancewar akwai hasken wuta, yasanya har kalan motar tana’iya hangowa.
Tsayawa tayi cak daga inda take, domin bazata sake tabka babban kuskuren da ta tabka a baya ba, batasan waye ba don haka bazata Ζarasa ba, idan wanda ke cikin motar yagaji ya fito, ya isketa daga inda take tsaye…
Cikin hanzari wani wanda baza’a Ζirasa da suna matashi ba, bakuma za’a Ζirasa da suna tsoho ba, yafito daga cikin motar hanunsa Ιauke da wani kwali, yayinda aka Ιaura wani kyakkyawan flower a saman kwalin… Ganin yanufota kaitsaye yasanya ta Ιan sake ja da baya..
“Sannu da fitowa ranki shi daΙe” mutumin nan yafaΙa..
“yauwa sannu” Zahrah ta bashi amsa a taΖaice…
” dama saΖone aka bani nakawomiki” wannan mutumin ya kuma faΙa cikin rusunawa haΙi da girmamawa, duk da kuwa cewa shiΙin ba yaro bane, domin yakusan haifar Zahrah’n ma, domin itama bawani yawan shekaru ne da’ita ba…
Cike da tsananin mamaki Zahrah, ta saki baki da hanci tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, yana miΖomata saΖon dake hanunsa…
“Wayekai?” shine kawai abun da ya iya fitowa daga bakinta, saboda gaba Ιaya kanta ya kulle…
Murmushi mutumin yayi haΙe da cewa “Ba’a bani daman sanar dake koni waye ba, kawai dai an umarceni dana kawomiki wannan saΖon, sannan dan Allah kada kice bazaki ansaba, saΖone mai mahimmanci, yanada kyau ki karΙa, sannan daganinki ke mai ilimi ce, kinsan bakyau maida hanun kyauta baya!” mutumin yafaΙi haka still yana mai sake miΖo mata kwali da flowern dake riΖe a hanunsa…
Kai Zahrah tashiga gyaΙawa, cike da tsarguwa tace ” Kana da girma da kuma mutumcin da bazanyimaka gardama ba, amma kuma saidai kayi haΖuri, bazan karΙi abu daga wanda bansani ba, bankuma san menene nufinku a kai na ba” tafaΙi hakan da iyaka gaskiyarta….
STORY CONTINUES BELOW
“Hakane, amma ki ceci aikina, domin wanda ya ban saΖonnan nakawo zuwa gareki ya tabbatarmin da cewa, idan har baki karΙi saΖon ba, to abakin aikina, kitaimaka, ina da iyalai, kuma da aikina na dogara” mutumin yafaΙi haka cikin rauni.
Zaro idanu Zahrah tayi haΙe da jinjina maganar mutumin aranta, lallai kuwa kowaye ya aikosa yacika Ιan jin kai, ita kuma irin mutanen da tafi tsana kenan a rayuwarta wato mutum mai jin kansa….
Cike da kokonto haΙi da zullumi tasanya hanu ta karΙi abun da mutumin ke miΖomata.
“ZankarΙane kawai saboda kai, domin na fuskanci rashin karΙana zai iya sanyaka acikin matsala, amma koma waye ya turoka kace masa injini ya sanja hali, domin wannan ba hali mai kyau bane” daga haka tasakai tayi komawarta cikin gida..
Cike da murna’n cewa ta karΙi saΖon wannan mutumin yakoma mota haΙe da yi mata key yabar area’n unguwar tasu….
Zahrah tana shiga gida kaitsaye Ιakinta ta wuce, yayinda Inna ta rakata da idanu…
Zama tayi akan katifa, haΙe da tsurawa kyakykyawan kwalin nan idanu, ba iya shi kaΙai bane, abun Ιaukar hankali, hadda wannan haΙaΙΙen flower’n dake samansa ma abun burgewane, alal haΖiΖa ma ita flower’n ne yafi Ιaukar hankalinta….
Cikin sanyin jiki tasa hanu ta Ιauki flower’n haΙe da matso dashi kusa da fuskarta….lokaci Ιaya ta zabura haΙe da wurgi da flower’n gefe, take idanunta suka kaΙa sukai jajur dasu, jitayi kanta yafara juyawa, tabbas bazata taΙa mantawa da wannan Ζamshinba har abada kuwa, ajikin mutum Ιaya tasan wannan Ζamshi, bayan shi kuma batasakejin Ζamshin a jikin kowa ba,, hannayenta ta sanya duka biyu haΙe da dafe kanta dayake sara mata,, tabbas irin Ζamshinsa fulawar nan keyi, take taji wani irin tsanar flower’n ya cika mata zuciya, san nan kuma tsanarsa tasake dawo mata sabuwa fil, cike da Ιacin rai ta Ιauki flowern haΙe da fita waje da’ita, ko son ganinta ma batason yi, kai tsaye wajen da suke aje shara ta nufa, cike da tsanar flower’n ta jefa ta cikin kwandon shara, haΙe da furzar da yawu akan flower’n duk wani abu da zai tuna mata da Zaid ta tsanesa…
Ranta a Ιace takoma Ιaki, ita dai Inna dake zaune a tsakar gidan haka ta saki baki galala tana ganin ikon Allah..
“Wallahi na tsaneka, tsana mafi muni, bantaΙajin tsanar wani a raina sama da wanda nakeyi maka ba, ya Allah kada ka sake haΙa fuskata da tasa!” tafaΙi hakan a bayyane, kuma cikin tuΖewar murya…
Gaba Ιaya Ζamshin da taji flower’n nan nayi ya Ιaga mata hankali, sabuwar tsanar Zaid yasake Ιarsuwa acikin zuciyarta…
Lallai da zataga wanda yasanya akawo mata flower’n nan da ta gargaΙesa da kada ya sake kawo mata komai nasa, don bata so, domin kuwa duk wani abu da zai sanya tayi tunanin Zaid bata Ζaunarsa, koda sunansa nema batason ji”
Kwanciya tayi lamo akan gado, tana mai da numfashi, ji takeyi gaba Ιaya ta tsani Ιakin nata, domin kuwa Ιakin gaba Ιaya ya Ιau Ζamshin turaren dake jikin flower’ Ιin nan….
Wayartace tasoma Ζara alamar shigowar Ζira, ganin Dr Sadeeq ne me Ζira yasanya ta Ιaga wayan, cikin son Ιoye damuwarta..
“InaΖofar gida” abun da Dr Sadeeq yafaΙa kenan, a cikin wayar, domin kuwa shima dai yauΙin yana cikin damuwa….
Babban tabarma ta shumfuΙa musu a tsakar gida, kafun tanufi Ζofar gida don yi masa iso..
Kusan tare suka shigo cikin gidan, tana gaba yana biye da’ita a baya.. Gaba Ιaya yagama karantar yanayinta, ya kuma gane cewa tana cikin damuwa.
Zama yayi akan tabarman da ta shumfuΙa musu, haΙe da tanΖwashe Ζafafunsa.. Gaba Ιaya nutsuwarsa ya miΖa zuwa gareta, ta hanyar zuba mata idanu….
Gyara zama Zahrah tayi haΙe da Ιaga idanunta ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauΖa akan na juna.. Cikin son basarwa tace ” Sannu da zuwa, ya hanya?”
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya ya sauΖe haΙe da lumshe idanu…”Hanya ba daΙi duk nagaji da tuΖin ma, i hope you will find a driver that will take me home” cikin zolaya yaΖare maganar..
Kallonsa tayi kawai, haΙe da yin Ιan murmushi, shiru tayi batare da tace dashi komai ba…
“Meke damunki naganki haka, ko dai ciwon kanne?” Yatambayeta cike da kulawa..
“No bashi bane, ka wai dai gajiya ne, baisakeni ba haryanzu” tafaΙi hakan a taΖaice…
“Kansa yajinjina, haΙe da sake lumshe idanunsa, shi Ιinma Ζarfin haline kawai yasa sa yazo, amma tabbas damuwar dake damunsa tana da yawa.
“Meke damunka, naga gaba Ιaya kamar baka cikin farinciki?” Zahrah ta tambaya cikin siga da yanayi na nuna damuwa..
Wani irin sanyin daΙi yaji a zuciyarsa, badon komai ba, saidon kulawa da yasamu daga gareta.
Gyara zamansa yayi haΙe da bata duka nutsuwarsa….”Bazan Ιoyemiki ba Zahrah, tabbas inacikin damuwa, kuma duk akan kine, Ina tsananin sonki Zahrah, ina da burin baki farinciki a cikin rayuwarki, amma sai dai na haΙu dake a Ζurarren lokaci, inafata zaki fahimci abun da zance dake?”
Cike da Ιaurewar kai Zahrah take kallon Dr Sadeeq, domin kuwa sam ita bata fahimci inda kalamansa suka dosa ba.
“Mahaifiyata ta zaΙamin matar da zan aura, yanzu haka maganar da nakeyi miki, har ansanya mana rana, saura sati uku”
dummm haka Zahrah taji Ζirjinta yabuga, duk da cewa bata wani jin son Dr Sadeeq a ranta, amma bazata taΙa so kyakkyawan namiji mai nagarta kamarsa ya kuΙuce mata ba, take idanunta suka ciko da Ζwalla wanda batasan na menene ba.
“Dan Allah kada kiyi kuka kinji Zahrah na, nafaΙamiki hakane don kisan halin da nake ciki, amma bawai hakan nanufin bazan aureki bane ba”
Cike da kulawa yakama duka hannayenta biyu, haΙe da kafeta da idanu. Gaba Ιaya abun da yake wakana ya kwashe ya faΙa mata, hatta maganarsa da Baffa Amadu, saida ya sanar da’ita, sai dai ya Ιoye mata Ζiyayya dakuma maganganun da yayarsa da kuma mahaifiyarsa suka faΙa akan ta na Ιatanci.
Cigaba yayi da cewa “Ki kwantar da hankalinki, na miki alΖawari nan bada jimawa ba, zaki zamo mallaki a gareni, insha Allah zanzamo mijinki Zahrah!”
Hawayene suka shiga zirya akan fuskan Zahrah, cikin murya mai rauni tace ” Dama nasan cewa nayi ganganci, domin kuwa kai ba sa’an aure na bane, nagode sosai da irin kulawa da kuma ΖoΖarin da kayi a kaina, bakuma zan taΙa mantawa da hakan ba, na yarda da Ζaddara mai kyau ko marar kyau, idan aurena dakai baiyi wu ba, na yarda haka Allah yatsara, tun da fari shiya gurΙatamin rayuwa, ya cutar dani, cuta mafi muni, ta yanda babu wani wanda zai lamuncewa haΙa zuri’a dani, tabbas daman nasan koda kai ka aminta da aurena, ba lallai iyayenka su aminta ba?….Kukane ya Ζwace mata sosai.
Sake damΖe hannayenta yayi acikin nasa, haΙe da kafeta da idanu, sosai tausayinta ya sake kamasa.
“Kinaso nasake shiga cikin damuwa ne Zahrah?” yayi maganar cikin tausasa murya.
Bata iya amasa masa ba, sai gyaΙa masa kai da tayi alamar “A’a”
“To idan har bakyaso nasake shiga damuwa, ki daina kuka kinji Zahrah na, insha Allah, zamu rayu tare dake, harma ki haifamin kyawawan babies, masu kyau kamarki, masu irin idanunki, da bakinki, harma da irin hancinki, da kuma…” sai yayi shiru, yana mai dariya Ζasa Ζasa.
Kunyane ya kama Zahrah haΙe da dariya, duk da kuwa cewa tana cikin halin damuwa, sai kawai ta kawar da kanta gefe, gaba Ιaya jinta take a tsarge sakamakon hanunta da ke saΖale acikin nasa…
“Zantafi saboda naga dare yasoma yi, amma saikinmin alΖawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma za kisa kanki a damuwa ba, idan kikayi haka zanji daΙi sosai”
STORY CONTINUES BELOW
Abune mai matuΖar wuya, a dake ka sannan a hanaka kuka, amma tabbas zata jarraba wajen daure zuciyarta.
“Bazanyi kuka ba” tafaΙa cikin muryar da bata fita sosai, da badon yana kusa da’ita sosai bana ma to tabbas da bazaiji maitace ba..
“Kinyi alΖawari?” yatambayeta
“Eh” tafaΙi haka bayan taΙanyi jim…..
“Yauwa Zahrah na, nasan ai kina da cika alΖawari, taso muje mota na baki magungunanki” babu musu ta miΖe daga zaunen da take, haΙe da rufa masa baya.
Murfin motar ya buΙe haΙe da fiddo wata Ζatuwar leda.
“Ungo magungunan suna ciki, akwai bayanin yanda zakisha a jiki, please ki kulamin da kanki kinji” yafaΙi haka cikin lallashi, haΙe da miΖa mata ledan dake hanunsa.
Kasa amsan ledar tayi, saima kawar da kanta gefe da tayi.
Murmushi Dr Sadeeq yayi, domin kuwa sarai ya fuskanci hakan da tayi metake nufi.
“Kiyi haΖuri ki karΙa kinji Zahrah na” yakuma faΙan hakan cikin lallashi.
Baki Zahrah taturo gaba haΙe da cewa …
“Kasan tun ba yauba nafaΙama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!” ta tambayesa cike da sakalci..
“Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka, amma yanzu dai banso kice a’a ki karΙa kinji” still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karΙi ledan.
“Saida safe” tace dashi cikin sanyin murya haΙe da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.
“Kada kimanta kin Ιauki alΖawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alΖawari kinji mai kyau na!”
Murmushi kawai tayi masa haΙe da Ιaga masa kai alamar taji.
Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haΙe da bata wuta yabar unguwar tasu..
Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haΙe da fusge ledar dake hanunta, babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaΙan zuciyarta zata fashe, saboda wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen Ζwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin Ιakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.
Ζaukan kwalin nan da aka kawo mata tayi, haΙe da soma kiciniyar buΙewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..
Tana buΙe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haΙe da zobe masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaΙai ya’isa ya bayyana haka, ΖaΖΖarfan ajiyar zuciya ta sauΖe haΙe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar yanda ta samu, Ιaukan kwalin tayi dukansa, haΙe da Ιoyesa a cikin kayanta, dawowa tayi kan katifarta ta kwanta zuciyarta cike tab da tunanin son gano wanda ya soma
bibiyar rayuwarta…
Hajiya Habiba (mahaifiyar Dr Sadeeq) ne zaune akan kujera gaba Ιaya ta tattara nutsuwarta ta miΖasa ga Baffa Amadu dake zaune akan Ιaya daga cikin kujerun falon…
Baffa Amadu ne yaci gaba da cewa ” Banzo nan don na yi miki dole ba, amma Hajiya Habiba yana da kyau wasu lokutan muna ΖoΖari wajen bawa Ζ΄aΖ΄anmu dama akan abun da suka nuna zuciyarsu naso, musamman ma aΙangaren abun da yashafi aure, haΖiΖa Sadeeq yasameni da wannan maganar yakuma min bayani tayanda zan fahimta, Alhmdlh nakuma fahimta, yanzu saura ke, kada kice wai don Ζaddara ya taΙa faΙa mata, Ιanki bazai aure ta ba, kada kiyi haka, domin ita Ζaddara tanakan kowa mai kyau da marar kyau, sannan abu nagaba danakeso kisani, ko da ace alal misali yarinyar ta kasance karuwa ce, addini bai hana masa auren taba, wala Allah saboda auren saiki ga ta shiryu, balle kuma ma bahakan take ba, amma bazan miki dole akan cewa saikin amince ba, Ιan kine kuma kina da iko akansa”…
STORY CONTINUES BELOW
Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauΖe, haΖiΖa Baffa Amadu yazo mata da magana mai girma.
Ιan nisawa tayi haΙe da cewa “Bawai naΖi aurensa da ita bane, saboda wani abu ba ne, kawai dai inajiye masa yanda tarbiyan yaransa zai kasance ne matuΖar takasance tana cikin gidansa, domin na tabbatar rashin wadataccen tarbiyan da aka bata a gidansu, shiya jawo faruwar haka a kanta, kaga itama bata samu tarbiya mai kyau ba, balle tayi ΖoΖarin bawa nata yaran, haΖiΖa Sadeeq yarone mai biyayya agareni, kuma harcikin zuciyata na Ζudurta aniyar cewa bazai taΙa auren wannan yarinyar ba, amma tunda harka shigo cikin al’amarin shikenan na’amince, amma kuma fa sai dai idan su biyun duka zai haΙasu ya aura, kaga dai Salima Ζ΄ar wajen Ζ΄ar uwata ne, haka kuma mamarta aminiyata ce, bayanda za’ayi na watsa musu Ζasa a ido, tahanyar cewa Sadeeq bazai auri Salima ba, kuma kaga yanzu saura Ζ΄an satika ne suka rage, har anriga da anfara shirye shiryen biki”
“Ζwarai kina da gaskiya ta wani wajen, amma kuma bamu iya ja da haΙin Allah, yanzu zansanar da Sadeeq Ιin duk yanda mukayi dake, zan kuma faΙa masa amincewarki, nasan shi Ιinma zai amince da umarninki, amma inaga zaifi kyau ayi bikin nasu a rana Ιaya, domin babu amfanin jan lokaci”
“Eh duk yanda kukace shikenan” Hajiya tafaΙi haka badon ranta yaso ba.
“Shikenan to duk dai yanda ake ciki, zai zo yasanar dake” Baffa Amadu yafaΙi haka bayan yamiΖe tsaye ya gyara zaman garen dake jikinsa…
Cike da mutun ta juna sukayi sallama shida Hajiya…
Zama Hajiya tayi afalon haΙe da yin jigum, tabbas ba’ason ranta ta amince da wannan auren ba, saboda ita gani take tamkar yarinyar ba kimtsatstsiya bace, ta amince ne kawai saboda Baffa Amadu yashigo cikin maganar, kuma tana matuΖar darajasa haΙe da basa girma, domin tana masa kallo ne tamkar marigayi mijinta, amma da ba haka ba da bazata taΙa amincewa ba, yanzu dai kawai sai dai tayi addu’an Allah yabasu zaman lafiya, amma ta wani Ιangare na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari Ζ΄ar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi, bazata taΙa son hakan ba, domin saboda bala’inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa Ζara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa Ζ΄arta Ιaya tilo zata haΙa miji da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince… Haka dai Hajiya tadinga saΖawa da kuncewa daga Ζarshe ta tashi ta wuce Ιakinta….
Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haΙa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa.
“Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaΙin mahaifiyartaka bane?” Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa.
Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai..
Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq Ιin yake ciki. “Kada ka Ιaga hankalinka Sadeeq, atunanina ka kai namiji wanda zai iya riΖe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaΙin mahaifiyartaka, addu’anmu shine Allah yatayaka riΖo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?”
Gaba Ιaya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. “Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaΙamin ranan da zakuzo, saina faΙa maka” inji cewar Dr Sadeeq..
“To shikenan Allah yakaimu” daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani Ιangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daΙi. Zahrah tana buΖatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma “Miye mafita?” yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma Ζudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban….
AmatuΖar mamakance Alhaji Ma’aruf ke kallon Zaid wanda yafaΙi maganar daya matuΖar basa mamaki…. “Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?”
“Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad”
Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma’aruf yace “Alhmdlh! naji daΙi Ζwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, Ζ΄ar wayene kuma a ina take?”
“Ba Ζ΄ar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta” yafaΙi haka da iyaka gaskiyarsa..
Jinjina kai Alhaji Ma’aruf yayi haΙe da cewa “Zan sa rana sainaje naga mahaifinta”
“To” kawai Zaid yace haΙe da tashi yabar falon Dad Ιinnasa….
Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman zuwa Ιauko ta ba…
Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa Ιauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma Ζawatasa da flower mai walwali..
“Ranki ya daΙe barka da yammaci” saurayin yafaΙa.
“Yauwa barkan ka dai” itama ta mayarmasa amsa cikin Ιari Ιari dashi..
“SaΖo aka bani nakawomiki” yafaΙi maganar yana me miΖa mata kwalin dake hanunsa..
Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta..
Murmushi saurayin yayi mata haΙe da sake miΖo mata kyakkyawan gift Ιin dake hanunsa.
“Waye ya aikoka?” tayi masa tambayar cikin dakiya…
“amsar tambayarki duka suna cikin nan” yaΖare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa.
Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karΙi saΖon.. Hanu biyu tasa ta karΙa, batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya Ζaraso tashiga.
Tsurawa kyakkyawan kwalin idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haΙe da Ιaukar hankali, gaba Ιaya ta Ζosa, tabuΙe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saΖonni, batare da yabari tasan kowaye shiΙin ba.
Tana shiga gida direct ta wuce Ιakinta, ko mayafinta bata cire ba, ta zauna haΙe da soma yaye ledan da akayimawa kwalinnan ado dashi, tana buΙe kwalin tayi arba da wani Ζatuwar ta karda wanda aka naΙeta, cikin sauri ta Ιago takardan haΙe da soma warwareta, amatuΖar razane tayi wurgi da takardan sakamakon idanunta da sukayi mata tozali da zanen hoton dake jikin takardan.
(?Ga Zaid ga Sadeeq ko waye cikinsu zai mallaki Zahrah?♀
Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 7 BY FATYMA SARDAUNA"