TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 5

TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 5

ÆŠago kai Saifullah yayi ya ga me Baban Sasa ya ke yi ya dai ji yana shafa masa kamar mai neman tubarrukin maraya. “Watau Baban Sasa in a ce kowa zai dace da fitowa daga tsatson mutum irin ka ai ba sauran tashin hankali” ya faÉ—i bayan sun haÉ—a idanu.6 Dariya Baban Sasa yayi yana mai jin wani sanyi na ratsa shi don ya kasa gaskata abin da kunnuwar sa su ka jiye masa. “Nagode da biyayyarku gareni Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya” Baban Sasa ya ce yana mai murmushin farin ciki, Aameen yayi nauyin fita daga bakin Saifullah, sai yaÆ™e yake yi don shi bai son a tsawaita addu’ar ma balle a dace da yinsa a bakin Æ´an Aameen.7 “Bari na shiga wajen amaryar in tabbatar da dagaske na kada kai” yace yana mai miÆ™ewa.3 “Ja’iri ai ni É—in nan nine masoyinta na asali kai sai manaji” baban Sasa yace shima cikin dariya. Ficewa Saifullah yayi don ya gaji da É“oye halin yake ciki, neman inda zai zuba su yake yi. Bai É“ata lokaci ba ya wuce É—akin mahaifiyar sa ba tare da ya ankara da mahaifinsa da ke zaune a Æ™arÆ™ashin bishiya ba tare yake da Baba Salihu suna tattauna abubuwa da su ka jiÉ“inci danginsu. Haka su ka É—aga kai su ka kalle shi, kallo É—aya za ka masa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Shiru Baba Salihu yayi yana mai addu’a a cikin ransa yayin da Baba Anas ya tashi kamar wanda aka tsikare shi ya bi bayan Saifullah. *** Zaune ya iske Hajiya tayi tagumi da hannunta duka biyu, tun bayan fitar mijinta ta rasa ina za ta sa ranta taji sanyi, shike nan mafarkin da tayi ba mai tsawo bane balle ta sa ran tabbatuwarsa. Ba za ta ce ga lokacin da Madina ta fita daga gidan ba. “Yanzu Fisabilillahi kin yi abin da duk wata uwa yaci tayi kenan? Kalli lokacin da Amatullah ta nuna ba ta so kina ganin in uwarta ba ta mara mata baya ba za ta iya furtawa ne? Ku kenan ÆŠanku banza ko? Ni wallahi sakin ta zanyi ku neme ni ku rasa” ya ce yana mai sakin kuka kamar wani Æ™aramin yaro.8 Har cikin ranta take jin kukansa tsanar Amatullah na Æ™ara mamaye zuciyarta. Ko Baba Anas da ke tsaye bakin Æ™ofa ya ji kukan Saifullah har cikin ransa har ya fara tunanin bai yi ma É—ansa adalci ba. Yana shirin shiga É—akin ya ji hajiya ta É—ora da faÉ—in “kul! Sakin Amatullah daidai yake da nawa sakin” tace cikin muryar lallashi da son tare kuka. “What!!! Hajiya me kike faÉ—i ne” Saifullah ya faÉ—i a firgice. “Eh haka mahaifinka ya ce, yanzu maganar da ake sai dai muyi mata gashin Æ™uma, kar ka kuskura ka nuna baka son auren, mu bi ta da kisar mummuke” tace kai tsaye, hakan ya sanya Baba Anas yaye labule.3 “Kin san Allah sadiya, daidai da kuka na tabbatar Amatullah ta yi a gidan aurenta sai kin yi mafiyinsa. Ba zan hana ku ba fa, duk abin da kuka shirya ku aiwatar ni kuma zan tabbatar da na aiwatar da mafiyinsa gareki” ya ce daga bakin Æ™ofa ya juya ya fice daga É—akin.2 Shiru duk su kayi babu abin da ake ji a falon se shesshekar kukan hajiya wanda maimakon ya sanyaya zuciyarta Æ™ara rura wutan Æ™iyayyar Amatullah da mahaifiyarta kawai yayi.. Sun zauna fiye da mintuna goma sha biyar kafin Saifullah ya samu Æ™arfin tashi ya bar É—akin sakamakon kiran Sallah da aka yi. Jiki a sanyaye ya bi jam’i ya koma É—akin sa, duk wani notin tunaninsa ya kwance akan mafita kafin can da kyar ya tuna da ai dama kiran gaggawa aka yo masa ya dawo, kuma kullum hanyar da aka hau ta nan ake sauka. Ji yayi kamar ya jawo lokaci zuwa tsakankanin magariba da isha’i da iyayensa kan zauna. STORY CONTINUES BELOW *** Tuki ya ke kamar wanda ya ke shirin rasa ransa da gangan, zagi kuwa ya sha ba adadi a haka har Allah ya isar da shi gidan da su ke zaune. Nan ma fitowa daga motar ne ya gagare shi, kansa ya kifa bisa sitiyari ya na mai zubda hawaye. Karar da wayar shi ta ke bai sa ya É—ago ba balle ya duba ya ga wanda ke kiransa har wayar ta katse, aka kara kira karo na biyu, ta sake katsewa. Sai a karo na uku ya dago a fusace da niyar kashe wayar gabada É—aya. Ko da ya ga number da ke kiran sa tuni ya daga ya na mai faÉ—in3 “Mummy…….” “David na shiga uku David, dama nima na mutu na huta, na Æ™ara rasa miji! Philemonis dead, my husband is dead!! life is never fair to me!!!!”3 Mummy ce ta katse shi cikin ihu da kururruwa wanda hakan ba karamin gigita shi ta yi, cikin tashin hankali ya furta “Mummy calm down and talk to me, mai ya samu Dady?” “He is dead, Philemon is dead!” “Jesussssss” Cewar Dee yayin da maganar Mummy ya daki kunnan shi a karo na biyu. Kuka da kururruwa jama’a da ya ke ji ya na tashi shi ya daÉ—a gasgata abin da zuciyar shi ke kokarin karyatawa. “But why? How? When?”2 Tambayar da ya jero mata kenan. kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa buÉ—e baki ta bashi amsa. Tausayin ta ya lullube shi, ya na kukan rashin Amatullah, ashe shi ba rashi yayi ba, Mahaifiyar shi ita ce ta yi rashi babba. “It’s ok Mummy, ki yi hakuri gani nan zuwa” Ya aje wayar cikin zafin nama ya shiga ciki. Cikin kankanin lokaci ya shirya tsaf, kamar goma daidai ya hau titin da zai sada shi da birnin tarayya. **** A daddafe Saifullahi ya iya hakurin jiran ayi sallan magariba. Bai ko tsaya azkar ba ya tashi ya je wajen zaman iyayensa ya zauna yana jiran su. ÆŠaya bayan É—aya su ke fitowa nan yake gaida su, amsawa su ke suna mai masa fatan alkhairi a aurensa. Bai ji dadin fitowar mahaifinsa ba amma sai ya ji sanyi ganin baban Sasa ya fito “Fitinannen tsoho dole ka yi Æ™arfin fitowa sallah tun da ka gama haÉ—a fitina” ya samu kansa da fadin haka a zuciyar sa duk da murmushi ke kwance a fuskar sa.3 “Baban Sasa gara da ka fito dama ina shirin shigowa in same ka ne, wannan makaranta tamu yan bakin ciki ne, sun min kiran gaggawa” yace yana yamutsa fuska kamar wanda aka shiga hakkinsa da gaske.2 “Subhanallah! Yaushe ake bukatar ganin ku” Baban Sasa ya faÉ—i ba tare da ya samu shakku a maganar saifu ba. “Wai nan da Laraba fa Baban Sasa, ka ga ba samun jirgi zan yi ba gara na kama hanya zuwa Lagos gobe na fara rage zango, domin fara Shirin tafiya, idan na ci sa’a nan da kwana biyu ma zan iya samin jirgi” ya fadi yana mai sinne kai. “Amma da matarka za ka wuce ko? Ko jiÆ™a jibge kake tunanin mu ka yi?” Baba Anas ya ce yana Æ™ara yamutsa fuska cikin takaicin hali irin na É—ansa.3 “Anas!!!” Baba Zubairu da Baban Sasa su ka faÉ—i a tare cikin sigar tsawatarwa. “Saifullahi zango nawa ya rage maka a Rasha” Baba Zubairu ya faÉ—i yana kallon Saif. “Zangon Ƙarshe nake zan haÉ—a masters É—ina, inshaAllah nan da wata uku na kammala da yardan Allah” yace cike da ladabi, kallon sa Baba Anas yake kamar ya kwaÉ—e shi. “Toh madalla, abu ya kawo gangara, tun da buri na ya cika ka je, in ka dawo nan da wata uku sai matarka ta tare inshaAllah” fadin Baban Sasa yana mai mikewa don shiga gida. “Amma Baba sai ku ta biye masa” Baba Anas ya ce don ba haka ya so ba. Ko ta kansa Baban Sasa bai yi ba illa ya wuce abin sa ya tafi don ya shiga cikin gida Saifullahi na bin bayan sa yana mai cika shi da daÉ—in baki. “Ni Anas na rasa irin ka, wai me Mairo ta baka ne? Kwatakwata in dai abin da ya shafe ta ne ko yaranta idonka rufewa yake yi. Ina laifi yaron nan bai nuna rashin so ba amma ita yar gwal din Æ™aton arne ta kawo don ta aura. Wallahi ka yi ma kanka faÉ—a” Baba Zubairu ya ce cikin fushi. Nan duk su ka shiga faÉ—in albarkacin bakin su akan bakin halin Amatullah da mahaifiyar ta duk da cewa su kansu ma su faÉ—in sun san Æ™arya su ke shirgawa. *** A bakin mahaifin ta Amatullah ta ji batun tafiyar Saifullahi wanda hakan ba karamin kwantar mata da hankali ya yi ba, domin kuwa idan akwai abin da ta ke fargaba ya bi bayan ranar tarewar ta gidan Saifullahi. Washagari da safe Saifullahi yayi harama duk da kuwa jirgin sa na zuwa Lagos na yamma ne, gani ya ke zaman jiran lokacin tafiya tsautsayi ne. Sanye ya ke cikin kananan kaya, shuÉ—in riga mara hannu da shudin wandon jeans yayi kyau kamar bakin bature. Bayan ya sallami Hajiya har zai fice daga gidan ya hangi É“angaran su Amatullah, Gwaggo ce ta ratsa zuciyar sa, ya tuna alkhairin ta gare shi kuma ya san tabbas idan ya je yiwa Baban Sasa sallama sai ya tambaye shi ko ya shiga wajan amaryar ta sa ta dole, dan haka ya yanke hukuncin shiga ba dan komai ba ko dan darajar Gwaggo. ‘Allah ka min katangar karfe da ganin bakar fuskar yarinyar nan!’2 Addua’ar da ya ke yi kenan yayin da ya nufi bangaran su Amatullah. Da sallaman shi da shigar shi falon lokaci daya ya yi su, tsayawa yayi baki bude tamkar wani soko sanadiyar abinda idanun sa yayi tozali da shi, Amatullah ce kwance a bisa kan doguwar kujera, irin wannan kwanciyar na rigingine. Bai san sanda ya bi ta da kallo tunda daga dogayen yatsun kafarta, har zuwa dogon wuyar ta, zuwa kanta da ke daure da kallabi ba, Yayinda bugun zuciyar sa ta karo cikin kaduwa da ganin baiwar ubangiji. Sanye ta ke cikin koran materials riga da siket, da ke Amatullah mashaAllah akwai diri, kayan ya zauna jikin ta ya yi mata cif cif. Littafin husnul muslim ne kife a kirjin ta, hawayen da ke gangarowa daga idanun ta da yake a lumshe ne ke nuna alamun ba bacci ta ke yi ba. A hankali ya furta14 “Hasbiyallahu wani’imal wakil” Hakan yayi daidai da fitowar Gwaggo daga dakin ta, ganin yanda Saifullahi ya shagala ya na kallon Amatullah wacce daga ganin alama ba ta san da shigowar shi ba, da niyyar Amatullah ta farga ta furta “Ah ah Saifullahi shirin tafiyar kenan!”2 Jin haka a zabure Amatullah ta bude Idanun ta su ka yi ido hudu da Saifullahi wanda yayi tsaye bakin kofa. A rikice ta tashi da sauri ta nufi dakin ta, Saifullahi kuwa ganin Gwggo bai sa ya fasa bin ta da idanu ba har ta shige daki.3 “Saifullahi ka na ji na kuwa?” Gwaggo ta sake magana a karo na biyu ta na mai duban Saifullahi wanda sai a sannan ya lura da fitowar Gwaggo, cike da jin kunya ya durkusa har kasa, yana mai sosa kyeya ya furta “Iyye? Na’am Gwaggo barka da asuba, ai ban ga fitowar ki ba ne”3 Gwaggo na murmushi ta ce “Eh gaskiya dai ba ka gani ba, cewa na yi shirin tafiyan kenan” “Eh Gwaggo, dama sallama na zo na mi ki, sai Allah ya dawo da ni” Ya bata amsa a takaice domin kuwa Allah Allah ya ke ya fita daga gidan tsabagen kunyar da ya rufe shi. Kamar wanda ya ke kan Æ™aya yayiwa Gwaggo sallama a gaggauce ya fito. Haka ma Baban Sasa, sallamar a tsatsaye aka yi ta domin kuwa sam ba ya cikin hankalin sa.8 Cikin ikon Allah ya samu motar da zata kai shi Kaduna tun kafin ya isa tasha saboda fitowar direbobi masu lodin Kaduna Abuja. Gidan baya ya shiga a cikin Sharon É—in da ya samu. Wayar sa Æ™irar Sony Ericson ya É—auko yana karanta abu a yana gizo duk don ya cire tunani a ransa amma ina, maimakon ya ga rubutu, surar Amatullah kawai ya ke gani a fuskar wayar sa. Yana jin ana faÉ—in mata masu mazauna da dukiyar fillo bai taÉ“a haÉ—uwa da wanda nata su ka zauna daidai da jikinta ba. Lumshe ido yayi maimakon ya bar gani sai hango ta yayi kamar ta nufi shi cikin murmushi. “Yaa Rabbi” ya samu kansa da neman agajin Ubangiji. Amatullah da tun bayan fitar Saifullah gaban ta ke faÉ—i, ta san tsayuwar da yayi kallon nan na kaskanci ya ke mata. Ta ji haushin ganin ta da yayi a haka. Kirjinta ne ya mata nauyi duk da ba ta son tuno halin da Dee zai kasance abin ya gagara.2 Saboda kwallafa rai har mafarki ta yi ya zama gawurtaccen pastor hakan ya sanya ta tashi da nannauyyar Æ™irji.2 Tun da ta yi sallah ta yi azkar É—inta na safe ta ke karanta addu’ar da ake lokacin Æ™unci da damuwa, can dai ta Hau kan kujera ta miÆ™e baya. Rashin jin dadin kwanciya da hijabi ya sa ta cire ashe za ta yi mummunar gamo ne. Sai da ta tabbatar da ya fice da daÉ—ewa ta sanyo hijabinta don zuwa gaida iyayenta a cikin gida. “kuma in kin shiga É—akin hajiya ka da kiyi gaggawan fitowa, yanzu banda Kasancewar ta matar babanki uwar mijinki ce, saura kije kina soliÉ“iyanci” ta tsinkayi mahaifiyarta na faÉ—i yayin da za ta bar É—akin. Haka kuwa aka yi, sai da ta gaida sauran ta shiga É—akin hajiya. Sai da ta zauna a Æ™asa sannan ta gaida ta cike da ladabi. Hango hawayen Saifullah da hajiya tayi ne ya sa ta kauda ido gefe ba tare da amsawa ba. Sai da ta yi zaman mintoci sannan ta Mike don gaida Baban Sasa.3 A nan ta iske wasu daga cikin Baffaninta ta gaida su kafin ta isa kusa da baban Sasa kamar za ta shige jikinsa. “Jiya ban ganki ba, nace har kin fara kewan na ainihin ne” yace cikin sigar tsokana. Sinne kai ta yi tana dariya sannan tace “Ai zan dinga ganin fuskarka kullum a tashi fuskar in maka addu’a da ka zaÉ“a min baÆ™in bature, nagartacce tsatson Muhammadu Jamoh” ta ce tana kwantar da kanta a jikinsa.3 “Ki yi hakuri kinji. Ke kin san shi ma, hajiya Sahura ba ta san ni ba sai bayan ta tare, hajiya Talatu na haka, kadarko ce kawai mu ka yi soyayya kan aure. Kinga a tsawon zaman mu da su ban taÉ“a ganin halittu mafi soyuwa a gare ni sama da su ba. Ki zama nagartacciyar mata soyayya zai zo daga baya. Ki yi hakuri ki yafe min… “3 ” shisssssssssssshhhhhh!!! ” tace tana rufe bakin sa. ” Babu abin da ka min sai gata da kauna. Ka tabbatar min da duk cikin zuri’a ni ce ta Æ™asan heart” ta ce tana dariya, shi É—in ma dariya yayi.5 *** Tun isar sa Abuja jiya da azahar ya ke rarrashin Mahaifiyar shi, mijin na ta ya mutu ne irin wannan mutuwar fuji’a, babu ciwo aka wayi gari babu shi Allah ya ma sa cikawa. Alhinin mutuwar da kuma shirye shiryen bikin birne mamacin bai bashi daman zama yayi tunanin Amatullah ba, duk da kuwa zafin rashin na ta ya zame masa tamkar gyambo cikin zuciyar sa.4 A safiyar aka shirya mamacin tsaf cikin riga da wando suits, kwance cikin akwati da ya sha ado da furanni iri iri. Akalla motoci uku ne su ka jeru wajan rakiyar mamacin, in da Dee ke tuka motar da ke dauke da Mamacin, hanyar Yola su ka dauka in da za a yi bikin birne mamacin. **** Igiyar auren Saifullahi bai hana Amatullah tunanin Dee ba, wanda hakan ba Æ™aramin tayar mata da hankali ya ke ba, ta na matar aure ta na tunanin wani namiji daban, har ta na duba wayar ta ko za ta ga sako ko kira daga gare shi ya shigo. Ganin hankalin ta na shirin gushewa ya sanya ta É—auro al’wala, sanye da hijabi ta kalli gabas, da kyar ta iya idar da raka’a biyu. Tun tana addua a hankali har kuka ya ci Æ™arfin ta ta fara addua a bayyane, tana cewa5 “Ya Allah ka rufa min asiri, ya Allah kar ka kamani da laifin soyayyar da na ke yi wa wanin mijina, ya Allah ka yaye min wannan masifar da na ke ciki, Allah kar ka jarrabe ni da wannan masifar bayan ka sanya tazara mafi girma a tsakanina da wannan bawa na ka, ya Allah…..ya Allah…ya Allah….. ya Allah……”4 Kuka ne ya ci karfin ta, ta kasa magana sai shasshekar.2 **** Yanda Amatullah ke cikin halin ha’ulai, haka Saifullahi ke cikin halin damuwa, tun barowar shi Zaria babu abinda ya ke tunani face kyakkywar surar Amatullah, haka zalika ko ya rufe idanun sa da niyar runtsawa ita É—in dai ya ke gani. Abin takaicin shi shine wai kamar shi Saifullahi duk surar da ya sha gani birjik a titin Allah a kasar turai ya rasa wanda zai gigita shi wai sai na bagidajiya, yar kauye kamar Amatullah!!11 Zaune ya ke Airport ya na jiran isowar jirgin da zai tashi da su zuwa Lagos, dake an sami delay na wajan minti talatin kafin isowar jirgin. Idanun shi lumshe yayinda ya kifa fuskar sa cikin tafikan hannun sa, yayi kusan minti goma cikin wannan halin kafin daga bisani ya dago yana mai zaro wayar shi daga cikin aljihun wandan sa, kai tsaye wajan hotuna ya shiga in da ya lalubo hoton budurwarsa Aysha Ayuba Daneji, wacce aka fi sani da Ayush. Ayush ‘yar Kano ce, irin ‘yan matan nan ne marasa kamun kai, da tarbiya, Amma idan wajan wayewa, ado, matse jiki da fidda tsaraici idan aka same ta sai dai a shafa fatiha. Kasancewar ta É—iyar hamshakin mai kudi, primary school kaÉ—ai ta yi a Nigeria, hatta secondary turai ta yi, saboda haka za a iya Kiran ta rainon turawa. Tare su ke masters da Saifullahi, duk duniya ta ce babu wanda yayi mata sai Saifullahi, shi kuwa dama faÉ—uwa ce ta zo ma sa daidai da zama, domin kuwa burin shi ne auran wayayyiyar mace.3 A shekaru Ayush ta girmewa Amatullah, saÉ“anin Amatullah ita fara ce tas, duk da dai ta kan Æ™ara da na kanti. In aka dauke fari da wayewa babu abin da za ta nunawa Amatullah. Idanun sa kan hotan Ayush, wanda take sanye cikin kananan kaya riga da wando, kan nan ba dankwali an zubo da gashi har kyeya. Ajiyar zuciya ya saki, a zahiri ya furta “Me zan yi da wannan bagidajiyar when I’ve someone like you? Haba ga mace nan har mace zuciya ta za ta addabe ni da wata yar kauye mamalam!”2 Jin ana sanarwar jirgin su zai fara boarding ya sanya shi tashi da sauri ya na mai tura wayar cikin aljihu. Allah ya kai su Dee Yola lafiya, kasancewar da daddare su ka isa, Nan family house din mamacin aka sauka, in da su ka tarar da yan uwa da abokan arziki suna tsimayin isowar na su. Tun a daren ranar Dee da Æ´an uwan mamacin su ka fara shirye-shirye bikin birne gawar, wanda za a yi nan da kwana goma sha biyu zuwa sha uku. Kamar yanda kwanaki su ka yiwa Dee tsawo, haka su yi ma Amatullah, kwana bakwai da aka ba su hutun midsemester É—in ya zame mu su kamar shekara bakwai, a É“angaran Dee; rashin Amatullah da mijin Mahaifiyar ta shi ba karamin karamin girgiza shi ya yi ba, gashi shirye shiryen birne gawar kaÉ—ai ya isa ya gajiyar da É—an adam. A ce an rasa mutum amma sai an yi gagarumin biki ranar da za a rufe shi? Shi kam Dee wannan na É—aya daga cikin al’adar kiristanci da sam bai ma sa ba.2 Amatullah kuwa a nata É“angaran yanda matan gidan kan kira ta da Amarya duk da tana hango isgilanci a sautinsu yayin da su ke ambato mata wannan sunan ya hana ta sukuni, Ba wai isgilancin ke Æ™ona mata rai ba, jin da take hakan kamar danganta ta da saif ne ya fi komi É“ata mata rai. Angon na ta kuwa tun da ya sa kafa ya tafi babu wanda ya sake jin É—uriyar shi, hatta Baba Anas yayi kokarin samun shi a waya, amma abin ya gagara, shi kuma bai kira ya shaida mu su isar sa Russia ba.4 Ranar Laraba da safe ta tashi da matsanancin tsanar gidan, tunanin wajen zuwa ta ke yi don ta samu sauyin iska. “Zulaikha” Kawai taji É“arin zuciyarta ta ambato mata hakan ya sanya ta sakin murmushi. Kamar yadda ya ke al’ada garesu gaida iyayensu bayan sun idar da azkar hakan ta tashi ta yi, haka kuma kamar yadda mahaifiyarta ta umurce ta duk ta shiga É—akin Hajiya ta kan É—an É“ata lokaci, don ko jiya sai da ta kama mata ninkin kaya sannan ta fito. Cikin sa’a ta samu Baba Anas zaune yana sauraron sashin hausa na radiyon BBC, gaishe su tayi a ladabce sannan ta yi shiru tana Æ™ara sunkuyar da kai. “Ƴar Baba Anas da magana a bakin nan” Baba Anas ya ce cikin sakin murmushi. Ƙara sunkuyar da kai ta yi. Harara Hajiya ke watsa mata tana zagin ta a zuciya, ita da Amatullah za ta hakura da shigowa É—akin ta da ya fiye mata komai. “Ehmm! Amatullah Ina saurarenki” ya ce yana mai rage sautin radiyon sa don ya ji me take tafe da shi. “Baba don Allah izininka nake nema, ina son in duba Æ™awata Zulaikha” tace gaban ta na faÉ—uwa, tsoro bai sake cika ta ba sai da ta É—an É—aga kai ta kallo sashin Hajiya ta ga harar da ta watso mata, ta ke ta shiga da na sanin tambaya tun farko. Gani ta yi shine mahaifin mijinta a tunanin ta zai iya bata izini makwafin mijin nata. “Allah ya dawo da ke lafiya, kar dai ki kai almuru a waje” yace yana murmushi. “Na gode Allah ya kara girma da lafiya” ta ce cikin farin ciki. “Aameen Ƴar Baba” yace Shima cikin farin ciki. Da haka ta tafi É—akin mahaifiyarta cikin farin ciki, jinta take zaman ta a gidan Jamoh kamar wacce ke zaune a gidan maza. Da wannan farin cikin ta iske mahaifiyarta ta faÉ—i mata yanda su ka yi da Baba Anas, tana kallon yadda murmushin fuskar mahaifiyarta ya ke dusashewa a hankali. “Yanzu ke sai ki É—auki jiki ki fita tsigau tsigau se kace wacce ba ta da mafaÉ—a, ko da can kan ki yi aure haka kike fita kamar baÆ™ar Leda balle yanzu da aure ke kanki? Mijinki kawai zai baki izini in bari ki fita, sakarai mara kishin kai” Gwaggo ta faÉ—i tana tashi daga wajen.3 STORY CONTINUES BELOW ‘Oh ni mai na yi na laifi yanzu da Gwaggo ta ke kausasa halshe akai na. Allah na tuba ka yafe ni ba zan sake ba’ ta ce cikin ranta tana mai tausayin kanta. Wayarta ta É—auko ta kunna cike da addu’ar ganin saÆ™o daga Dee, maimakon nashi sai na mahaifinta ta gani wanda ya wuce Abuja a safiyar Litini, nasiha ce da addu’a haÉ—e da fatan alkhairi gareta. Tayi murna sosai, kaunar mahaifinta na Æ™ara cika ta, gani take wacce ta rasa uban da zai bata kariya da tallafi a duk halin da za ta shiga lallai ta yi rashin majingini babba.2 Ba ta fita daga akwatin tura saÆ™o ba ta lalubo lambar zulaikha ta aika mata da sako, daga nan É—auko littafin ‘the end of the world’ na Dr. Muhammad Abdulrahman Al-arifi ta fara dubawa cikin natsuwa, tsoron Allah na Æ™ara ratsa ta. Ba ita ta tashi ba sai wajen Æ™arfe goma sha É—aya na rana in da ta tashi ta je taya mahaifiyar ta É—aura sanwar abincin rana. *** Zulaikha ba ta ga saÆ™on ba sai kusan Æ™arfe goma sha biyu, “An É—aura aure na da yaya Saifullah ranar Asabar bayan sallar asuba” ta karanta ta Æ™ara karantawa tana mai Æ™aryatawa. Numbar Amatullah ta latsa kira ya ci ringing har ya tsinke ba tare da an É—aga ba. Haka ta dinga kira ganin ba a É—aga bane yasa ta kira maman Jaafar. “Zully ke ce yau da kira” tace tana É—agawa. Su kan yi ma zulaikha tsiyar ba ta kiran waya walau ta turo sms ko kuma ta ishe mutum da flashing. “Yoh maman Jaafar ai dole na kira yanzu, kinji an É—aura auren Amatullah wai” tace cikin mamaki da rashin yarda. “Aure kuma, sai kace Æ´ar takarda” maman jaafar tace cikin Æ™in yarda. “Yanzu na ga text É—inta, na kira kuma bata É—aga ba, amma Daman akwai alkawarin aurenta da Yaya Saifullah É—in” Zulaikha ta faÉ—i tana son ta haska ma maman Jaafar yiwuwan auren. “Allah sarki Dee Yusuf kuma kin san ranar Juma’a na kwatanta masa gidansu, yanzu shike nan ba rabon sa bane” maman jaafar tace cikin tausayawa don ba za ta mance tsantsan son Amatullah da ta hango a idanunsa ba ranar.. “Haba! Ai in har Dee ya isa gidan su Amatullah toh tsaf Baban Sasa zai sa a É—aura auren nan. Ai jin auren nan yake kamar in ba ayi ba ya rasa wani sashi na jin dadin duniyar sa ne” Nan zulaikha dai ta ba maman jaafar labarin da ta sani a takaice. Tayi mamaki kwarai musamman da ta ji Dee Yusuf ba musulmi bane. Da ga baya su ka yi sallama akan sai sun ji daga Amatullah.2 **** Ana sauran kwana biyu bikin birne mijin mahaifiyar Dee aka koma makaranta. Da sassafe Amatullah ta hada nata ya na ta cike da farin cikin za ta bar gidan ta huta da habaice habaice. Kafin ta ta tafi sai da Gwaggo ta zaunar da ita ta mata fada sosai, irin wannan fadan mai shiga jiki. Har sun yi sallama ta dau jakar ta Gwaggo ta dakatar da ita ta na mai fad’in “Amatullah?” “Na’am Gwaggo” Amatullah ta amsa jiki a sanyaye. “Na yarda da ke tun kafin nauyin aure ya hau kan ki, bare yanzu, dan Allah ki tsare mutuncin ki, dan Allah Amatullah, kin dai san ke matar aure ce, wannan yaran da na ji ana magana akan shi……” “Gwaggo…..” Amatullah ta katse ta yayinda idunun ta ke fidda kwalla. Kana ta kara fadin “Gwaggo kin ce kin yarda da ni…..” Tashi tsaye ta yi ta zo gaban Amatullah, ga mamakin Amatullah sai ga Gwaggo ta ruko hannayen ta biyu, cikin sassanyar murya ta furta ” Na yarda da ke É—iyata, Amma zuciya ba ta da kashi, ba na so in ji ance ko sannu ta haÉ—a ki da wannan yaron, dan Allah Amatullah ki rufa mana asiri, kar ki ga kamar ban damu da lamarin ki ba, kawai ina kawaici ne”2 Kai Amatullah sannan ta ce “Na mi ki alkawarin cigaba kare mutunci na da hakkin addinina kamar yanda na saba Gwaggo” Cikin jin dadi Gwaggo ta rakota har kofar falo, sannan ta umarce ta da ta je ta yiwa Hajiyar Saifullahi sallama. Ta ci sa’a ba ta sami Hajiya ba, Baba Anas ma gun Baban Sasa ta same shi tare da su Baba Zubairu. Nan duka su ka mata nasiha tare da sa albarka, Baba Anas ne ya bata kudi a cewar shi yanzu dole ya na wakiltar Saifullahi, gashi babu yawa. zuciyar ta cike da farin cikin addu’oi da ta sha daga gare su ta wuce makaranta. Tun da ta sa kafar ta cikin makarantar gaban ta ke faduwa ba dan komai ba dan Dee Yusuf da ta ke fargaban gani, da ta hangi namiji ya doso ta sai ta yi saurin kau da kai, kai har gani ta ke kamar ma gizo ya ke mata. Kirjin ta na dukan uku uku yayinda ta ke karanta ‘Lailaha illaanta subhanaka inni kuntu minil zalumin’. Ba ita samu kwanciyar hankali ba sai da ta ganta cikin hostel. Kaf É—akin ita ta riga kowa kowa dawowa. Mayafi da jaka ta aje ta shiga gyaran daki..