YANAYIN RAYUWA CHAPTER 1
?YANAYIN RAYUWA??????????? Book 1?? Bismillah Rahmani Rahim …. Tafiya take cikin nutsuwa, hankalin ta sam baya wajen da take, da ka kalle ta ka san tunani take bisa ga yanda ta rungumi littafinta. Alamu sun nuna daga school ta tashi. Yarinya ce yar kimanin shekara 10 zuwa 11. Ba tada wani jiki amma ba siririya bace, baka ce amma ba sosai ba. Wani gida ta shiga da sallama amma shiru babu wanda ya amsa mata. Hakan ya sa ta cusa kai domin ta san ko zata kwana ba amsawa za ayi ba. Ta shiga, a falo ta tarar da yaran gidan da maman su, gaishe ta tayi ta amsa fuska a murtuke, shigewa dakin ta yi, har sakiyan dakin ta zauna kan katifanta ta ajiye takardan hannun ta da jakan bayanta, tashi tayi ta canza kayan ta izuwa atamfa riga da skirt ta zura hijabinta tayi waje, kamar yanda ta bar su haka ta same su. Ta dan matsa kusa da matan, tace; “Mama ina abinci na?”. Juyawa maman tayi ta wurga mata harara tare da jan tsaki. Hmmm ni kuma nace daga tambaya bunar bakin. Mama tace…