YAR MAKIYAYA CHAPTER 19

YAR MAKIYAYA CHAPTER 19
YAR MAKIYAYA CHAPTER 19 Rasheed abunda ka aikata bai yi daidai ba, this family is a very respected family, da baka yi gaggawar k’iran police ba, duk bamu san menene gaskiyar lamarin ba da ka bi abun a hankali…….” Abban Habeeb bai kammala maganar sa ba Rasheed ya katse shi ta hanyar d’aga masa hannu kafin yace+ “a bi abun a hankali? Me kake nufi da hakan?? Gosh! Brother na yi zaton kai ka fi ni hankali da tunani, but it seems ba haka bane. Yaya za’a yi ace an kama mutum dumu dumu da laifin kisa sannan kace kar a k’ira police,just because this is a respected family, shikenan se a kyale talaka ya cutu? All evidences are pointing towards Ameer. Kar ka manta wanda aka kashe uba yake a gun y’ata Layla se inda k’arfi na ya k’are”. Dad da Abban Habeeb kawai kallon Uncle Rasheed suke yi cike da mamakin sauyawar sa karaf d’aya, babu wanda ya sake furta kalma d’aya a cikin su. ******** ********* ******** Shimfid’e take kan gado Suraj na zaune gefen ta hannun …