WATA FUSKA CHAPTER 7
WATA FUSKA CHAPTER 7 Kai tsaye fareedah gidanta ta nufa tae wanka tae salla ta zauna ta qurawa wannan pic d’in ido ita sam ta kasa nutsuwa akan wannan maganar, yaya zaka dauki rayuwar d’an uwanka musulmi ba komai ba? Ko rayuwar arne babu wanda yace ka dauka ka kashe kace kaci bulus maganr nan da daddy keyi akan qyamatar talakan da Anty Nasara keyi har yaje wannan wurin!! Yasha yin fad’a akan korar mutanen datake yi idan sunzo masa, yakance mata yana tausayin ta kar wata rana wannan qiyayyar datakewa talaka ya janyo mata wata musibar, gashi yanzu ta fara gani tunkan aje ko ina, sabida tsabaragen iskanci da sonkai gashi nan ta soma safarar mutane…..”Bazan iyaba!!!” Ta furta a sarari da d’an qarfi ladiyo me mata aiki tace “Na’am hajiya, Magana kike ne?” Murmushi ta sakar mata na yaqe tace….a gayawa d’an liti ya shirya zan fita, wayarta ta d’auka tawa Maheer waya yana d’agawa suka gaisa tace “Kana ina ne zamui magana dakai ne” “Shirin zuwa sokoto nakeyi ko ince nama kammala sokoto…