MRS AMIDUD CHAPTER 4
MRS AMIDUD CHAPTER 4 Kafin yace wani abu, tuni ta rab’awa Jalal macijin nan a kafad’arshi, ta kuma ce mishi. “Kaii! Wayyo ga macijin a jikinka” A firgice ya juya kafad’arshi kawai yayi mugun gamo, aikuwa ya sake wayar shi me kirar LG, sai da ta ɓare gida biyu. Ya kuma buga ihu tare da watsar da key din motar. Ai kuwa ya fadi a sosai sai da yaji ciwo. Dariya tasaka sannan tace. “Kutt! Sai kace wanda aka sanya mihi maciji me rai duk ya tsorata”+ Duk da ran AMIDUD yan ɓaci amma bai hana shi dariya ba, musamman yadda Jalal ya birkicewa. Tana ganin AMIDUD ta falla a guje, tana kyakyatawa. “Sannu! Kaji wannan Yarinyar kai jama’a zan zaneta” “A’ah! Kyaleta, yarinta ke diban ta wata rana bazata yi ba.” Ya karkad’e jikin shi sannan yace. “Bro muje!” Duk yadda AMIDUD yaso yayi magana Jalal ya hana shi, sai ma shiru da yayi mishi. Tunda Mamie taga ta manno a guje ta fahimci ta lakato AMIDUD shine ta arto a guje. …