WATA BAKWAI CHAPTER17
WATA BAKWAI CHAPTER 17 Yauma bayan sun shirya sai da suka fara biyawa suka ce ma Nas zasu je yawo in sun dawo zasu biyo.+ Idan doctors din sun yarda wajen shi ma zasu kwana. “Go do your romantic yawo. Nikam am fine. Bama saikun dawo ba munyi waya” Nas ya fadi yana musu murmushinsa yana jin dadin ganin yayan na shi cikin nutsuwa da walwala haka. Saida suka dan kara hira tukunna suka fita. Mai taxi din da suka hau yana gane turanci dan haka prince ishaq yace yakai su inda ake bada renting din mota. Aikam shi ya rakasu. Kasancewar ba yan kasa bane yasa da suka biya kudin renting din motar. Saida ya bada passport dinsu shida husna. Insun dawo da motar a basu abinsu. Sai da suka shiga ne suka dauki hanya husna tace masa “Ina zamuje ne wai? Ka wani kama mota kaman kasan gari” Dariya yai ya daga mata kafadu yace “Mu dauki hanya kawai muga gari. Duk inda muka gaji mu dawo” Rigimar shi din nan tana bata mamaki a lokaci daya tana burgeta. “Kawai ina son yanda nake da damar fita duk ind…