WATA BAKWAI CHAPTER 6

WATA BAKWAI CHAPTER 6
WATA BAKWAI CHAPTER 6 Yanayin tsari na garin abuja ya burgeta matuqa.+ Zataso ace da ammar dintane sukazo dataji dadin zuwan. Bude musu mota akai. Tana fitowa takalli yanayin ginin gidan batasan “wow” ta subuce mata ba. Zagayawa tai dan zatonta zaa bude bayan motar ne su dauki kayansu. Ganin ta tsaya yasa shi fadin “Muje mana” “Zan dauki kayana ne” ta bukata tana masa kallon da yake fassara wannan wacce irin tambaya ce? Kallonta yai sosai kamun yace. “Muje za.a shigo maki dashi” Ganin ya wuce abinsa yasa tabi bayanshi Tsakiyar wani qayataccen falo suka isa. “Za.a nuna miki bangarenki. Inkina buqatar wani abu hadiman gidan zasuyi miki” Ya fada mata. Bai jira amsarta ba ya wuce. Wata ce tazo ta rakata har bangarenta. Wajen ya hadu dan duk tsanar mammalakin gidan datai bai sa yaqi burgeta ba. Wanka tayi dan tagaji sosai tunda bata samu tsarki ba balle tace zatai sallah. Ta duba wayarta ammar bai dawo online ba har lokacin. Ta soma kewarshi. Tunawa tai ashe fa kausar na abuja…